Leadership News Hausa:
2025-09-24@08:37:37 GMT

Wata Mahanga Ta Daban Ta Kallon Ayyukan Ta’addanci

Published: 21st, September 2025 GMT

Wata Mahanga Ta Daban Ta Kallon Ayyukan Ta’addanci

 

Al’amari mai rikitarwa

Hakikanin gaskiya ya fi an rikitarwa. Bisa al’amari, ana kiyasta cewa mutane kimanin 15,000 zuwa 20,000 ne suka mutu a sakamakon kashe-kashen da suka shafi ƴ an bindiga da ta’addanci a Arewa maso Yamma kaai cikin shekaru 10 da suka wuce. Wannan adadi yana daidai da yawan rayukan da aka rasa a Yakin Kosobo, ko kusan kashi 40 cikin ari na asarar rayuka a Yakin Basasar Saliyo na tsawon shekaru 10, duk da cewa ba gwamnati ba bace ke yakar ƴ an bindiga, sai dai ƴ an ta’adda ne masu zaman kansu.

Wannan kididdigar ba ta bayyana irin wahalar da dubban yara ke sha ba, waanda aka kashe iyayensu, gidaje marasa uwa ko masoya, mutane da suka ji rauni har abada ko aka raba su da muhallansu, hanyoyin neman rayuwa da aka lalata, makoma da aka rusa, da rayuwar yanzu da ake yi cikin tsoro da rashin tabbas.

Lawal ya taba ba da labari kan yadda wasu ƴ an bindiga, waanda aka gano shirinsu bisa bayanan sirri, suka tsere kafin ya iya ratsa dogon jerin umarnin soja na Abuja.

Yana da, domin yana takaicin yadda ake rage karfin gwamnoni tare da mai da su tamkar wasu jagorori ta fuskar manyan matsalolin tsaro, domin muna shakku akansu cewa za su iya yin amfani da rundunar ƴ an sandan jihohi wajen zalunci.

 

Ilimin Zamantakewar Ƴan Bindiga

Sai dai, ba fasaha da ƴ ansandan jihohi kaai ne za su iya takaita wannan masiba ba. Wannan shi ne abin da wani bincike da Cibiyar Nazarin Harkokin Kasa ta Denmark ta gudanar a Agustan 2025. Sakamakon binciken, wanda aka saki kwanan nan, ya cancanci a yi la’akari da shi.

Binciken da Peer Schouten da Barnett James suka gudanar na farko, babban mai bincike na biyun kuma alibin PhD a Jami’ar Oford, mai taken “Dibided, They Rule? Sabon Yanayin Ƴan Bindiga a Arewacin maso Yammacin Nijeriya

“Binciken ya duba ilimin zamantakewar ƴ an bindiga, tushensu da yadda suka samo asali, da kuma yadda suka maye gurbin ƴ an jihadi waanda a da suka fi rinjaye a matsayin reshen Sahel mai girman tasiri.

Labari na yau da kullum kan ƴ an bindiga, ƴ an jihadi, da masu tsattsauran ra’ayin addini ya kan bayyana su a matsayin “ƴ an ta’adda da masu laifi.” Sai dai wannan bincike ya auki wata hanya mai zurfi wadda ta bayar da wata fahimta, inda ya bambanta ƴ an bindiga da ƴ an jihadi ko wasu kungiyoyin laifi, musamman bisa akida, wuri, da kuma hanyoyin gudanar da ayyuka.

Ya ce, alal misali, “Sabani da kungiyoyin jihadi, kungiyoyin ƴ an bindiga ba sa aiki bisa ga wata akida ta ra’ayi, amma suna da tasiri sosai a mulkin yankunan karkara, suna kalubalantar ikon gwamnati ta hanyar fyae da yin barna, da kuma ta hanyar tsayayyen haraji da karbar kuin fansa.”

 

Lallai Lamarin Ta’addanci Ne

Sau da yawa na kan yi amfani da kalmomin nan ba tare da bambanci ba. Amma su idan suna magana suna banbancewa, kamar su ce, ƴ an bindiga suna kai hari, masu garkuwa na kai hari, kuma dukkansu suna barin jama’a cikin bakin ciki, hawaye da jini, to, a wajena dukkan su ƴ an bindiga ne, ƴ an jihadi, ƴ an ta’adda da masu laifi. Sai dai manufar binciken ita ce, idan ba a tantance dalilai da hanyoyin da suke bi ba, to mayar da martani da manufofi na iya sauka daga ainihin layin da ya dace.

Idan za mu yi magana da salon Lawal, Gwamnan Zamfara ko duk wani gwamna a Arewacin maso Yammacin Nijeriya da ke sha’awar shawo kan matsalar tsaro, domin ya yi aiki fiye da ikon zartarwarsa don ya yi nasara, to ba ya ga samun ƴ ansandan jiha, dole ne su fahimci ilimin zamantakewa da tunanin abokan gaba, in ba haka ba, watakila mu shiga mawuyacin hali fiye da yanzu a cikin watanni arba’in.

Wannan binciken ya bayyana yadda, ta hanyar tsarin “yin barna da kuma kararbar kuin fansa,” Tun daga shekarar 2011 ƴ an bindiga suka kirkiro wani tsarin mulki “wanda hanyoyi ne masu muhimmanci da suke tunatar da tsarin mulki na tattara haraji a yankin tun kafin zuwan Turawan mulkin mallaka.”

 

Yekuwa Daga Daular Usmaniyya

A cikin tausasa harshe, binciken yake cewa ƴ an bindiga, waanda suka samo asali kusan shekaru 15 da suka gabata, suna maimaita wani fasali na tsarin Khalifanci a Arewacin Nijeriya, wanda ya dogara kan “kai hari da karbar haraji” don faaawa da kuma tabbatar da wanzuwar tsarin.

A cewar binciken, “Ƴan bindiga na yau,” “suna maimaita waannan tsarin, inda babura na zamani da wayoyin hannu suka maye gurbin dawaki da bindigogin karni na 19.

Duk da cewa kayan aikin sun canza ba kamar na da ba, amma tsarin mulki da tattara arziki na asali suna nan kamar yadda suke, wanda hakan yana da matukar wahala mutanen karkara da wasu waanda abin ya shafa su fahimta.”

Binciken bai auka cewa duk ƴ an bindiga Fulani ne ba, kamar yadda aka fi samu a karni na 18 da na 19. Ko kuma cewa suna da burin gina jiha ko tsantsar imani kamar ƴ an jihadi na lokacin. Sai dai, binciken ya lura da maimaita wasu tsarin iko da sahihanci a waannan yankuna da suka yi kama da tsarin Khalifanci.

 

Lamarin Ya Zama Gagaradau

Lawal ya ji takaici kan rasa babban burinsa akan kawo karshen ƴ an bindiga saboda tsarin umarni na soja. A bangaren su, sojoji ma sun kai hari kan fitattun shugabannin ƴ an bindiga, inda nasarorin baya-bayan nan suka haa da Baleri Fakai da Halilu Buzu.

Waannan matakai sun kasance gagarumin ci gaba a yaki da ƴ an bindiga. Sai dai, wannan binciken ya kwatanta kungiyar ƴ an bindiga da dabbobi wato (Hydra-headed monster). Kungiya ce mai hain gwiwa amma ba ta da tsari mai karfi, wadda ke iya daidaitawa da sake habaka kanta ko da an cire shugaba na yanzu.

An tsara su ne don su iya jure rashin shugabansu, inda cire su wani lokacin ba abin so bane ga al’ummar da suke ciki.

Me ya sa? A bara, lokacin da aka kashe Halilu Sububu, alal misali, wata majiya ta shaida wa masu binciken cewa, “Kuskure ne a kashe Buzu (Halilu). Ya fara yin abubuwa masu kyau, yana gaya wa ƴ an bindiga su daina damun Fulani, wanda hakan yi tasiri soasi a Zamfara, Kaduna, Katsina, Kebbi da Sokoto.”

A wasu kalmomi, a wani yanayi na canjin hali mai ban mamaki, ƴ an bindiga suna sauyawa daga “ƴ an ta’adda da masu laifi” zuwa “masu kula,” suna cike gibin da gwamnati marasa halarta suka bari.

Za ka iya kiran shi ‘Stockholm Syndrome’, idan ka so, amma waanda suka yi mamakin dalilin da ya sa shugaban ƴ an bindiga, Kachalla Ado Aliero, aka naa shi Sarkin Fulani a Zamfara a 2022, ba sai sun sake tambaya ba.

Kuma waanda suka ji haushi da rashin hankali wajen yin yarjejeniya da ƴ an bindiga maimakon tarwatsa su da bama-bamai, watakila za su so su dakata su yi tunani akan dalilin yin hakan.

Yayin da ya kawo wani misali a cikin wani lamari mai tausayi, binciken ya ce, “A shekarar 2024, mutanen Kachalla Najaja (ƴ an bindiga) sun hukunta garin Anka (a Zamfara) saboda karbar masu gadi na gari ta hanyar hana mazauna garin girbin dawa, suna amfani da yunwa a matsayin hanya don tilasta su yin biyayya.”

A karshe, mazauna garin da suka shiga cikin hali na tsanani sun cimma yarjejeniya ta “zaman lafiya” ta hanyar biyan Naira miliyan 50. Wani mai shiga tattaunawar ya bayyana cew, ‘Shugabanmu na gida ya hana mu shiga sulhu, amma ba zai iya ba mu kariya ba ko ya samar mana da abin da za mu ci.”

 

Su karbi kui masu yawa, su mutu da talauci

Me ƴ an bindiga ke yi da kuin? Suna ajiye “dukiyarsu,” mafi yawanci daga haraji na tilas, kuin fansa ne, da satar shanu, a cikin sifofi masu saukin sarrafawa, wanda suke amfani da su wajen sayen karin shanu, sannan kuma a wajen sayen makamai alamari ne mai muhimmanci.

Kamar yadda manyan masu mallakar bayi a Afirka lokacin mulkin mallaka suka kasance, darajar shugabannin ƴ an bindiga wani lokaci ana auna ta ne da adadin mayaka, waanda aka sace ko mabiyansu, ba sa yin karyar nuna daidaito, domin shugaban yana more wani kaso na dukiyar da aka sato.

Sai dai, duk da shahararsu ta almara, wani masunci daga Kebbi ya shaida wa masu binciken cewa, “Kaan ne abin da suke samu na duniya” kuma suna mutuwa cikin talauci.

Binciken ya kawo karshe cewa ƴ an bindiga suna ta’addanci ne sakamakon rashin jajircewa mai orewa wajen raya karkara, samar da damammakin tattalin arziki, da kuma gyaran cibiyoyi. Wannan abu ne da mai hankali ya dace ya yi tunani a kansa ga kowace gwamnati da ke sha’awar warware wannan matsala nan ta tsawon lokaci.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Hisbah ta kama masu safarar mata zuwa Saudiyya a Kano

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama gungun wasu mutane da ake zargi da safarar mata zuwa kasar Saudiyya.

Hisbah ta dakile yunkurin mutanen ne a yayin da suke kokarin safarar wasu mata hudu daga jihohin Kano da Jigawa da Yobe, ta hannun wakilansu da ke sassan kasashen Yammacin Afirka?

Mataimakin Babban Kwamnand Hukumar, Dakta Mujahideen Aminudeen, ya ce masu safarar matan sun yaudarin matan da aka ceto cewa za su yi musu biza zuwa kasar Ghana inda daga nan za su wuce da su zuwa Saudiyya domin sama musu ayyukan yi.

An kana daya daga cikin mutanen ne a ranar Lahadi, wanda hakan ya kai ga cafke shugabansu da ake kira Bashir Sani Ibrahim.

Ballon d’Or: Wa zai lashe kyautar 2025? Yadda aka kashe jami’an tsaro 53 cikin mako biyu NAJERIYA A YAU: Yadda Wata Bakuwar Cuta Take Cin Naman Jikin Mutanen Malabu

Uku daga cikin matan masu shekaru 30 sn fito ne daga jihohin Kano da Jigawa a yayin da hudun mai shekara 35 da fito daga Jihar Yobe.

Dakta Aminudeen ya bayyana cewa matan sun biya mutanen Naira milian bibbyu, za su ciko Naira miliiyan 1.5 kowannensu domin sama musu biza.

Ya ce, “Wannan shi ne abin da muke ta gargadin mutane a kai — kar a yarda da tafiya ba tare da sanin inda za a kai su ba. Ana yaudarar mutane, ana kwace musu kuɗinsu, kuma da zarar sun isa ƙasashen waje ana tilasta musu shiga harkar karuwanci, fataucin miyagun ƙwayoyi ko kuma tsunduma cikin rayuwar kunci.”

Ya shawarci ’yan Najeriya da su guji irin waɗannan haɗurran tafiya, yana mai jaddada cewa kuɗin da ake ɓatawa wajen irin wannan safarar ya fi dacewa a saka shi a harkokin kasuwanci a gida.

“Da naira miliyan biyu ko uku da rabi, mutum zai iya fara kasuwanci mai kyau a Najeriya maimakon fadawa tarkon waɗannan miyagun dabaru,” in ji shi.

Ya nuna godiya cewa an samu damar dakile wannan yunkuri, yana mai cewa da masu safarar mutanen sun ci nasara, da lallai matan sun ɓace ba tare da sahu ba.

“Mun tattara bayanansu da fasfofonsu muka mika su ga Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane (NAPTIP). Za mu ci gaba da sa ido har sai an kammala bincike kan lamarin,” in ji shi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Groosi: Masu Binciken Hukumar Kula Da Makamashin Nukiliya Suna Hanyar Zuwa Iran
  • ‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Filato
  • Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Da Ɓullar Cutar Mpox A Jihar
  • Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Ɓullar Cutar Mpox A Jihar
  • Hisbah ta kama masu safarar mata zuwa Saudiyya a Kano
  • Karin ƙananan hukumomi 2 sun yi sulhu da ’yan bindiga a Katsina
  • Yadda Wasu Mata Ke Gwada Mazansu Ta Hanyar Magana Da Su Ta Wasu Hanyoyi Don Sanin Ku Suna Kula Mata
  • Yadda Ƴan Agbero’ Ke Cin Karensu Ba Babbaka A Abuja
  • SERAP, Amnesty Sun Bukaci Tinubu Ya Janye Ƙarar Da Ya Shigar Kan Sowore, X Da Facebook