DAGA LARABA: Tasirin Bambance-bambance Tsakanin ‘Yan Najeriya Shekara 65 Da Samun ‘Yancin Kai
Published: 1st, October 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Tun daga ranar 1 ga Oktoba, 1960, Najeriya ta samu ’yancin kai daga Turawan mulkin mallaka. Amma tun daga wannan lokaci, al’ummar Najeriya sun kasance cike da bambance-bambancen addini da kabila da harshe da al’adu da kuma ra’ayin siyasa. Wadannan bambance-bambancen sun kasance ginshiki guda biyu: a wani lokaci suna zama jigo wajen gina ƙasa mai cike da nishaɗi da ɗimbin albarkatu, wani lokaci kuma suna haifar da tangarda wajen tafiyar da ci gaban ƙasa.
Bayan shekaru 65 da samun ’yancin kai, ana iya cewa bambance-bambancen da ke tsakanin ’yan Najeriya sun taka muhimmiyar rawa wajen gina ƙasar, amma kuma sun bar gibi a fannin haɗin kai da kwanciyar hankali da samar da ci gaba.
NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa Mutane Suka Dawo Daga Rakiyar Kirifto? DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamatawannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai shekara 65 bayan samun ‘yancin kan Najeriya.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Sha Alwashin Bunkasa Goyon Bayan Juna Tsakaninta Da Saliyo
ShareTweetSendShare MASU ALAKA