Leadership News Hausa:
2025-09-17@20:30:16 GMT

Ranar Hausa: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka

Published: 31st, August 2025 GMT

Ranar Hausa: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka

Matsala ta farko na yi mata take da:

1. Sai Bango Ya Tsage….: Gaskiyar diyan Bawo, da yake cewa, ‘Sai bango Ya tsage, kadangare ke samun wurin shiga. Lallai babu yadda za a yi gwamnati da sauran manyan al’umma suna kallon harshen Hausa a matsayin wani harshe wanda nazartarsa koma baya ne ga al’umma kuma a samu wannan harshen ya ci gaba da yaduwa kamar wake dan arba’in.

An taba yin wani shugaban kasa da ya ayyana nazartar wasu darussa a matsayin bata lokaci domin bai ma san a ina za su yi aiki ba. Duk kuwa da kasancewar duk kasar da ya ratsa a Arewacin kasar domin yakin neman zabe, da harshen Hausa yake magana.

Abin da nake nufi a takaice, gwamnati ta yi watsi da harkar koyo da koyarwar harshen Hausa, domin a ganinta ba shi da amfani, wannan ne ya sa har harshen Yarabanci wanda ko kwalar harshen Hausa bai kai ba a wajen tara manyan manazarta kama daga Farfesoshi da kuma yawan gidajen yada labarai da jaridu da makarantun duniya wadanda suke amfani da harshen Hausar ba.

Kadan daga cikin gudunmuwar da gwamnati ta bayar wurin ci bayan nazarin harshen Hausa sun hada da: a. Mayar da karatun Hausa a matakin sakandare ZAbI. b. Tsaurara matakin neman gurbin karatun jami’a domin karantarsa da JAMB suka yi. c. Rashin bayar da tallafin karatu domin nazartar harshen kamar yadda sauran harsuna da kuma gwamnatoci ke yi a wasu darussan. Da sauransu da yawa.

 

Na sa wa batu na biyu taken:

2. Ka ki Naka, Duniya Ta So Shi: Hakika da yawan al’ummar Hausawa ba sa alfahari da harshen Hausa musamman ta fannin zuwa su nazarci harshen kamar yadda Turawa da Larabawa ke nazartar nasu harsunan, duk kuwa da irin tasirin da hakan yake da shi a rayuwa bakidaya. Amma a haka sai ka iske kasashen waje sun dage wajen gabatar da rubuce-rubuce da yada harshen ta kafafe mabambanta har ma da karantar da shi a manyan jami’o’in duniya. Amma mu a nan kallon uku aho ake yi wa da yawan wadanda suke nazartar Hausa. Abin takaicin masu wannan dattin kwakwalwar kuma su ne za ka tarar a kaso 90 na rubututtukansu a shafukansu na sada zumunta da Hausa suke yi, idan suna koyon littafan addini duk sai an fassara masu da Hausa ko da kuwa da wane irin harshe aka rubuta littafin addinin nan, ko ka san batan bakatantan!

Abin dariya abin tausayi, wai kunama ta harbi dan tsako. Yanzu bai zamo abin kunya ba, a ce kasa kamar Nijar wadda masu magana da harshen Hausar kasar ba su kama kafar rabin na Arewacin Nijeriya ba, amma a ce kasar sun ayyana harshen a matsayin harshen kasa. Me ya sa gwamnatocin Arewa ba za su ayyana shi a matsayin harshen Arewacin kasar ba, idan ana tokabon kasar bakidaya tana da manyan harsuna guda 3?

Har wa yau, wasu daga cikin malamai suna bayar da gudummuwa wajen kin nazartar wannan harshe, musamman ta fuskar yadda suke mu’amalantar dalibansu musamman ta fuskar kwauron maki da bayar da wahala yayin bincike na ba gaira babu dalili, wanda a hasashena ba komai yake kawo haka ba, sai don kawai a razana ka, wanda hakan ne ya razana da yawa suka kauracewa nazartar harshen.

 

Batu na uku na yi masa ishara da:

3. Idan An Bi Ta barawo.. Lallai malamai da daliban harshen ya kamata su ci gaba da ayyukan da na san an faro da dadewa na fassarar muhimman kalmomi na fannonin ilimi da dama, wanda hakan shi zai ba wa masu nazartar harshen dama wajen kutsawa kowane fanni da yin kaka-gida wajen fito wa da dalibai abubuwan a sarari domin saukaka fahimtar darussan. Kamar yadda sauran harsunan duniya irin su: Larabci da Turanci da Indiyanci da Sinanci (Chinese) da sauransu, suka yi.

 

Gudummuwar Harshen Hausa.

Ido ba mudu ba, amma ya san kima. Ga kadan daga cikin wasu gudunmuwar da harshen yake bayarwa a takaice:

1. Babu wani littafi na addini da ake karantarwa a kasar nan wanda ba a fassara ba ko ake yunkurin fassara shi zuwa harshen Hausa.

2. An fassara da yawan littattafan kimiyya da na Lugga da na lissafi hada har da na tarihi da sauransu domin ci gaban al’umma.

