Muhawara game da sanya doka a kan makarantu masu zaman kansu yana ta ci gaba a  ciki da wajen jihar Kaduna saboda ƙaruwar makarantun masu zaman kansu a cikin ƴ an shekarun nan musamman a cikin sabbin unguwanni da ke cikin ƙwaryar Kaduna.

Abubuwan da jama’a ke magana a kai sun haɗa da tabbatar da inganci, kare haƙƙoƙin ɗalibai, da daidaita kuɗaɗe.

Masu mallakar makarantun masu zaman kansu sun koka da yawan haraji da tsadar aiki, wanda ya sa su yi tsayin daka  wajen ƙara kuɗin makaranta.

Sanya doka mai tsauri na iya ƙara musu nauyi kuma ya tilasta wasu rufe makarantunsu.

Sai dai masana harkar ilimi Sun bayyana cewa daidaitawa da haɓaka inganci: dokar za ta sa makarantu masu zaman kansu su bi ƙa’idojin koyarwa na jihar Kaduna, wanda hakan zai inganta ingancin ilimi ga kowa.

Hakazalika,  dokar za ta taimaka wajen kare iyalai daga biyan kuɗi mai tsoka da kuma tabbatar da cewa suna samun ilimi mai inganci a farashi mai sauƙi Hasalima, da yawa daga cikin wadannan makarantun  wato makarantu masu zaman kansu  suna da ƙarancin inganci saboda suna ɗaukar ma’aikatan da ba su da cikakkiyar horo saboda rashin son biyan su albashi mai tsoka.

Wannan matsala na tattare da ingancin ilimi ga zalibai. Da dama daga cikin makarantun masu zaman kansu ba su da kayan aiki da ya kamata, kamar ɗakunan karatu da ɗakunan gwaje-gwaje. Wasu daga cikinsu suna amfani da gine-gine masu haɗari da ba a duba ingancinsu ba, wanda hakan yana haifar da haɗari ga ɗalibai.

Hakan ya sanya da  dama daga cikin jama’a na goyon bayan dokar da gwamnatin jihar Kaduna ta sanya; suna ganin cewa hakan zai daidaita ingancin koyarwa da kuma sa makarantu su riƙa bin ƙa’idoji.

Binciken leadership Hausa ya gani cewa wasu masu makarantun masu zaman kansu sun nuna damuwa game da dokar, suna jin cewa hakan zai ƙara musu nauyi da kuma rage musu damar samun riba.

Ɗaya daga cikin manyan ƙalubale shi ne rashin iya sa ido kan makarantun masu zaman kansu. Akwai haɗarin cin hanci da rashawa, wanda zai iya sa a yi watsi da ƙa’idoji.

Wasu na cewa dokar ba za ta iya magance matsalar ingancin koyarwa ba, matuƙar gwamnati ba ta inganta makarantun ta na gwamnati ba.

A zantawar da Wakilinmu da wasu iyaye Sun bayyana hamsuwarsu dangane da Wannan dokar inda suka sanya dokar tazo a daidai lokacin da ake buƙata.

Hakazalika, Sunce muddin gwamnatin jihar Kaduna Tana son ɗorewar dokar sai ta Samar da Jami’ai waɗanda zasu rinƙa biybiyar makarantun domin tabbatar da dokar Tana aiki yadda ya kamata.

Wasu makarantun da wakilinmu ya Kai ziyara a ƙananan hukumomin Kaduna ta Arewa da ta Kudu da kuma ƙaramar hukumar Igabi wacce tafi kowacce ƙaramar hukuma yawan makarantu masu zaman kansu Sun bayyana cewa idan wannan dokar ta ɗore kuma basu samu Tallafin gwamnatin ba babu shakka akwai yiwuwar durƙushewar makarantu da yawan gaske duba da ganin cewa kuɗaɗan da ɗalibai suke biya dana sayar da littafai sune suke riƙe makarantun suna masu cewa rashin samun hakan zai haifar musu da ƙalubale mai tarin yawa.

Wani mamallakin wata makaranta a garin Hayin Rigasa da Unguwar Kawo sun tabbatarwa da wakilinmu cewa a haƙiƙanin gaskiya basa goyon bayan Wannan dokar muddin ba  za’a basu damar ƙara ɗudin makaranta inda suka ce ƙarin kuɗin man fetur shi kaɗai ya cancanci wasu makarantun su ƙara kuɗinsu domin suma malaman da suke koyarwa Sun samu ƙarin kuɗin abun hawa Wanda dole a ƙara musu albashi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Makaranta makarantun masu zaman kansu makarantu masu zaman kansu jihar Kaduna

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da janye dokar ta-baci a Jihar Rivers daga ƙarfe 12 na daren 17 ga watan Satumban 2025.

Shugaban Ƙasar, a wata sanarwa da ya sanya wa hannu, ya ce dokar ta-bacin da ta dakatar da Gwamna, Mataimakiyarsa, da ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida ta cimma manufarta na dawo da zaman lafiya a jihar.

Tinubu ya bayyana cewa ya yi amfani da Sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulkin 1999 ne a watan Maris na 2025 sakamakon durƙushewar mulki a Jihar Rivers.

A cewarsa, rashin jituwa tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Majalisar Dokokin Jihar, da kuma lalata muhimman kadarorin gwamnati sun jefa jihar cikin rikici.

“Lamarin ya kai ga Babbar Kotun Ƙoli ta bayyana a ɗaya daga cikin hukuncinta cewa babu gwamnati a Jihar Rivers.” In ji Shugaban Ƙasa.

Ya gode wa Majalisar Ƙasa bisa amincewa da wannan sanarwa, tare da yabawa Sarakuna da jama’ar jihar bisa haɗin kan da suka bayar.

Tinubu ya kuma yaba wa  masu adawa da suka kalubalanci wannan mataki a kotu, yana cewa wannan shi ma wani ɓangare ne na dimokuraɗiyya.

Da yake magana kan sabuwar fahimta tsakanin manyan ‘yan siyasa a jihar, Shugaban Ƙasa ya ce babu dalilin ƙara tsawaita dokar ta-bacin.

Ya bayyana cewa Gwamna Siminalayi Fubara, da Mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu, da Shugaban Majalisar Dokoki Martins Amaewhule da dukkan mambobin majalisar jihar za su koma bakin aiki daga 18 ga Satumban 2025.

Tinubu ya yi kira ga shugabannin siyasa a faɗin Najeriya da su ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai domin isar da fa’idodin dimokuraɗiyya ga al’umma.

 

Daga Bello Wakili

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mutum 1,666 ne suka kashe kansu a Legas cikin shekaru biyar – ’Yan sanda
  • Amurka Ta Yi Amfani Da Kujeran Veto Don Hana Zaman Lafiya A Gaza
  • Ce-ce-kuce Kan Shirin Ƙara Wa Ƴan Siyasa Masu Riƙe Da Madafun Iko Albashi
  • ’Yan sanda sun kama mutum 9 kan yin garkuwa da kansu
  • Uwargidan Shugaban Kasa, Oluremi Tinubu Ta Yi Kira Ga Zaman Lafiya A Duniya
  • Karamar Hukumar Malam Madori Ta Horar Da Mata Kare Kai Daga Cututtukan Mahaifa
  • Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
  • Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna