Aminiya:
2025-09-24@08:37:36 GMT

Shettima ya tafi New York don halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya

Published: 21st, September 2025 GMT

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar Abuja zuwa birnin New York na Ƙasar Amurka, domin halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80.

Taron zai gudana daga ranar Litinin, 22 ga watan Satumba, zuwa ranar Lahadi, 28 ga watan Satumba, 2025.

Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu Jami’ar European-American ta musanta bai wa Rarara digirin girmamawa

Shettima zai wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wannan babban taro.

Zai gabatar da jawabi, tare da shiga muhawarar shugabannin ƙasashe a zauren taron.

A yayin taron, Mataimakin Shugaban zai kuma bayyana sabbin muradun Najeriya a ƙarƙashin yarjejeniyar kare muhalli.

Wannan zai gudana ne a wani taro na musamman kan sauyin yanayi da Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya zai shirya a ranar Laraba, 24 ga watan Satumba.

Haka kuma, Shettima zai halarci wani taron koli kan samar da gidaje masu sauƙi da sauƙin farashi, wanda Shugaban Ƙasar Kenya zai jagoranta.

Bayan kammala taron, Shettima zai wuce Birnin Frankfurt, na Ƙasar Jamus, inda zai gana da jami’an bankin Deutsche Bank kafin dawowa Najeriya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Majalisar Dinkin Duniya taro Tattauanawa

এছাড়াও পড়ুন:

Tattalin arzikin Najeriya ya ƙara haɓaka — NBS

Hukumar Ƙididdigar a Najeriya, NBS ta ce arzikin cikin gida da ƙasar ke samu ya ƙaru da kashi 4.23 cikin 100 a rubu’i na biyu na shekarar 2025 da muke ciki.

Sabbin alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa an samu ƙarin kashi 3.48, idan aka kwatanta da daidai wannan lokacin a 2024, lamarin da hukumar ta ce alamu ne na bunƙasar tattalin arzikin ƙasar.

An gudanar da bikin ɗaga tutar Falasɗinu a Birtaniya CAC ta soma yi wa kamfanoni rijista da fasahar AI

NBS ta ce fannin aikin gona ne kan gaba wajen samar da ƙaruwar arzikin ƙasar, wanda ya ƙaru zuwa kashi 2.82 saɓanin kashi 2.60 a 2024.

Sauran fannonin da hukumar ta ce an samu ci gaba sun hada da fannin masana’antu da, da man fetur da kuma fannin ma’adinai.

NBS ta ce a rubu’i na biyu na shekarar 2025, arzikin cikin gida da Najeriya ta samu ya kai naira tiriliyan 100.73, ƙari kan naira tiriliyan 84.48 da aka samu a 2024 daidai wannan lokacin, abin da ke nuna ƙarin kashi 19.23 cikin 100.

A watan jiya na Agusta ne Majalisar Ƙoli ta tattalin arziki a Najeriya, ta sanar da amincewa da sabon tsarin ci gaban tattalin arziki zango na biyu na tsawon shekaru 5 wato 2026-2030, bayan ƙarewar zangon farko wato daga 2021 zuwa 2025.

Sabon tsarin da majalisar ta ƙaddamar wadda ke ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shetima ci gaban tattalin arziki zai yi la’akari da sauye-sauyen da aka samu kamar cire tallafin man fetur, sabbin dokokin haraji da makamatansu.

Ƙarƙashin sabon tsari ne kuma gwamnatin ke son cimma ƙarfin tattalin arziƙi na Dala tiriliyan ɗaya nan da shekarar 2030, abinda ya dace da manufofin ƙasar har zuwa shekarar 2050.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Firaministan Sin Ya Isa New York Don Halartar Babban Taron Mahawara Na MDD Karo Na 80
  • Majalisa ta ɗage ranar dawowarta zuwa 7 ga watan Oktoba
  • Talata ce ɗaya ga watan Rabi’ul Thani — Sarkin Musulmi
  • Tattalin arzikin Najeriya ya ƙara haɓaka — NBS
  • Kasar Sin Za Ta Shirya Taron Mata Na Duniya A Beijing Yayin Cika Shekaru 30 Da Taron Mata Na 1995
  • Kashim Shettima Ya Isa New York Halartar Taron UNGA Na 80
  • Ranar Zaman Lafiya ta Duniya: Kungiyar Arewa Ta Nemi Ƙarfafa Sirrin Tsaro Don Kare ‘Yan Najeriya
  • Shettima ya bar Abuja don halartar taron majalisar ɗinkin duniya a New York
  • Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu