Muhammad ElBaradei Ya Yi Kakkausar Suka Ga Shirin Trump Akan Gaza
Published: 1st, October 2025 GMT
Tsohon shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa,Muhammmad El-Baradei ya ce, Shirin na Trump akan Gaza ba komai ba ne sai kokarin tilasta larabawa su mika wuya, su kuma rusuna.
Muhammad El-Baradei ya wallafa a shafinsa na X cewa; na saurari taron manema labaru a fadar White House akan Gaza, amma na fada cikin damuwa mai tsanani akan halin da Gaza take ciki da kuma makomarta, haka nan kasashen larabawa baki daya.
Tsohon shugaban hukumar makamashin Nukiliyar ta kasa da kasa ya kuma ce; Wannan Shirin ba komai ba ne, sai na neman a mika wuya a kuma rusuna, ba shiri ne na neman zaman lafiya ba.”
Har ila yau, ya kuma yi suka akan yadda shugaban na kasar Amurka bai ambaci wahalhalun da Falasdinawa suke ciki ba a yayin jawabin da ya yi a MDD.
Shirin na Amurkan dai ya kunshi nada tsohon fira ministan Birtaniya Tony Blair a matsayin wanda zai jagoranci hukumar da za a kafa a Gaza. Haka nan kuma yin kira ga Hamas da ta mika makamanta na gwgawarmaya, sannan kuma ta saki dukkanin Fursunonin yakin da ke hannunta. Sai idan an yi hakan ne HKI za ta saki fursunonin Falasdinawa da suke zaman kurkuku na har abada, ta kuma fara janyewa sannu a hankali daga wuraren da ta mamaye a cikin Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Trump Ya Bayar Da Umarnin Aike Wa Da Jiragen Ruwa Na Nukiliya Zuwa Kusa Da Rasha October 1, 2025 Gaza: ‘Yan Gwagwarmaya Suna Ci Gaba Da Kai Wa Sojojin Mamaya Hare-hare October 1, 2025 Sojojin Yemen Sun Kai Hari Akan Wani Jirgin Ruwa Da Ya Nufi HKI October 1, 2025 Pezeshkian: Iran Zata Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Kawo Zaman Lafiya A Duniya September 30, 2025 Mataimakin Shugaban Kasar Iran Ya Ce: Hari Kan Iran Gwajin Karfinta Ne A Fagen Kimiyya Da Fasaha September 30, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Ana Musayar Sakonni Tsakanin Kasar Iran Da Amurka September 30, 2025 Janar Safawi; Iran Ta Kashe Matukan Jirgin Saman Isra’ila 16 A Yakin Kwanaki 12 Da Aka Yi A Tsakaninsu September 30, 2025 Ambaliyar Ruwa Ya Yi Barna A Sassan Sudan Tare Da Kara Janyo Matsalolin Jin Kai A Kasar September 30, 2025 Hamas : Shirin da Trump ya gabatar yana “Kusa da Hangen Isra’ila” September 30, 2025 Isra’ila : Netanyahu na shan suka bayan ya nemi afuwar Qatar September 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan tsaron Iran na Ziyara a UAE don karfafa dangantakar tsaro tsakanin kasashen yankin
Ministan tsaron Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh ya kai ziyarar aiki a Hadaddiyar Daular Larabawa don inganta dangantakar soja da kuma huldar tsaro a yankin.
Nasirzadeh ya jagoranci wata babbar tawaga, wadda ta isa Dubai a ranar Litinin bisa gayyatar takwaransa na Hadaddiyar Daular Larabawa.
Ministan tsaron Iran yana shirin yin tattaunawa da jami’an Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma halartar taron Dubai Airshow na 2025, wanda aka shirya gudanarwa a tsakanin 17-21 ga Nuwamba.
Ziyarar ta zo ne a karkashin tsarin diflomasiyyar tsaron Iran kuma tana da nufin inganta huldar yanki da kuma gano damar yin hadin gwiwa a fannoni daban-daban.
A lokacin rangadin baje kolin, an shirya cewa ministan tsaron na Iran zai yi tarurruka da jami’an tsaro daga kasashe da dama.
Bikin Dubai Airshow na 2025 zai karbi bakuncin masu baje kolin sama da 1,500, wadanda suka hada da sabbin masu baje kolin sama 440, masu Ziyara da ‘yan kasuwa 148,000, da kuma wakilai 490 na sojoji da fararen hula daga kasashe 115.
Za a nuna sama da jiragen sama 200, ciki har da jiragen sama na kasuwanci, na soja, na liken asirri, jiragen sama marasa matuki, da kuma fasahar zamani, wanda shi ne baje koli irinsa mafi girma a tarihi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Masu shigar da kara na ICC sun bukaci hukuncin daurin rai da rai a kan kwamandan RSF November 18, 2025 MDD ta amince da kudurin tura dakarun kasa da kasa zuwa Gaza November 18, 2025 Congo ta tsawaita haramcin fataucin ma’adinai a gabashin kasar November 18, 2025 Rasha: An dakile wani yunkurin kisan gilla kan Sakataren Majalisar Tsaron kasa November 18, 2025 Aref: Iran Tana Da Kyakkyawar Alaka Da Mambobin Kungiyar Hadin Gwiwa Ta Shanghai {SCO} November 17, 2025 Na’ini: Jagora Ne Da Kansa Ya Jagoranci Lamurra A Lokacin Yakin Kwanaki 12 Da Aka Kaddamar Kan Iran November 17, 2025 Mahukuntan Gaza Sun Yi Gargadin Bullar Bala’in Jin Kai A Yankin Da Ba A Taba Ganin Irinsa Ba November 17, 2025 Sheikh Na’im: Gwamnatin Lebanon Zata Yi Babban Kuskure Matukar Tabi Hanyar Sassauci November 17, 2025 Rushewar Ramukan Hako Ma’adinai Ta Kashe Mutane 32 A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango November 17, 2025 Alummar Kasar Ecodo Sun yi Watsi Da Batun Sake Dawo Da Sansanin Sojin Amurka A Kasar November 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci