Matasan Nijeriya sun koma yin ci-rani a Nijar da Chadi
Published: 19th, September 2025 GMT
A yau a Nijeriya, kalmar “Japa” ta zama gamagari wajen bayyana yadda matasa da dama ke barin ƙasar domin neman ingantacciyar rayuwa a wasu ƙasashe.
Abin da ya bambanta shi yanzu shi ne inda suke nufa: ba kawai Turai da Amurka ba kawai, har ma da ƙasashen Afirka maƙwabta.
Yawaitar tsadar rayuwa da ƙarancin ayyukan yi da rashin tsaro, da kuma faɗuwar darajar Naira sun sanya matasa su fara duba wasu ƙasashen Afirka a matsayin mafaka.
Maimakon tsallaka tekun Bahar Rum da haɗarin mutuwa, da dama daga cikinsu sun fara kallon ƙasashen Nijar da Chadi da Mali, Kwat D’Ibuwa da Kamaru da Jamhuriyar Binin a matsayin wuraren da za su iya fara sabuwar rayuwa.
Binciken Aminiya ya gano cewa, a yau dubban matasa daga Arewa da Kudancin Nijeriya sun tsere zuwa maƙwabtan ƙasashe, inda suke gudanar da sana’o’i ko haƙar ma’adinai ko shiga kasuwancin canjin kuɗi. Wasu ma sun koma neman ilimi a jami’o’in ƙasashen da suka fi samun kwanciyar hankali.
Masu lura da al’amura sun ce wannan sabon salo na hijira ko ci-rani yana nuna yadda matsalolin Nijeriya suka tsananta, har matasa ke ganin ƙasashen da a da suke kallo a matsayin marasa ci-gaba sun fi tasu sauƙin rayuwa.
Rayuwar baƙin haure
A biranen Nijar, musamman Maraɗi da Yamai, ana iya ganin ɗimbin ’yan Nijeriya suna gudanar da ayyukan yau da kullum. Wasu suna zama a ƙauyuka, wasu kuma a cikin manyan birane.
Rayuwarsu ba ta da sauƙi, amma duk da haka suna ganin ta fi ta gida sauƙi. Daga ƙakin haya mai cunkoso da suke raba shi tare da abokan tafiyarsu, zuwa cin abinci mai sauƙi kamar tuwon gero da miyar kuɓewa, matasan suna jurewa don cimma manufar da ta kawo su ta samun abin dogaro da kai.
Habibu Abdullahi, matashi daga Maiduguri, ya ce: “A da ’yan Nijar ne ke zuwa Nijeriya domin neman aiki. Amma yanzu mu ne muke zuwa wajensu saboda CFA ta fi Naira ƙarfi.”
Wasu kuma sun ce rayuwar baƙin haure tana da tsada, amma ribar da suke samu daga sana’o’in da suke yi na sa su ci gaba da zama.
Sana’o’in da suke yi
A Maraɗi da Zinder, sana’ar ɗinki ta zama abin dogaro ga ɗimbin matasan Nijeriya. Umar Mukhtar, tela ne daga Katsina, ya ce: “A nan kullum akwai kwastomomi. A Kano zan iya shafe mako ba tare da na yi ɗinki ba, amma a nan babu ranar da babu aiki.”
Umar Papa, wanda ya kammala karatun Biochemistry amma bai samu aiki a Nijeriya ba, yanzu yana aikin gini a Nijar. Ya bayyana cewa a rana ana biyan shi CFA3,000 zuwa CFA5,000, wato fiye da Naira 10,000. A wata guda, zai iya tara har N400,000 — abin da bai taɓa tsammani ba a gida.
Nasir Mustapha daga Malumfashi, kafinta ne da ya koma Nijar. A cewarsa, “A Nijeriya aikin kafinta yana da wahala saboda babu rarraba aiki. Amma a nan zan iya yin kujera guda na samu N65,000 a cikin kwana uku, alhali a gida sai na wahala in samu rabin hakan.”
A Djado, wani yanki mai tazara daga Maraɗi, matasa daga Nijeriya sun shiga sana’ar harkar haƙar zinari. Abdulkareem Dogo, wanda ya kammala karatu a Jami’ar Maiduguri, ya ce: “Haƙar zinari tana da haɗari, amma tana da riba. Gram ɗaya da aka tace zai iya kaiwa N170,000.”
Ya bayyana yadda suke shiga ramuka masu zurfi fiye da kafa 150, suna rataye da igiya, suna tono ƙasa cikin zafi da ƙura. A rana sukan yi zango guda na awa shida, sannan a fita wasu su shiga. Duk da haɗarin da ke tattare da wannan sana’a, yawanci matasan suna ci gaba da shiga saboda fatan samun arziki cikin sauri.
A biranen Diffa da Ƙonni, matasan Nijeriya sun kafa kasuwancin hada-hardar kuɗi ta POS da canjin kuɗi. Malam Musa Abdulƙadir, wanda ya buɗe ofishinsa shekaru biyu da suka gabata, ya ce, “A yau Naira ce ke yawo a kasuwannin kan iyaka, amma ana juya ta zuwa CFA domin samun ribar canji.”
A bara, CFA1,000 ana canza ta a kan N1,870, amma yanzu ta kai N2,800 — alamar yadda darajar Naira ke ci gaba da faɗuwa. Wannan ya sanya kasuwancin canjin kuɗi zama wata hanya ta samun kuɗin shiga mai yawa ga matasa.
Matsalolin da suke shiga
Duk da nasarar da wasu suka samu, akwai ƙalubale da dama. Mafi girma daga ciki akwai:
Wahalar zama: Mafi yawa daga cikin matasan na rayuwa ne a ƙakunan haya masu cunkoso. Mutum uku ko huɗu na kwana a ɗaki ɗaya, suna raba shimfiɗa.
Haɗarin lafiya: Rashin isasshen abinci mai gina jiki, gajiyar aiki da kuma rashin samun isasshen jinya suna jefa su cikin haɗari.
Takurar jami’an tsaro: A wasu lokuta ’yan sanda ko sojojin ƙasashen da suke ciki na tsangwamar su, suna karɓar cin hanci ko kuma suna korar su saboda rashin takardun zama.
Haɗarin sana’a: Musamman a haƙar zinari, inda rami zai iya ruftawa ya binne masu aiki gaba ɗaya. Wasu kuma suna shaƙar ƙura da hayaƙi har su kamu da cututtuka.
Alherin da suke samu
Duk waɗannan ƙalubale, matasan sun bayyana alherai da nasarorin da suke samu.
Ibrahim Lawal, mai san’ar ɗinki a Mali ya ce, “Na tafi Bamako ne bayan na gaji da zama Kano babu aiki. A nan ina samun CFA100,000 a wata, abin da ya fi abin da zan iya samu a gida gaba ɗaya.”
Shi ko Mubarak Musa ɗan kasuwa a Abidjan, ya ce, “Na fara sayar da kayayyakin gwanjo a Abidjan. Yanzu duk wata ina iya samun N500,000. Duk da cewa aikin na da wahala, amma aƙalla ina iya tallafa wa iyali na a gida.”
Deborah Ufedou, ɗaliba a Binin ta ce, “Na tsere ne saboda yajin aiki ASUU (Ƙungiyar Malaman Jami’a) domin na iya kammala karatu. A lokaci guda na fara sayar da kilishi da dambun nama. A kowane mako ina kashe N170,000 amma ribata na kaiwa N400,000 zuwa N430,000.”
Kira ga gwamnati
Matasan da muka yi hira da su sun roƙi gwamnati ta samar da ayyukan yi a gida, ta taimaka wa matasa su sami tallafin jari, sannan ta inganta tsaro domin a rage gudun hijira, sa’annan ta sauƙaƙa tsarin kasuwanci domin matasa su iya yin sana’a ba tare da wahala ba.
Habibu Abdullahi ya ce: “Idan gwamnati ta samar da aiki da tsaro, babu wanda zai bar iyalinsa ya shiga ƙasashen da ba ya jin harshensu. Amma muna barin gida ne saboda babu madadin.”
Tsohon jakadan Nijeriya, Mohammed Ibrahim, ya bayyana cewa wannan sabon salo na hijira alama ce ta tsanani da ƙasar ke ciki. A cewarsa, “Tun da daɗewa matasa kan yi hijira, amma abin da ya bambanta yanzu shi ne yawansu ya ƙaru kuma sun fi karkata zuwa ƙasashen Afirka.”
Ya kuma ba da labarin wata tawaga ta diflomasiyya a shekarar 2006 tare da jakadun Jamus da na Birtaniya a lokacin, wanda ya yi tattaki daga birnin Tripoli na Ƙasar Libya ta cikin hamadar Sahara zuwa Nijar da Nijeriya.
Ya ce, tafiyar ta taƙaita ne saboda tsananin yanayi da aka fuskanta a cikin sahara.
Da yake tsokaci a kan yanayin ƙaura, ya ce ƙauran da ’yan Nijeriya ke yi zuwa wasu ƙasashe ba na gefe ɗaya ba ne. ‘’Kamar yadda mutane ke ganin ’yan Nijeriya na yin hijira zuwa wasu ƙasashe, ‘akwai wassu mutane daga ƙasashe da dama daga ƙasashen Afirka da ke maƙwabtaka da su ma suna ƙarasowa suna shiga Nijeriya don neman ingantacciyar dama na rayuwa da samun sana’a mai nagarta.
Masu nazari sun ce idan aka ci gaba da barin lamarin haka, Nijeriya za ta ci gaba da rasa matasa masu ƙwarewa. Wannan kuma zai shafi tattalin arzikin ƙasar nan gaba.
Rahoton Aminiya ya nuna cewa “Japa” zuwa ƙasashen Afirka ba wai ba ce mafita ga matasa ba ce kawai, illa ce kuma ga Nijeriya baki ƙaya.
Idan gwamnati ta yi watsi da matsalolin da suka haddasa wannan hijira, za a iya wayan gari matasa da dama sun bar ƙasar, wanda hakan zau bar giɓin da zai wahalar da tattalin arziki da ci-gaban ƙasa.
Fassara: Ahmed Ali, Kafanchan da Ahmed Muhammad Bauchi
Rahotanni Daga Tijjani Ibrahim ( Maradi) da Sani Ibrahim Paki (Kano) da Hamisu Kabir Matazu (Maiduguri) da Gbenga Adebayo da Eugene Agha (Lagos) da kuma Willie Bassey (Yenagoa)
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ci rani Najeriya Nijar a wasu ƙasashe Nijeriya sun
এছাড়াও পড়ুন:
Chadi: Majalisa ta amince a baiwa shugaban kasa damar ci gaba da Mulki har karshen rayuwa
Majalisar dokokin kasar Chadi ta amince da gyare-gyaren kundin tsarin mulkin kasar da zai tsawaita wa’adin shugabancin kasar daga shekaru biyar zuwa bakwai da kuma baiwa shugaban kasar damar ci gaba da mulki na tsawon wa’adi maras iyaka.
Majalisar dokokin kasar Chadi ta amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar a ranar Litinin da kuri’u 171, yayin da aka kada kuri’a daya tilo da taki amincewa da hakan.
A ranar 13 ga watan Oktoba ne aka shirya kada kuri’ar karshe a majalisar dattawa, a cewar sanarwar da shugaban majalisar Ali Koloto Chaimi ya fitar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito. Sannan kuma shugaban kasar zai sanya hannu kan kundin tsarin mulkin sannan ya zama doka.
Shugaban kasar Chadi, Mahamat Idriss Deby ya karbi mulkin kasar ne bayan kisan mahaifinsa tsohon shugaba Idriss Deby, a lokacin da ya ziyarci sojojin da ke yaki da mayakan ‘yan tawaye a arewacin kasar a shekarar 2021.
Deby ya yi ikirarin samun nasara bayan zaben da aka gudanar bayan shekaru uku na mulkin soja a watan Mayun 2024, sannan kuma aka gudanar da zaben ‘yan majalisar dokoki a watan Disamba, wanda ya bai wa jam’iyya mai mulki rinjayen kujeru.
An samu cece-kuce game da sakamakon zaben, bayan da madugun ‘yan adawa kuma firaministan kasar Succe Massara ya yi ikirarin samun nasara, ikirarin da hukumar zaben kasar ta yi watsi da shi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Yunkurin Kasa da Ka Na Kauracewa Isra’ila September 17, 2025 Kwamitin bincike na MDD ya zargi Isra’ila da aikata “kisan kare dangi” a Gaza September 17, 2025 Iran da Saudiyya sun bukaci hadin kan Musulmi game da halin da ake a yankin September 17, 2025 Duniya na tir da sabon farmakin Isra’ila kan Gaza September 17, 2025 Akalla Falasdinawa 78 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila a Gaza September 17, 2025 Akalla Falsdinawa 78 Ne Suka Yi Shahada A Yau A Gaza. September 16, 2025 Isra’ila Ta Kai Hari A Tashar Jirgin Ruwan Hudaida Dake Yamen September 16, 2025 Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki 5 A Wajen Taron kere-kere . September 16, 2025 Iran Ta Bukaci IAEA Tayi Tir Da Harin Da Isra’ila Ta Kai A Tashoshin Nukiyarta. September 16, 2025 Jonathan Zai Jagoranci Taron Tattaunawa Kan Dimokuraɗiyya A Ghana September 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci