Larijani: Donald Trump Yana A Matsayin Makwafin Adolf Hitler
Published: 24th, September 2025 GMT
Babban magatakardar malajisar koli ta tsaron kasar Iran Dr. Ali Larijani ya bayyana cewa; Batun sake kakabawa Iran takunkumi yana nuni da gajiyawar kasashen turai.
Dr. Ali Larijani wanda tashar talabijin din al’mayadin’ta yi hira da shi, ya kara da cewa, matakin da kasashe uku na Faransa, Birtaniya da Jamus, su ka dauka akan batun sake kakabawa Iran takunkumi, yana sake yin nuni ne da tsohuwar gabar da kasashen turai da Amurka suke da ita akan al’ummar Iran.
Dr. Ali Larijani ya kuma ce, wanann irin kiyayya da siyasa tana cin karo da kudurin MDD mai amba 2231 da kwamitin tsaro ya fitar da shi a baya. Bugu da kari, wanann siyasar tana a matsayin wani yunkuri ne na yin matsin lamba akan kawancen gwgawarmaya da kuma hana Iran ci gaba a fagagen ilimi da tsaro.
Sai dai duk haka, Dr. Larijani ya ce, wannan irin siyasar za ta mayar da kasashen turai din zama saniyar ware a duniya.
Da yake Magana akan halayyar shugaban kasar Amurka Donald Trump, Dr. Ali Larijani ya bayyana cewa yana a matsayin wani sabon zubi na Adolf Hitler shugaban ‘yan Nazi a lokacin yakin duniya na biyu.
Dr. Ali Larijani ya kuma ce, kamar yadda yadda Hitler ya yi mummunan karshe, shi ma Donald Trump abinda zai faru da shi kenan.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Fiye Da Falasdinawa 900,000 Ne Su Ka Yi Hijira A Cikin Gaza September 24, 2025 Imam Khamenei: Hadin kan al’ummar Iran a yakin kwanaki 12 ya sanya makiya kunya September 24, 2025 Larijani: Iran na kare tsaron kasa da azama September 24, 2025 Jagora: Iran Ba Za Ta Taba Yin Watsi Da Inganta Sinadarin Uranium Ba September 24, 2025 Larijani: Iran Tana Nazarin Shawarwarin Turai Da Na Rasha Domin Kare Muradunta September 24, 2025 Araqchi; Iran Da Norway Sun Tattaunawa Batun kyakkyawar Alakar Da Ke Tsakaninsu September 24, 2025 Groosi: Masu Binciken Hukumar Kula Da Makamashin Nukiliya Suna Hanyar Zuwa Iran September 24, 2025 Kasashen Afirka Uku Sun Sanar Da Ficewa Daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka Ta Duniya September 24, 2025 Imam Khamenei Zai Yi Jawabi Ga mutanen Iran A Cikin Makon Tsaro Da Ya Shigo September 23, 2025 Lebanon: A yau Ne Aka Yi Jana’izar Shahidan Bitij Bail Wadanda HKI Ta Kai Ga Shahada A Ranar Lahadi September 23, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Ali Larijani ya kasashen turai
এছাড়াও পড়ুন:
Hamas ta bukaci kasashen duniya da MDD su mayar da Isra’ila saniyar ware
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da amincewar da kasashen Birtaniya, Australia, da Canada suka yi wa kasar Falasdinu, tana mai bayyana hakan a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da hakkin al’ummar Palasdinu na kasarsu.
A cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Lahadi, kungiyar ta yi kira ga kasashen duniya da MDD da su mayar da Isra’ila saniyar ware tare da dakatar da duk wani nau’i na hadin gwiwa da ita.
Hamas ta yaba da wannan amincewa da ita a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da ikirarin da al’ummar Falastinu ke yi na neman kare filayensu da wuraren ibadarsu masu tsarki, tare da fatan samun kasa mai cin gashin kanta wacce take da Quds a mastayin babban birni.
Har ila yau kungiyar ta yi kira da a kara daukar matakan ladabtarwa kan Isra’ila tare da hukunta shugabanninta kan laifukan cin zarafin bil’adama.
Sanarwar ta soki gwamnatin Isra’ila kan yadda take ci gaba da yin watsi da dokokin kasa da kasa da kuma ka’idojin jin kai, tare da bayyana “mummunan cin zarafi” da ake yi wa Falasdinawa.
An fitar da wannan sanarwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da takun sakar diflomasiyya tsakanin kasashen dake amincewa da Falasdinu a matsayin kasa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran : Dakatar da kisan kiyashi a Gaza, ‘’zakaran gwajin dafi ‘’ne ga MDD” September 22, 2025 Italiya: An yi gagarimar zanga-zangar tir da kisan kiyashi da ake yi a Gaza September 22, 2025 Iran ta la’anci harin da aka kai kan wani masallaci a Sudan September 22, 2025 Ana Ci Gaba Da Kidayar Kuri’aun Zaben Shugaban Kasa A Guinea September 22, 2025 Kwamandan Sojan Iran: Ba Za Mu Taba Wasa Da Manufofinmu Na Kasa Ba September 22, 2025 Korea Ta Arewa Ta Sanar Da Kera Wani Sabon Makami Na Sirri September 22, 2025 Jirgin Ruwan “Umar Mukhtar” Na Agaji Ya Kama Hanyar Zuwa Gaza Daga Kasar Libya September 22, 2025 Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Jinjinawa Tawagar Kokawar Greco-Roma Ta Iran Murnar Lashe Gasar Cin Kofin Duniya September 22, 2025 Pezeshkian: Kasashen Da Ba Su Cika Alkawura Da Suka Dauka Ba Suke Zargin Iran Kan Rashin Mutanta Yarjejeniyar Nukiliya September 22, 2025 Dakarun IRGC: Iran Za Ta Tarwatsa Makiya Tare Da Mayar Da Martani Kan Duk Wani Zalunci September 22, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci