Komai Nisan Dare Gari Zai Waye
Published: 21st, September 2025 GMT
Sabo da irin mawuyacin halin da ake ciki ta fannin tsarin jagorancin duniya musamman a daidai wannan lokaci, ya sa shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar inganta tsarin jagorancin duniya a kwanakin baya, shawarar da ta yi nuni da cewa, ya kamata a tsaya tsayin daka a kan kin yarda da daukar matakai na kashin kai, tare da kiyaye matsayin MDD, don ta taka rawar da ba wanda zai iya maye gurbinta a cikin tsarin jagorancin duniya.
A sati mai zuwa, za a gudanar da babbar muhawara da ma babban taron tabbatar da shirin samar da kasashe biyu a yayin babban zauren MDD, kafin haka, manyan kawayen Amurka irinsu Birtaniya da Faransa cewa suka yi za su amince da kafuwar kasar Palasdinu, lamarin da ya sake shaida cewa, babu wanda zai iya hana adalci. Lokacin da Amurka ta kada kuri’ar nuna rashin amincewa, ba yarjejeniyar zaman lafiya kadai ta jefa cikin kwadon shara ba, har da matsayinta na jagorancin duniya.
Tabbas “komai nisan dare gare zai waye”, duk duhun da Gaza ke ciki, haske zai bayyana. Fatan kasa da kasa na wanzar da zaman lafiya zai kai ga kawar da dukkan abubuwan da ke tarnaki tare da shimfida dauwamammen zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya, wanda hakan zai bude mana sabon babin tsarin jagorancin duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: tsarin jagorancin duniya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Da Ɓullar Cutar Mpox A Jihar
Ya ce Kano na cikin hatsari saboda cunkoson jama’a da kuma zirga-zirgar mutane daga wurare daban-daban.
KNCDC ta gudanar da cikakken bincike a Ungogo, inda aka duba unguwar da marar lafiyan yake da kuma asibitocin da ya ziyarta.
Duk wanda aka bincika yana cikin ƙoshin lafiya kuma babu wanda ya kamu da cutar.
Farfesa Abbas ya jaddada muhimmancin wayar da kan jama’a don hana yaɗuwar cututtuka.
Ya nemi kafafen watsa labarai su ci gaba da yaɗa bayanan lafiya ga al’umma.
Ya kuma buƙaci jama’a su kasance masu lura, inda ya tabbatar da cewa Kano tana da tsarin sa ido da shiri don shawo kan kowace irin cuta nan gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp