CBN ya rage kuɗin ruwa zuwa kashi 27 cikin 100
Published: 23rd, September 2025 GMT
Kwamitin da ke kula da tsare-tsare da manufofin kuɗi na Babban Bankin Najeriya (CBN) ya zaftare maki 60 daga nauyin kuɗin ruwa da ke kan masu karɓar basussuka.
Wannan dai shi ne karo na farko cikin shekaru biyar da aka samu babban bankin ya yi rangwamin kuɗin ruwa a ƙasar.
CBN ɗin ya ce kwamitin a wannan Talatar ya rage yawan kuɗin ruwan daga kashi 27.
Gwamnan Babban Bankin, Olayemi Cardoso, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai bayan kammala taron kwamitin karo na 302 da ya gudana a Abuja.
Cardoso, ya bayyana cewa an kuma mayar da buƙatar adana tsabar kuɗi a manyan bankuna zuwa kashi 45 cikin ɗari, yayin da na bankunan ’yan kasuwa aka bar shi a kashi 16 cikin ɗari.
Haka kuma, Babban Bankin ya ƙaddamar da matakin sanya kashi 75 cikin ɗari na tsabar kuɗin da aka adana mallakin ma’aikatu da hukumomin gwamnati da ba sa cikin asusun gwamnati na bai-ɗaya wato TSA.
Cardoso ya bayyana cewa wannan mataki na kwamitin na zuwa ne bayan sauƙin da aka fara gani a farashin kayayyakin a ’yan kwanakin nan.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: kuɗin ruwa Olayemi Cardoso
এছাড়াও পড়ুন:
CORET Ta Yaba Da Nasarar Shirin Ciyarda Daliban Makarantun Makiyaya
Haddadiyar Kungiyoyin Makiyaya na kasashen Africa (CORET) ta bayyana cewa an samu karin yawan ɗalibai a makarantun makiyaya cikin watanni goma da aka fara shirin ciyar da ɗalibai.
Babban Sakataren CORET, Muhammed Bello Tukur, ya bayyana haka a taron kwana ɗaya da aka gudanar a Kaduna domin ƙara wa ma’aikata da abokan hulɗarsu ƙwarewa kan harkar ciyar da ɗalibai.
Taron ya mayar da hankali ne wajen duba nasarorin da aka samu cikin watanni goma tun lokacin da aka fara shirin a Ladduga, Karamar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna, da kuma Maigatari a Jihar Jigawa.
Babban Sakataren CORET, Muhammed Bello Tukur, ya bayyana cewa shirin ya shafi makarantun makiyaya kawai a jihohin Jigawa da Kaduna.
Ya ce ciyarwa na daga cikin manyan matsalolin da ke sa yara barin makarantu, don haka shirin ya ƙunshi amfani da al’ummomin yankuna wajen samar da abincin ɗalibai.
Ya ƙara da cewa an sayi kayan abinci daga cikin al’umma tare da haɗa su wajen tabbatar da ingancin abincin da ɗalibai ke ci. Bugu da ƙari, CORET ta samar da rijiyoyin burtsatse domin tabbatar da samun ruwa na sha da na yau da kullum.
Muhammed Bello Tukur ya yaba da irin goyon bayan da abokan hulɗa musamman ECOWAS, da kuma Gwamnatin Tarayya da Jihohi ke bayarwa wajen tabbatar da nasarar shirin.
A nasa jawabin, Ko’odinatan Shirin, Dakta Abdu Umar Ardo, ya bayyana cewa shirin ya zama nasara daga komai zuwa abu mai amfani tun da jihohin suka rungumi karatun ’ya’yan makiyaya.
Haka kuma, a kasidarsa, Bashir Abbo ya bayyana cewa bincike ya nuna akwai bukatar ƙwararrun malamai, farfaɗo da kwamitocin gudanar da makarantu da ƙarfafa ƙungiyoyin mata domin su riƙa taka rawar da ta dace.
Ya ce ɗaukar ƙarin malamai ƙwararru zai samar da sakamako mai kyau nan gaba.
Mahalarta taron sun fito ne daga Ladduga, yayin da wasu daga cikin mahalarta daga Karamar Hukumar Maigatari ta Jihar Jigawa suka halarci taron ta yanar gizo.
COV: Adamu Yusuf