Bayan wuya sai daɗi: Sakon Tinubu ga ’yan Najeriya
Published: 1st, October 2025 GMT
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa kasar ta shiga sabon salo na gyaran tattalin arziki, kuma matsin da ake ciki na dab da wucewa su zama tarihi.
A cikin jawabinsa ga ’yan kasa don bikin cikar Najeriya shekara 65 da samun ’yancin kai, shugaban ya ce gwamnatinsa ta damu da radadin da mutane ke ciki sakamakon gyare-gyaren da ake aiwatarwa.
Sai dai ya jaddada cewa da Najeriya ba ta dauki matakan da ta dauka ba, da tuni ta shiga halin karyewar tattalin arziki.
Yunwa na kashe ’yan Najeriya, amma Tinubu ko a jikinsa – Atiku DAGA LARABA: Tasirin Bambance-bambance Tsakanin ‘Yan Najeriya Shekara 65 Da Samun ‘Yancin KaiTinubu ya tuna da jaruman da suka kafa kasar, yana mai cewa sun yi imani da cewa Najeriya ce jagorantar bakaken fata a duniya, kasancewar ita ce kasa mafi yawan jama’a bakaken fata.
Ya ce, “Ko da ba mu cimma duk burin da kakanninmu suka yi ba, amma ba mu kauce daga kan layinsu ba. A cikin shekaru 65 da suka gabata, Najeriya ta samu ci gaba mai yawa a fannin bunkasar tattalin arziki, hadin kan al’umma da ci gaban kasa.
“Yayin da sauki ya fi ga masu suka su dinga fadin abin da ya kamata, dole ne mu gane mu kuma yi murna da ci gaban da muka samu. A yau, ’yan Najeriya na da damar samun ilimi da kiwon lafiya fiye da a shekarar 1960,” ,” in ji shi.
Daukar matakai masu tsauriTinubu ya ce lokacin da ya hau mulki, ya gaji tattalin arzikin da ya kusa durkushewa sakamakon kuskuren manufofin kudi da rashin daidaito na tsawon shekaru.
Ya ce: “Mun fuskanci zabin da ya kasance mai sauki: ci gaba da tafiya da yadda ake yi ko kuma mu dauki hanyar gyara mai tsanani. Mun zabi hanyar gyara. Mun zabi gobe fiye da jin dadin yau.”
Shugaban ya ce kasa da shekaru uku bayan daukar wadannan matakai masu wahala, an fara ganin amfaninsu.
Ya ce gwamnatinsa ta kawo karshen tallafin man fetur da kumatsarin musayar kudade da mutane ’yan kalilan ke cin moriyarsa, yawancin al’umma ba sa amfana.
“Mun karkata tattalin arzikin zuwa hanyar da kowa zai amfana, inda kudade ke tafiya zuwa fannin ilimi, kiwon lafiya, tsaro, noma da muhimman ababen more rayuwa kamar hanyoyi, wutar lantarki, intanet da ayyukan tallafi.
“Sakamakon wadannan matakai, yanzu gwamnati ta samu karin kudade a matakin tarayya, jihohi da kananan hukumomi don kula da al’umma da warware matsalolin ci gaba.”
Ci gaban da aka samuTinubu ya ce gwamnatinsa na kokarin gina sabbin hanyoyi, gyara tsofaffi, da kuma gina makarantu da asibitoci.
Ya ce: “Ba mu da isasshiyar wutar lantarki don masana’antu da gidaje, ko kudaden gyaran hanyoyin da suka lalace, ko gina tashoshin jiragen ruwa, layin dogo da filayen jiragen sama masu inganci, saboda rashin zuba jari da ya kamata tun shekaru da suka wuce.”
Sai dai ya ce gwamnatinsa na gyara abubuwa:
“Ina farin cikin sanar da ku cewa mun wuce tsanani. Wahalhalun jiya sun fara sauyawa zuwa sauki. Ina murna da juriya da goyon baya da fahimtar da kuka nuna. Zan ci gaba da aiki domin ku, kuma ina sane da amincewar da kuka ba ni.
“Tattalin arzikinmu na farfadowa da sauri. GDP na zango na biyu na 2025 ya karu da kaso 4.23 cikin 100, mafi sauri cikin shekaru hudu, ya zarce hasashen IMF na kaso 3.4 cikin 100. Hauhawar farashi ta sauka zuwa kaso 20.12 cikin 100 a watan Agusta 2025, mafi kankanta cikin shekaru uku,” in ji Tinubu.
Shugaban ya kuma ce gwamnatinsa na kokarin bunkasa noma da tabbatar da wadatar abinci don rage farashin kayan masarufi.
NasaroriTinubu ya lissafa wasu daga cikin nasarorin da gwamnatinsa ta samu cikin shekaru biyu da ya ce sun hada da karuwar kudaden shiga daga bangaren da ba na mai ba, inda aka samu sama da Naira tiriliyan 20 kafin karshen Agusta 2025, samun damar zuba jari a fannin tattalin arziki da shirye-shiryen tallafi bayan cire tallafin man fetur, karuwar kudaden ajiyar kasashen waje zuwa biliyan $42.03, mafi girma tun 2019
Ya kuma yi ikirarin cewa Najeriya na sayar da kaya fiye da yadda take saya daga kasashen waje, wanda ke karfafa kudin kasar da samar da ayyukan yi.
Tinubu ya kuma ce kayayyakin da aka kera a Najeriya da aka fitar sun karu da kaso 173 cikin 100, yayin da fitar da kayayyakin da ba na mai ba ya kai kaso 48 cikin 100, yayin da na mai ke da kaso 52 cikin 100.
Ya ce hakan na nuna cewa ana karkata tattalin arzikin kasar daga dogaro da mai zuwa bangarori daban-daban.
Matsalar tsaroDangane da tsaro, Tinubu ya ce gwamnatinsa na kokarin inganta tsaro don bunkasa tattalin arziki.
Ya ce: “Sojoji da sauran jami’an tsaro na aiki tukuru don kare kasar. Sun samu nasarori a yaki da ta’addanci, ’yan bindiga da sauran laifuka. Muna ganin nasarorinsu a cikin aikace.
“An samu dawowar zaman lafiya a daruruwan al’ummomin da aka ’yanta a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas, inda dubban mutane suka koma gidajensu lafiya,” in ji Shugaba Tinubu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Sakon yancin kai ya ce gwamnatinsa Ya ce gwamnatinsa ce gwamnatinsa na tattalin arziki cikin shekaru yan Najeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Yace Iran Ba za Ta Taba Mika Wuya Ga Duk Wata Barazana Ba
Rahotanni sun bayyana cewa jakadan iran a majalisar dinkin duniya Amir Saeid Iravani yayi gargadin cewa Tehran ba za ta taba mika wuya ga matsalin lmbar soji ba, ko ta siyasa ko kuma takunkumin tattalin Arziki, kuma ta yi tir da Amurka da Isra’ila game da harin da ta kai kan tashoshin nukiliyarta da ya sabama doka, da kuma yin fuska biyu a matakenta na kasa da kasa
Wannan bayani na Iravani yana zuwa ne adaidai lokacin da zaman tankiya ke kara Kamari bayan hari da Amurka da isra’ila suka kai a watan yuni shekara ta 2025 da muke ciki, wanda iran tace wurare ne dake karkashin kulawar hukumar nukiliya ta Duniya IAEA.
Kamalan nasa sun nuna cewa bisa mahangar iran tsarin sa ido na hukumar nukiliya ta duniya an siyasantar da shi yadda yanzu ba zai iya bada lamuni da tsaro ga kasashen dake memba a cikinta ba.
Hakazalika yayi tir da hukumar nukiliya ta duniya da daraktan ta da ya kasa yin tir da kai harin, duk da yake cewa hukumar tasha nanata cewa bai kamata akai hari kan tashoshin nukiliya ba,saboda hadarin da yake dashi ga lafiyar alumma, da kuma yanayi, yace yin shiru da tayi ya sanya a lamar tambya kan inganci da matsayin hukumar
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasashen Latin Amurka Sun Shirya Tsaf Don Mayar Da Martani Kan Wuce Gona Da Irin Amurka Kan Venuzuwela November 15, 2025 Rasha Tace Bata Da Shirin Kai wa Kungiyar Nato Hari Amma Za ta Mayar Da Martani Kan Duk Wata Barazana November 15, 2025 Shugaban Iran Da Prime Ministan Iraqi Sun Tattaunawa Kan Batun Zabe Da Kuma Alakar Dake Tsakaninsu. November 15, 2025 M D D Ta yi Tir Da Harin Da Yahudawa Yan Share Wuri Zauna Suka Kai A Masallaci A Yammacin kogin Jodan November 15, 2025 Mali ta Dakatar da Tashoshin Talabijin na Faransa TF1 da LCI November 15, 2025 Gaza: Amurka na matsin lamba ga kwamitin tsaro don amincewa da shirin Trump November 15, 2025 AU da MDD, sun karfafa dabarun tabbatar da zaman lafiya da tsaro November 15, 2025 Iran ta bukaci duniya ta gaggauta daukar mataki a Sudan November 15, 2025 EU ta nemi Isra’ila ta dauki mataki kan tashin hankali a Yammacin Kogin Jordan November 15, 2025 Amurka Ta Sanar Da Fara Kai Farmakin Soja Mai Sunan ” Mashin Kudu” Akan Yankin Latin November 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci