An Kaddamar Da Shirin Dashen Itatuwa A Gundumar Bakori
Published: 20th, September 2025 GMT
Gundumar Bakori ta jihar Katsina ta kaddamar da shirin dashen itatuwa domin rage zaizayar kasa a yankin.
A cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin aikin gona, Cigarin Bakori Alhaji Shehu Ishiye ya fitar, ya bayyana cewa Hakimin Bakori, Makaman Katsina Alhaji Garba Tukur Idris, ya yi kira ga jama’a da su daina sare itatuwa ba bisa ka’ida ba don kare muhalli.
Ya jaddada bukatar wayar da kai kan muhimmancin dasa itatuwa wajen habaka tattalin arziki.
Alhaji Garba Tukur Idris ya ce gundumar za ta tabbatar da cewa an kula da itatuwan da aka dasa yadda ya kamata domin cimma burin kare muhalli.
Hakimin ya bayyana cewa taron ya kuma kunshi rabon kayan abinci da tabarmi ga wadanda hare-haren ‘yan bindiga suka shafa a gundumar.
Alhaji Garba Tukur Idris ya sake tabbatar da kudirin masu rike da sarautun gargajiya na gundumar wajen tallafawa marasa galihu a cikin al’umma, tare da samar da muhalli mai kyau domin ingantacciyar rayuwa.
Suleiman Sani Rigachikun
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Dashen Itatuwa
এছাড়াও পড়ুন:
Sashen Raya Kimiyya Da Fasaha Na Sin Ya Kai Babban Matsayi Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Karo Na 14
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp