HKI Tana Ci Gaba Da Yi Wa Mutanen Gaza Kisan Kiyashi
Published: 23rd, September 2025 GMT
A daidai lokacin da aka shiga cikin kwanaki na 718 da fara yakin Gaza, HKI tana ci gaba da yi wa Falasdinawa kisan kiyashi da makamai da kuma yunwa.
Majiyar Falasdinawa ta tabbatar da cewa daga safiyar yau Talata zuwa tsakiyar ranaFalasdinawa masu yawa sun yi shahada.
Majiyar dai ta ce, jiragen yakin ‘yan sahayoniyar sun kai hare-hare akan wani gida da yake a gabar ruwa a yammacin Gaza.
Wasu yankunan da HKI ta kai wa hare-haren sun hada titin Umar Mukhtar a tsohon garin birin Gaza.
A unguwar Tal-hawa ma sojojin mamayar sun kai wasu hare-hare akan gidajen fararen hula a yammacin birnin Gaza. Sai kuma wasu makarantun da suke a karkashin Unruwa da kan titin “al-Nasr” dake yammacin birnin Gaza.
Daga fara yakin Gaza a 2023 zuwa yanzu adadin wadanda su ka rasa rayukansu sun kai 65,344, sai kuma wadanda su ka jikkata da sun kai 166,795. Haka nan kuma da akwai wasu Falasdinawan da sun kai 9,000 da ba a san inda su ka shiga ba.
Kisan kiyashin da HKI take yi wa Falasdinawan dai yana faruwa ne a karkashin cikakken goyon bayan Amurka, da kuma shiru da rufe idanu na sauran kasashen turai da abinda ake kira kungiyoyin kasa da kasa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Nato Na Yin Taron Tattaunawa Keta Hurumin Samaniyar Kasar Estonia Da Rasha Ta Yi September 23, 2025 Dembele Ya Lashe Kyautar Ballon d’Or Ta Shekara Ta 2025. September 23, 2025 Hindi: Amurka Da Kasashen Yamma Ba Sa Son A Dakatar Da Bude Wuta A Gaza. September 23, 2025 Tattalin Arzikin Najeriya Ya HaBaka A Rubu’i Na Biyu Na 2025 September 23, 2025 Kashi 80 Cikin Dari Na MDD Sun Amince Da Falasdinu A Matsayin Kasa. September 23, 2025 Iran Da Rasha Zasu Rattaba Hannun Kan Batun Gina Wasu Tashoshin Nukiliya. September 23, 2025 Hamas ta bukaci kasashen duniya da MDD su mayar da Isra’ila saniyar ware September 22, 2025 Iran : Dakatar da kisan kiyashi a Gaza, ‘’zakaran gwajin dafi ‘’ne ga MDD” September 22, 2025 Italiya: An yi gagarimar zanga-zangar tir da kisan kiyashi da ake yi a Gaza September 22, 2025 Iran ta la’anci harin da aka kai kan wani masallaci a Sudan September 22, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Tabbatar Da Hannun Amurka Wajen Kaddamar Da Yaki Kanta
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: A bayyane yake cewa Amurka tana da hannu dumu-dumu wajen wuce gona da iri kan kasar Iran
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ismail Baqa’i ya mayar da martani ga amincewar da shugaban Amurka ya yi na daukar alhakin harin da sojojin Sahayoniyya suka kai wa Iran, yana mai cewa: “Tun daga farko a bayyane yake cewa Amurka tana da hannu a harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai wa al’ummar Iran.”
Baqa’i ya rubuta a shafinsa na X-Platform: “Shin kuna tuna cewa Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya sanar a ranar 13 ga watan Yunin shekara ta 2025 cewa: Amurka ba ta da hannu a harin da ‘yan Sahayoniyya suka kai wa Iran, kuma ya jaddada cewa wannan ‘aikin hadin gwiwa ne’ da gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi kuma ‘ba su da hannu a hare-haren da aka kai wa Iran’?”
Ya ci gaba da cewa: “Wannan ikirarin karya ce karara, domin tun daga farko ya bayyana cewa: Amurka tana da hannu a harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai wa al’ummar Iran. Yanzu shugaban Amurka ya yarda cewa shi ne ke da alhakin hakan, yana fallasa karyar sakataren harkokin wajensa kuma a zahiri ya yarda cewa Amurka ce ke da alhakin gudanar da wannan aikin tun daga farko.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Da Mexico Sun Karyata Zarge-Zargen Da Aka Yi Kan Jamhuriyar Musulunci Ta Iran November 8, 2025 Hamas Ta Goyi Bayan Matakin shari’ar Turkiyya Kan Neman kama Masu Take Hakkin Bil’Adama A Isra’ila November 8, 2025 Tarayyar Afirka Ta Yi Kiran Da A Girmama ‘Yancin Kai Na Najeriya Da Rashin Tsoma Baki A Harkokin Gidanta November 8, 2025 Tanzania: An Tuhumi Mutane Da Dama Da Laifin Cin Amanar Kasa Bayan Rikicin Zabe November 7, 2025 Limamin Juma’ar Tehran: Tsayin Dakan ‘Yan Gwagwarmaya Daga Koyi Ne Da Alkur’ani Mai Girma November 7, 2025 Unicef: Kananan Yara 47 ” Isra’ila” Ta Kashe A Yammacin Kogin Jordan November 7, 2025 Tarayyar Turai: Ana Fuskantar Matsananciyar Wahalar Isar Da Kayan Agaji Zuwa Al-Fashar Na Sudan November 7, 2025 Iran Ta Yi Allah Wadai Da Wuce Gona Da Iri Kan Kasar Lebanon November 7, 2025 Iran Ta Yi Kira Da A Kafa Kwamitin Kasa Da Kasa Don Binciko Falasdiawan Da Suka Bace A Gaza November 7, 2025 Falasdinawa Miliyan 1.5 Ne Ke Cikin Mawuyacin Hali November 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci