Kungiyar Ansarullahi Ta Yemen: ‘Yan Koren Amurka Da Isra’ila Suke Neman Wargaza Hadin Kan Larabawa Da Na Musulmi
Published: 22nd, September 2025 GMT
Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada cewa: ‘Yan koren Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila na da nufin wargaza hadin kan Larabawa da na Musulmi
Jagoran kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen Sayyed Abdulmalik al-Houthi ya jaddada cewa: ‘Yan koren Amurka da na haramtacciyar kasar Isra’ila suna neman tada fitina da sanya kiyayya a tsakanin al’ummomin Larabawa da na Musulmi.
A cikin jawabin da ya gabatar a jiya Lahadi, a daidai lokacin da ake gudanar da zagayowar ranar juyin juya halin Musulunci na ranar 21 ga watan Satumba, Sayyid Al-Houthi ya ce: Dukkan ayyukan makaman Amurka da na haramtacciyar kasar Isra’ila, da kafafen yada labaransu, an karkata sune zuwa ga tada fitina da kunna kiyayya, da tayar da zaune tsaye karkashin tutar bangaranci, sabanin mazhaba, yanki, da kabilanci.
Ya yi bayanin cewa, “‘Yan koren Amurka da hukumar leken asirin Isra’ila ba su da wani aiki na hakika na yi wa kasa hidima, don haka yunkurinsu ya dogara ne kan kunna wutar gaba, sabani da kuma kiyayya da ake nunawa a halin da ake ciki.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Aiwatar Da Kisan Gilla Kan Fararen Hula 5 A Kudancin Kasar Lebanon September 22, 2025 Ministan Harkokin Waken Falasdinu Ta Yi Kira Ga Karin Kasashe Su Amince Da Samuwar Kasarta September 21, 2025 Iran Da Pakistan Sun Sake Tsara Dangantakarsu Ta Tattalin Arziki September 21, 2025 Trump Ya Bukaci Afganistan Ta Mayarwa Amurka Sansanin Jiragen Sama Na bagram September 21, 2025 Kasashen Ingila Da Canada Da Kuma Australia Sun Bayyana Amincewarsu Da Samuwar Kasar Falasdinu September 21, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya Yi Kira Ga Samar Da Tattalin Arziki Da Shugabancin Kwararru September 21, 2025 Arakci Ya Kore Cewa Ya Zanta Da Steven Witkoff Na Amurka September 21, 2025 Hizbullah Ta Yi Gayyar Tunawa Da Zagayowar Shahadar Sayyid Hassan Nasrallah September 21, 2025 Hamas Ta Yi Bukaci A Hukunta HKI Akan Rusa Asibitoci September 21, 2025 IRGC: Duk Wani Sabon Kuskuren Abokan Gaba Zai Fuskanci Mayar Da Martani Mai Tsanani September 21, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Larabawa da
এছাড়াও পড়ুন:
Gaza : MDD Ta damu kan keta yarjejeniya tsagaita wuta da Isra’ila ke yi
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya bayyana “matukar damuwarsa” kan keta yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra’ila ke yi akai-akai a zirin Gaza.
Da yake bayyana ga manema labarai a gefen taron koli na biyu na duniya kan ci gaban zamantakewa a Doha jiya Talata, Guterres ya ce: “Dole ne su dakatar da wadannan ayyuka, kuma dukkan bangarorin dole ne su mutunta sharuddan dake kunshe a matakin farko na yarjejeniyar zaman lafiya.”
“Muna aiki tukuru don kara taimakawa mutanen yankin Gaza; muna goyon bayan mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma dawo da alaka tsakanin Gaza da Yammacin Kogin Jordan,” in ji Mista Guterres.
Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta shiga tsakani, hare-haren Isra’ila a Gaza na ci gaba da kashe Falasdinawa da dama kowace rana.
A makon da ya gabata, hare-haren Isra’ila a fadin Gaza sun kashe mutane sama da 100, ciki har da yara 46.
Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a kawo karshen mamayar Isra’ila na tsawon shekaru da dama kuma ya jaddada ‘yancin al’ummar Falasdinawa na neman ‘yancin kai.
Ya jaddada cewa, “Kada mu manta da bukatar kafa wata hanyar siyasa mai inganci don kawo karshen mamayar.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Karon farko an zabi Musulmi magajin New York, birni mafi girma a Amurka November 5, 2025 Kungiyoyin agaji sun ce tallafin da ake bai wa Gaza bai isa ba November 5, 2025 China ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa Najeriya bayan barazanar Trump November 5, 2025 Imam Khamenei: Rikici Tsakanin Iran da Amurka na asasi ne November 5, 2025 Iravani: Kalaman Trump barazana ne ga zaman lafiyar duniya November 5, 2025 Khatibzadeh: Shirin Nukiliyar Iran ne aka fi maganarsa a duniya November 5, 2025 An zabi Mamdani musulmi na farko a matsayin Magajin Garin birnin New York na Amurla November 5, 2025 Hamas Ta yi Watsi Da Batun Tura Sojojin Kasashen Waje Zuwa Gaza November 5, 2025 Iran Da Pakistan Sun Kulla Yarjeniyoyi Guda Biyar Kan Harkar Sadarwa Da Al’adu November 5, 2025 Ansarullah: Dakarunsu A Shirye Suke Don Tunkarar Duk Wata Barazana Daga Isra’ila November 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci