Leadership News Hausa:
2025-09-24@08:34:05 GMT

Ƴan Bindiga Sun Sace Basarake Da Mata 2 A Filato

Published: 22nd, September 2025 GMT

Ƴan Bindiga Sun Sace Basarake Da Mata 2 A Filato

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba sun sace Hakimin Birbyang, Alhaji Zubairu Garba, tare da wasu mata biyu a daren Lahadi a ƙaramar hukumar Kanam ta Jihar Filato. Rahotanni sun ce ƴan bindigar sun shigo ƙauyen ne da tsakar dare, suna harbi a iska kafin daga bisani su yi awon gaba da mutanen. Matar hakimin, wadda aka yi garkuwa da ita a farkon harin, ta samu damar tserewa daga hannun masu garkuwa.

Wannan lamari na baya-bayan nan ya biyo bayan sace-shi-da-kashe wa da aka yi wa Dagacin Shuwaka a yankin Kyaram, wanda shi ma ke cikin ƙaramar hukumar Kanam, mako guda kacal da ya gabata. Hakan ya ƙara tayar da hankali a tsakanin al’ummar yankin kan yawaitar hare-haren ƴan bindiga.

Ƴan Bindiga Sun Kashe Sarkin Shuwaka Na Kanam A Filato Ɗan Majalisar Tarayya Ya Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-haren Ta’addanci A Sakkwato 

Ƙungiyar Cigaban Kanam (KADA), ta bakin shugaban ta Shehu Kanam da sakataren ta, Barista Garba Aliyu, ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ta fitar ga manema labarai a Jos. Sun ce harin ya auku ne misalin ƙarfe 1 na dare, inda ƴan bindigar suka yi awon gaba da hakimin zuwa wani wuri da ba a sani ba. Sun kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta ceto waɗanda aka sace tare da dawo da zaman lafiya a yankin.

Rahotanni sun nuna cewa garkuwa da mutane da hare-haren ƴan bindiga sun zama ruwan dare a yankin Kanam, inda mafi yawan waɗanda aka sace ake neman kuɗin fansa, yayin da wasu kuma ake hallaka su. Sai dai Daily Trust ya rawaito cewa, kakakin rundunar ƴan sandan jihar Filato, DSP Alabo Alfred, bai amsa tambayar wakilinta ba a lokacin da ake rubuta wannan rahoto.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji Sun Daƙile Hare-haren ISWAP, Sun Bai Wa Magidanta 10,000 Kariya A Borno

Haka kuma sun tabbatar da cewa manoma da suka koma gonakinsu kwanan nan sun samu kariya.

Babu wanda aka sace ko ɗaya, yayin da jama’ar yankin ke ci gaba da zama lafiya.

A ranar 19 ga watan Satumba, Birigediya Janar Ugochukwu Unachukwu, wanda shi ne muƙaddashin kwamandan rundunar sojojin 7 Division, ya kai ziyara Banki don yaba wa sojoji kan jarumtar da suka nuna.

Ya ce ‘yan ta’addan sun yi mummunan rashi kuma ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar sojojin Nijeriya za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi.

Sai dai rundunar ta tabbatar da cewa wani soja ya rasa ransa yayin kare mutanen, yayin da wasu suka ji rauni.

Sojojin sun ce wannan shaida ce ta jajircewar rundunar wajen tabbatar da zaman lafiya da kare ‘yan Nijeriya da suka koma gidajensu bayan gudun hijira.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Xi Ya Bukaci Hada Karfi Da Karfe Wajen Gina Yankin Xinjiang Ya Zama Mafi Kyau
  • Xi Jinping Zai Halarci Bikin Murnar Cika Shekaru 70 Da Kafuwar Yankin Xinjiang Na Uygur Mai Cin Gashin Kansa
  • Sojoji Sun Daƙile Hare-haren ISWAP, Sun Bai Wa Magidanta 10,000 Kariya A Borno
  • ‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Filato
  • Kasar Sin Za Ta Shirya Taron Mata Na Duniya A Beijing Yayin Cika Shekaru 30 Da Taron Mata Na 1995
  • Jariri ya mutu a bayan uwarsa yayin tsere wa ’yan bindiga a Neja
  • Yadda Wasu Mata Ke Gwada Mazansu Ta Hanyar Magana Da Su Ta Wasu Hanyoyi Don Sanin Ku Suna Kula Mata
  • Mata 400 sun amfana da kayan haihuwa a Gombe
  • Komai Nisan Dare Gari Zai Waye