An haifi jariri da ‘fuska biyu’ a Bauchi
Published: 1st, October 2025 GMT
A wani lamari da ba kasafai ake samu ba, wata mata mai suna Hannatu ta haifi jariri mai fuska biyu da kai daya a babban asibitin gwamnatin jihar Bauchi da ke garin Azare.
Mahaifin jaririn, Malam Bala Sa’idu wanda yake a kauyen Magonshi, ya bayyana wa Aminiya cewa wannan haihuwar wata alama ce ta ikon Allah da ke tabbatar da cewa babu abin da Allah ba zai iya ba.
Ya ce duk da cewa lamarin ya bambanta da yadda aka saba, amma bai zo masa da mamaki ba.
Yunwa na kashe ’yan Najeriya, amma Tinubu ko a jikinsa – Atiku Mata masu zaman kansu za su fara biyan haraji a NijeriyaA cewarsa, goyon cikin da matarsa ta yi ya dauki tsawon makonni 42, wanda ya zarce al’ada.
Ya gode wa babban likitan asibitin, Dr. Bello Idris, wanda ya gudanar da tiyatar cire jaririn ba tare da an caje su ko kwabo ba.
Hannatu, mahaifiyar jaririn, ta ce wannan haihuwa ta sha bamban da sauran haihuwarta takwas da ta yi a gida ba tare da zuwa asibiti ba.
Ta ce wannan karon an yi mata tiyata, kuma tana godiya ga Allah da ya ba ta wannan baiwa.
Ta kara da cewa tana kaunar danta kuma tana rokon Allah ya ba ta lafiya domin ta raine shi kamar sauran ’ya’yanta.
Dr. Bello Idris, babban likitan da ya jagoranci aikin, ya ce a duk tsawon aikinsa bai taba fuskantar irin wannan halitta ba.
Ya ce akan samu irin wannan yanayi a cikin mutum daya daga cikin mutum miliyan goma.
Ya ce jaririn na da kai daya, fuska biyu, idanu hudu, hanci biyu, baki biyu, kunne biyu, hannaye biyu da kafa biyu. Sai dai ya zo da yankakken baki da ake kira “bakin noma,” wanda ke hana shi shan nono.
Likitan ya kara da cewa da zarar mahaifiyar jaririn ta samu sauki daga tiyatar da aka yi mata, za a tura su zuwa babban Asibitin Koyarwa na Gwamnatin Tarayya (FUHSTA) da ke Azare domin ci gaba da kulawa da kuma gudanar da bincike kan sauran sassan jikinsa.
A karshe, Malam Bala Sa’idu ya roki gwamnatin jihar Bauchi, kungiyoyin agaji da daidaikun mutane da su taimaka masa wajen ganin an samu lafiyar jaririn, duba da karancin halin da yake ciki.
Ya ce tuni aka ce za a tura su babban asibiti, amma yana cikin damuwa kan yadda za su fuskanci lamarin saboda rashin kudi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jariri
এছাড়াও পড়ুন:
Aref: Iran Tana Da Kyakkyawar Alaka Da Mambobin Kungiyar Hadin Gwiwa Ta Shanghai {SCO}
Mataimakin shugaban kasar Iran na farko ya bayyana cewa: Iran tana da kyakkyawar alaƙa ta musamman da kuma al’adu da membobin ƙungiyar haɗin gwiwa ta Shanghai
Mataimakin Shugaban Kasa na Farko na Iran ya ce, “Iran tana da alaƙar haɗin gwiwa na musamman da al’adu da dukkan ƙasashe membobin Ƙungiyar Haɗin Kan Shanghai (SCO), kuma abin farin ciki, ƙasar Iran ta shiga ƙungiyar SCO a hukumance cikin shekaru biyu da suka gabata.”
Da yake jawabi a Filin Jirgin Sama na Mehr-abad kafin ya tashi zuwa Rasha don halartar taron kolin kungiyar Shaanghai ta SCO, Mataimakin Shugaban Kasa na Farko Mohammad Reza Aref ya ce, “Ƙungiyar SCO ƙungiya ce mai tasowa amma mai ƙarfi da cikakken iko. Jimillar yawan al’ummar ƙasashe goma wadanda suke mambobi a kungiyar sun kai kimanin biliyan 3.4.”
Ya ƙara da cewa, “Iran tana da alaƙar haɗin gwiwa tsakanin na musamman da al’adu da dukkan ƙasashe membobin kungiyar, kuma abin farin ciki, Iran ta shiga ƙungiyar ta SCO a hukumance cikin shekaru biyu da suka gabata. Duk da cewa tsarin zama memba a kungiyar ya dauki lokaci mai tsayi sosai, kuma kafin shigar Iran cikin kungiyar tana da kyakkyawar haɗin gwiwa da wannan ƙungiyar.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Na’ini: Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Da Kansa Ya Jagoranci Yaki Kwanaki 12 Da Aka Kaddamar Kan Iran November 17, 2025 Mahukuntan Gaza Sun Yi Gargadin Bullar Bala’in Jin Kai A Yankin Da Ba A Taba Ganin Irinsa Ba November 17, 2025 Na’im Dassim: Gwamnatin Lebanon Zata Yi Babban Kuskure Matukar Tabi Hanyar Sassauci November 17, 2025 Rushewar Ramukan Hako Ma’adinai Ta Kashe Mutane 32 A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango November 17, 2025 Alummar Kasar Ecodo Sun yi Watsi Da Batun Sake Dawo Da Sansanin Sojin Amurka A Kasar November 17, 2025 Sojojin HKi Sun Kashe Wasu Falasdinawa Guda 2 A Sansanin Yan Gudun Hijira November 17, 2025 Tawagar Wasan Wushu Ta Kasar Iran Ta Samu Lambobin Yabo 4 A Saudiya November 17, 2025 Shugaban Nukiliyar Iran Yace Amurka Da Israila Sun Shiga Sabon Mataki Mai Hadari November 17, 2025 Hamas Da Sauran Bangarorin Falasdinawa Sun yi Watsi Da Shirin Aikewa Da Dakarun Kasashen Waje A Yankin Gaza November 17, 2025 Nukiliya : Iran zata sake duba huldarta da IAEA idan aka dauki wani sabon mataki kanta November 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci