Hauhawar farashi ya ragu a watan Agusta — NBS
Published: 16th, September 2025 GMT
Hukumar ƙididdigar a Najeriya NBS ta bayyana cewa an samu raguwar hauhawar farashin kaya a watan Agusta idan aka kwatanta da watan Yulin da ya gabace shi.
Cikin sabbin alƙaluman da NBS ta fitar a ranar Litinin sun nuna cewa an samu raguwar kashi 1.76 a watan Agustan saɓanin watan Yulin, wanda ya nuna karo na hudu ke nan a jere hauhawar farashin yana sauka.
Rahoton na hukumar NBS na zuwa ne kwanaki bayan da Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin karya farashin kayan abinci ƙasar.
A watanin baya-bayan an riƙa samun raguwar hauhawar farashin kayyaki a ƙasar.
Ko alƙaluman da NBS ta fitar a watan Yuni, ta bayyana cewa hauhawar farashi a Najeriya ya sauka zuwa kashi 22.22 daga 22.97 da aka samu a watan Mayu.
A baya dai dai an yi ta kiraye-kirayen gwamnatin ƙasar ta ɗauki matakan rage hauhawarar farashi domin magance tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Hauhawar Farashi
এছাড়াও পড়ুন:
DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu
Hukumar Tsaron Farin Kaya a Nijeriya DSS, ta gurfanar da fitaccen ɗan gwagwarmayar nan, Omoyele Sowore a kotu.
A ƙunshin ƙarar da DSS ta gabatar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta haɗa da shafukan sada zumunta na X da kuma Facebook, inda take zarginsu da ba da ƙofar aibata Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Bida Poly ta sa sojoji kula da jarrabawar ɗalibai Kukan al’umma kan lalacewar hanyar DukkuDarekan shigar da ƙara na Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya, M.B Abubakar da wasu lauyoyi huɗu —M.E. Ernest da U.B. Bulla da C.S. Eze da kuma E.G. Orubor, ne suka shigar da ƙarar a madadin Gwamnatin Tarayya da kuma hukumar ta DSS.
DSS wadda ta kafa hujja da sashe na 24 da ke cikin kundin dokokin yanar gizo, ta ce Sowore ya yi amfani da shafukansa na dandalan sada zumunta na X da Facebook wajen wallafa wani saƙo da ke cin mutuncin Shugaba Tinubu.
Tun dai a farkon watan nan ne DSS ta buƙaci goge wani saƙo da ɗan gwagwarmayar ya wallafa wanda ta riƙa a matsayin bayanan ƙarya, cin zarafi ta yanar gizo da kalaman haddasa ƙiyayya, waɗanda kuma ta ce na iya haddasa rikici su kuma ɓata sunan Najeriya a ƙasashen waje.
Sai dai har zuwa ranar Litinin, 15 ga watan Satumba, babu wani mataki da aka ɗauka na goge saƙon da DSS ɗin ta buƙata.