3. Babu wata kafar sadarwa da harshen Hausa bai yi zarra a cikinta ba, kama daga Instagram da Tiktok da WhatsApp da D (Twitter) har ma da uwa uba Facebook.

Haka nan, Harshen Hausa shi ne ya mamaye kafafen yada labarai na Amuruka da Sin da Faransa da sauransu. Bar batun jaridu da kullum ake fito da su cikin harshen domin nusar da al’umma halin da duniya ke ciki.

4. Bugu da kari, Manazarta sun samar da kundayen bincike na falsafa da al’ada hadi da adabi da ma harshe. An kuma rubuta manya da kananan littattafai wadanda ba wanda ya isa ya fadi adadinsu da irin fannonin da littattafan suka tabo. Ana kuma samar da mukaloli a fagage mabambanta ba don komai ba sai don kokarin ciyar da harshen da kasa da kuma al’umma gaba.

 

SHAWARWARI:

Akwai matakai da yawa da ya kamata a dauka domin dawo da martabar koyon wannan harshe mai albarka. Ga kadan daga ciki:

1. Tafiya da zamani.

2. Saukaka hanyoyin koyo da koyarwa.

3. Mayar da nazarin harshen wajibi a kananan makarantu na firamare da sakandire.

4. Sanya koyon shi ya zama wajibi ga duk dalibin kasar waje da ya zo yin karatu a kasar nan, kamar yadda da yawan kasashe suke yi.

5. Kutsawa fannonin kimiyya da fasaha da fannin likitanci da magunguna domin ci gaba da gudanar da nazarce-nazarce.

6. Sanya shi a cikin darussan dole Gens/GSE manhajar koyarwar jami’o’i da kwalejojin ilimi da na kimiyya.

7. Mayar da harshen Hausa ya zamo harshen hukuma a yankin Arewa idan ma ba kasar (Nijeriya) duka bakidaya ba.

8. karfafa gwiwar iyaye da ta abokai har ma da uwa uba malamai ga masu nazarin harshen Hausa.

9. A aje kwarya a burminta. Ka da a dauki aikin da aka san manazarcin harshen Hausa ne kadai zai iya a danka shi ga wani, musamman abin da ya shafi ayyukan fassara da na talife-talife.

Aiwatar da wadannan da ma wasu abubuwa za su taimaka gaya wajen ganin an dawo da kima da kuma martabar nazarin harshen Hausa.

 

Kammalawa:

A takaice wannan takarda ta tattaro wasu bayanai ne da suka shafi matsalolin da harshen Hausa yake fuskanta wadanda suka haddasa mashi koma baya, da kuma gudummuwar da harshen Hausar yake bayarwa a zamanace da addini da ma rayuwa bakidaya, daga karshe kuma takardar ta bijiro da wasu hanyoyi da za a bi domin ganin an dawo da martabar nazartar harshen a kasa bakidaya.

Jikamshi, ya rubuta albarkaci bikin Ranar Hausa ta Duniya ta bana da aka yi bikinta ran 26/08/2025

 

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: da harshen Hausa nazartar harshen nazarin harshen kamar yadda da sauransu

এছাড়াও পড়ুন:

Za A Kaddamar Da Fim Mai Taken 731 A Sassan Duniya

Tun daga ranar 18 ga wata, za a kaddamar da fim mai taken 731 a sassan duniya da dama, fim din da ya bayyana yadda rundunar sojojin kasar Japan da suka kutsa kasar Sin suka gudanar da nazari a kan hada makamai da cututtuka tare da gudanar da gwaje-gwaje a jikin al’ummar kasar Sin, a birnin Harbin na lardin Heilongjiang da ke arewa maso gabashin kasar Sin, kafin al’ummar kasar Sin su cimma nasarar yaki da su.

 

A ranar 19 ga watan Agusta, hukumar kula da tsaron kasar Rasha ta fitar da wata takardar sirri da yanzu gwamnati ta mayar da ita ba ta sirri ba, wadda ta nuna cewa, domin neman yin amfani da makaman da aka hada da cututtuka a yakin kutsen da suka kaddamar a kasar Sin, reshen rundunar sojojin Japan da suka yi kutse a kasar Sin mai lambar 731, sun yi ta gudanar da gwaje-gwaje a jikin al’umma, har ma sun kai harin boma-bomai da aka samar da cututtuka a kan daruruwan Sinawa, don neman tantance ingancin cututtuka ta hanyar kirga mutanen da suka harbu da cututtuka.(Lubabatu)

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • Sowore Ya Maka DSS, Meta da X A Kotu Kan Take Masa Haƙƙi
  • DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya
  • ALGON ta karrama Gwamna Buni da lambar yabo kan kawo ci gaba a Yobe
  • DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu
  • DSS Ta Maka Sowore, Facebook Da X A Kotu Kan Wallafa Rubutu Game Da Tinubu
  • ’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhu
  • Ɗan Majalisar Tarayya Ya Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-haren Ta’addanci A Sakkwato 
  • An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar
  • Za A Kaddamar Da Fim Mai Taken 731 A Sassan Duniya