Pezeshkian: Dole Ne Kungiyar Hadin Gwiwar Shanghai Ta Zama Hanyar Sanar Da Zaman Lafiya A Duniya
Published: 1st, September 2025 GMT
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Dole ne kungiyar hadin gwiwar Shanghai ta dauki matakai wajen samar da duniya mai zaman lafiya
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi imanin cewa, kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) a matsayin muhimmin ginshiki na tsarin kasa da kasa, dole ne ta dauki matakai na zahiri, na musamman, da kuma a bayyane kan hanyoyi guda biyu masu kamanceceniya da juna, don samar da duniya mai zaman lafiya, da duniya mai shirin fadada hadin gwiwar tattalin arziki.
A yayin taron kolin shugabannin kungiyar hadin gwiwar Shaghai “SCO” karo na 25 a birnin Tianjin na kasar China, shugaba Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa, a cikin tsarin karfafa hadin gwiwar hada-hadar kudi don rage tasirin takunkumin karya doka kan huldar tattalin arziki tsakanin mambobin kungiyar, Iran ta ba da shawarar karfafa shawarar “Asusun SCO na musamman da matsuguni” a matsayin wata hanya mai amfani ta inganta hadin gwiwar hada-hadar kudi. Ya kara da cewa, wannan shiri ya ta’allaka ne kan manyan matakai uku: fadada matsuguni a cikin kudaden kasa da rage dogaro da dala a musayar mambobi; ƙaddamar da hanyoyin haɗin gwiwa na dijital da kuma amfani da kuɗin dijital na babban banki don aminci da biyan kuɗi mai sauri; da kuma kafa asusun musanya kudin waje don tallafawa kasashen da suka fuskanci matsin lamba ko rikicin kudi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shawarar Iran A Taron Shanghai Zai Durkusar Da Darajar Dalar Amurka A Duniya September 1, 2025 Baqa’i Ya Ce: Iran Zata Kare Muradunta A Zaman tattaunawanta Da Tawagar Kasashen Turai September 1, 2025 Adadin Mutanen Da Suka Mutu A Girgizar Kasar Afganistan Ya Karu Zuwa 800 September 1, 2025 Dakarun Kai Daukin Gaggawar Kasar Sudan Sun Kai Hari Kan Birnin El Fasher Da Ke Darfur September 1, 2025 Ana Fargaban Daruruwan Mutane Sun Rasa Rayukansu A Girgizan Kasa A fganistan September 1, 2025 An Gudanar Da Jana’ar Jami’an Gwamnatin Kasar Yemen Da Suka Yi Shahada September 1, 2025 Sojojinn Yemen Sun Kai Hari Kan Wani Jirgin Daukar Mai Na Haramtacciyar Kasar Isra’ila September 1, 2025 Sojojin HKI Sun Kara Kashe Wani Dan Jirida A Gaza September 1, 2025 Janar Mousawi: Karfafa tsaron sararin samaniyar Iran zai dakile barazanar makiya a kanta September 1, 2025 Al-Houthi: Kisan jami’an fararen hula manuniya ce kan gazawar Isra’ila September 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kungiyar hadin hadin gwiwar
এছাড়াও পড়ুন:
Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda
Sudan ta yi kira ga Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya da ya sanya rundunar Rapid Support Forces (RSF) a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda bisa ga ka’idojin yaki da ta’addanci na duniya, sannan ya dauki mataki a kan duk wanda ya yi mu’amala da ita, ko ya samar mata da makamai da sojojin haya, ko jiragen sama marasa matuki, ko kuma kasar da ta bar ta ta tsallaka iyakokinta.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a lokacin zaman gaggawa na Kwamitin Tsaro don tattauna yanayin da ake ciki a Sudan, Wakilin dindindin na Sudan a Majalisar Dinkin Duniya, Al-Harith Idris, ya bukaci Majalisar da ta yi Allah wadai da kisan kiyashin da ‘yan bindigar RSF, sojojin haya na kasashen waje, da masu goyon bayanta na yankin suka aikata a El Fasher da kuma sauran wurare a cikin Sudan.
Idris ya yi kira ga Kwamitin Tsaro da ya sanya takunkumi mai tsauri ga dukkan kasashe da daidaikun mutane da Majalisar ta sani wadanda ke bayar da kudi ga RSF, samar mata da makamai, ko samar mata da mafaka, sannan a fara bincike kan kisan kiyashin da ake yi wa mazauna El Fasher don ci gaba da kokarin daukar mataki. Ya kara da cewa “‘yan bindiga suna yin barazanar kashe mutane a kullum rana ta Allah.”
Wakilin na Sudan ya yi kira da a tabbatar da an aiwatar da kudurorin Majalisar Tsaro na 2736 da 1591, “kamar yadda shaidu a Darfur suka tabbatar da cewa wasu ƙasashe maƙwabta sun shiga cikin kisan fararen hula don tallafawa ‘yan bindiga.”
Bugu da ƙari, Al-Harith ya yi kira da a goyi bayan taswirar da gwamnatin Sudan ta gabatar wa Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, wadda ta dogara ne akan dakatar da yaƙi na dindindin da kuma kwance damarar makamai na ‘yan bindiga, sannan kuma su mika wuya.
Idris ya fayyace cewa ba za a yi tattaunawa da RSF ba har sai sun ajiye makamansu su kuma sun daina kai hari kan al’ummar Sudan.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya October 31, 2025 Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan October 31, 2025 Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar October 31, 2025 Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa October 31, 2025 Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta October 30, 2025 Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci