Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Ɓullar Cutar Mpox A Jihar
Published: 23rd, September 2025 GMT
Ya ce Kano na cikin hatsari saboda cunkoson jama’a da kuma zirga-zirgar mutane daga wurare daban-daban.
KNCDC ta gudanar da cikakken bincike a Ungogo, inda aka duba unguwar da marar lafiyan yake da kuma asibitocin da ya ziyarta.
Duk wanda aka bincika yana cikin ƙoshin lafiya kuma babu wanda ya kamu da cutar.
Farfesa Abbas ya jaddada muhimmancin wayar da kan jama’a don hana yaɗuwar cututtuka.
Ya nemi kafafen watsa labarai su ci gaba da yaɗa bayanan lafiya ga al’umma.
Ya kuma buƙaci jama’a su kasance masu lura, inda ya tabbatar da cewa Kano tana da tsarin sa ido da shiri don shawo kan kowace irin cuta nan gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Tarayya ta fara shirin sayar da matatun manta ga ’yan kasuwa
Gwamnatin Tarayya ta ce ƙofofinta buɗe suke ta sayar da dukkan matatun manta na Warri, Fatakwal da Kaduna ga ’yan kasuwa domin ƙarfafa gasa a fannin tace mai a Najeriya.
Mai ba Shugaban ƙasa Bola Tinubu shawara kan harkokin makamashi, Olu Verheijen ce ta bayyana hakan a wata hira da Bloomberg TV a gefen taron makamashi na ADIPEC da aka gudanar a Abu Dhabi, Hadaddiyar Daular Larabawa, ranar Talata.
Hafsan sojin sama ya umarci a yawaita yi wa ’yan ta’adda ruwan bama-bamai NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Cutar BasirVerheijen ta ce wannan mataki na daga cikin shawarwarin da ake dubawa don inganta harkar man fetur a Najeriya.
“Daya daga cikin matakan da za a iya la’akari da su kenan, musamman idan aka samu wanda yaje da kwarewa da kuma jarin da zai iya sayen su,” in ji ta.
Ta ce matatun man da a baya suka dade suna aiki a ƙarƙashin tallafin gwamnati, yanzu sun sami kishiyoyi bayan cire tallafin man fetur.
“Yanzu da muka cire tallafin, mun kawar da duk wani tarnaki da ke cikin wannan kasuwar ta man fetur,” kamar yadda ta fada.
A watan Oktoba, Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) Limited ya sanar da fara cikakken bincike na fasaha da kasuwanci kan matatun mai guda hudu da gwamnati ke da su.
Tun a watan Yuli, Shugaban kamfanin Group, Bayo Ojulari, ya ce aikin gyaran matatun ya ɗan samu tsaiko, yana mai cewa kamfanin na fatan kammala sake duba su kafin ƙarshen shekara.