Faransa ta amince da ’yancin ƙasar Falasɗinu a hukumance
Published: 23rd, September 2025 GMT
Faransa ta bi sahun Birtaniya, Australia da Canada da sauran ƙasashen duniya sama da 140 da suka amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai ’yanci.
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ne ya tabbatar da amincewar gwamnatinsa na kafa ƙasar Falasdinu a hukumance.
Tattalin arzikin Najeriya ya ƙara haɓaka — NBS NEF za ta ƙaddamar da taron zuba jari don bunƙasa ArewaMacron ya bayar da tabbacin ne a yayin da yake jawabi a babban taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York.
Mista Macron ya ce lokaci ya yi da ya kamata a kawo ƙarshen yaƙin Gaza tare da sakin sauran Isra’ilawa 48 da Hamas ke garkuwa da su.
Ya ce lokaci kaɗan ne ya rage wa duniya ta iya wanzar da zaman lafiya, don haka ya ce bai kamata a jira ba.
Mista Macron ya yi Allah-wadai da harin na ranar 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai wa Isra’ila.
Shugaban na Faransa ya ce yana son ganin an samar da zaman lafiya a yankin ta hanyar samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kai da ke zama makwabtan juna.
“Babu wata hujja na ci gaba da yaƙin Gaza”, in ji Macron, yana mai ƙarawa da cewa “ya kamata a kawo ƙarshen komai.”
A yau ne dai tawagar jami’an diflomasiyyan Falasɗinu ta gudanar da bikin ɗaga tutar ƙasar a birnin Landan, kwana guda bayan da Birtaniya ta amince da Falasɗinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Faransa
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Cutar Basir
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Cutar basir na daga cikin cututtukan da mutane da dama ke da mabanbantan ra’ayoyi akan ta.
A lokuta da dama za ka ji yadda mutane ke fadin dalilai daban daban da ke janyo cutar basir, yayin da wasu ke ganin yawan zama ne ke kawo ta, wasu kuwa gani suke yi zaki da maiko ne ke kawo ta.
Wannan shine abun da da yawa daga cikin mutane suka sani kan wannan cuta, sai dai masana kiwon lafiya na da nasu fahimtar daban kan wannan cuta.
NAJERIYA A YAU: Rashin aikin yi da hanyoyin magance su a Najeriya DAGA LARABA: Yadda ‘Yanbindiga Ke Amfani Da Hakar Zinare Wajen Mallakar MakamaiShirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai tattauna ne kan cutar basir da hanyoyin magance ta.
Domin sauke shirin, latsa nan