Aminiya:
2025-09-20@11:44:49 GMT

An tsinci gawar kwamandan hukumar NDLEA a otel a Kalaba

Published: 20th, September 2025 GMT

An tsinci gawar Igbonna Uzoma, kwamandan hukumar da ke yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) a otel da ke birnin Kalaba, Jihar Kuros Riba, a ranar Juma’a.

Rahotanni sun ce Uzoma, wanda aka dawo da shi aiki daga wata jiha zuwa Kuros Riba a kwanan nan, bai daɗe da kama aiki a sabon ofishin ba kafin wannan lamarin da ya jefa hukumar cikin ɗimuwa.

Kakakin NDLEA na ƙasa, Femi Babafemi, ya tabbatar da mutuwar babban jami’in, inda ya bayyana cewa an tsinci gawarsa a ɗakin otel ɗinsa a ranar Alhamis da ta gabata.

A cewarsa, “Kwamandan Ogbonna mutum ne mai tsananin jajircewa a aiki. An shirya fita aikin haɗin gwiwa tare da shi da misalin ƙarfe 10 na safiyar Alhamis, amma hakan bai samu ba. An kira wayoyinsa akai-akai babu amsa, har lokaci ya ƙure bai bayyana ba.”

Takari: Rayuwar baƙin haure ’yan Najeriya mazauna Saudiyya Wata mata ta ƙone fuskar ’yar mijinta da tafasasshen man girki a Borno

Babafemi ya ƙara da cewa, “Duk da ƙoƙarin da ma’aikatan otel ɗin suka yi na buɗe ƙofar ɗakinsa, daga ƙarshe sai da aka yi amfani da makulli na musamman kafin a tarar da shi kwance ba shi da rai.”

Ya ce hukumar ta sanar da rundunar ’yan sanda ta jihar Kuros Riba nan take, inda kwamishinan ’yan sanda ya kai ziyara da kansa zuwa otel ɗin.

Yanzu haka bincike na ci gaba a kan asalin sanadin mutuwar kwamandan.

Shugaban hukumar NDLEA na ƙasa, Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya), ya bayar da umarni ga kwamandan shiyyar 14 na hukumar, ACGN Mathew Ewah, da ya gaggauta komawa Kuros Riba domin ɗaukar ragamar shugabancin hukumar a jihar, har sai an kammala binciken da kuma gano musabbabin mutuwar babban jami’in.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: gawar Kwamandan

এছাড়াও পড়ুন:

An dakatar da shugabannin sakandare 6 a Sakkwato kan zargin cin amanar aiki

Gwamnatin jihar Sakkwato ta dakatar da wasu shugabannin makarantun sakandare guda shida kan zargin karbar kudi daga hanun dalibai na bisa ka’ida ba.

Kwamishinan Ilimin Firamare da Sakandare na jihar, Farfesa Ahmad Ladan Ala ne ya amince da dakatarwar.

Matasan Nijeriya sun koma yin ci-rani a Nijar da Chadi Akasarin masu kai mana hare-hare daga jihohin da suka kewaye mu suke – Gwamnatin Filato

Ana dai zargin dakatattun shugabannin makarantun ne da karɓar kudin jarabawa daga hannun daliban da suka kammala karamar sikandare (JSS) ba tare da izinin gwamnati ba, wasu daga cikinsu kuma ana zargin su sun walaƙanta shugabanni da ke sama da su.

Shugabannin da aka dakatar sun hada da shugabar makarantar mata ta Nana da Makarantar gwamnati ta Gagi (GDSS) da makarantar sakandare ta Mana da Kwalejin Giginya da Baisic ta Mana da sakandaren Silame.

Kwamishinan ya kuma kafa kwamitin mutum biyar karkashin jagorancin Farfesa Mustapha Namakka Tukur don su bincika zarge-zargen da aka yi wa shugabannin da aka dakatar.

Kwamishina, a cikin sanarwar da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar, Ibrahim Muhammad Iya, ya fitar ya umarci shugabannin su mika ragamar makarantun ga hannun mataimakansu na mulki nan take.

“Ma’aikatar ilmi za ta ci gaba da yin tsayin daka ta tabbatar da tarbiya da rike amana da gaskiya a dukkan makarantun jihar Sakkwato,” a cewarsa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Dakatar Da Shugabannin Makarantun Sakandire 6 A Sakkwato Kan Rashin Bin Dokokin Aiki
  • An dakatar da shugabannin sakandare 6 a Sakkwato kan zargin cin amanar aiki
  • Hukumar Alhazai Ta Jigawa Za Ta Shirya Taron Bita Na Musamman Ga Jami’anta
  • Hukumar Bunkasa Ilimin Manyan Makarantu Ta Shirya Taro Na Musamman Ga Jami’anta
  • Sojoji Sun Cafke Babban Kwamandan IPOB
  • UNICEF Ya Ba Da Tallafin Kayayyakin Aiki Ga Cibiyoyin Lafiya A Kirikasamma
  • Hukumar Tarayyar Turai Ta Gabatar Da Shawarar Jingine Aiki Da Yarjejeniyar KAsuwanci Da HKI
  • Karamar Hukumar Birnin Kano Ta Kaddamar Da Kula Da Lafiyar Ido Kyauta
  • Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi