2025-12-07@19:13:51 GMT
إجمالي نتائج البحث: 572
«Ibrahim Rabi u»:
Ofishin watsa labaru na hukuma a Gaza ya yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da kuma kungiyoyin jin kai, da su yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansu na doka da kyawawan halaye, su tsoma baki domin ceto da fararen hula a Gaza. Ofishin watsa labarun na hukuma a Gaza ya kuma...
Birgadiya Janar Rasul Sanaei-Rad wanda shi ne babban kwamandan sojan kasa na Iran ya bayyana hakan ne a wurin tunawa da zagayowar ranar ‘yanto da garin Khurramshahr daga mamaya sojojin Ba’asiyya na Sadam, a lokacin kallafaffen yaki. Birgediya janar Sanaei -Rad ya kuma yi ishara da ‘yanto da garin na Khurramshar yana mai kara da...
Kamfanin dillancin labarun Sputnik na Rasha ya sanar da cewa; sojojin kasar sun harba makamai masu linzami samfurin Iskander akan manyan akwatunan dakon kaya 100 dake dauke da makamai a tashar jiragen ruwa ta Odessa. Sanarwar ta kuma kunshi cewa makaman da sojojin na Rasha su ka tarwatsa sun hada kananan jiragen ruwa na yaki...
UNICEF ta gabatar da asusun abinci na yara don karfafa zuba jari a cikin manufofi da shirye-shirye. UNICEF ta jajirce wajen yin hadin gwiwa da gwamnatin Jihar Kwara don yaki da rashin abinci mai gina jiki, musamman a lokacin kwana 1000 na farko na rayuwar yara. “Kalubalen shi ne, yawan yara fiye da kashi 40...
Ofishin yada labaran Gaza ya bayar da rahoton mutuwar Falastinawa 299 da suka fada cikin mawuyacin hali na rashin abinci mai gina jiki, da karancin kayan masarufi da magunguna. Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga tashar talabijin ta Aljazeera na cewa, taimakon jin kai na cikin hadarin rubewa saboda haramcin da gwamnatin sahyoniyawan ta...
“Fanin na kuma taimaka wa wajen samar da ayyukan yi da samar da abinci mai gina jikin Dan’adam da kuma bunkasa hada-hadar kasuwanci, musamman duba da wayar da kai da ake yi na samar da abinci mai gina jiki,“ in ji shi. Shi ma, a nasa jawabin a wajen taron, Daraktan Cibiyar Bunkasa Samar da...
Daraktan Cibiyar Nazarin Al’adu da Ƙirƙirar Ƙirƙira, Jami’ar Ilorin, Farfesa Olutoyin Ogunade, ya ba da shawarar a bayyana kowace Litinin a matsayin Ranar Al’adu a harabar jami’ar. Farfesa Ogunade ya bayyana hakan ne a lokacin babban bikin ranar al’adu na jami’ar, mai taken “fayyace kyawawan Al’adun mu” a Ilorin. Ya ce wannan shiri...
Ministan Harkokin wajen kasar Omman ya bada sanarwan cew za’a gudanar da tattaunawa zagaye na 5 tsakanin Iran da Amurka kan shirin Iran na makamshin nukliya a ranar 23 gawatan Mayun da muke ciki a birnin Roma nakasar Italiay. Tashar talabijin ta Presstv a nnan Tehran ta ce Har yanzun ba’a ji tabakin kasashen biyu...
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce iran ba ta bukatar izinin kowa kan inganta sinadarin urenium din ta, don haka Amurka ta daina maganar banza da dagewa akan wannan batu inji shi. Ayatullah Khamenei ya kara da cewa, babban kuskure ne a ce su (Amurka) ba za su...
Ya misalta rashin basaraken da cewa, ba rashin ne kawai ga iyalai ko al’ummar masarautarsa ba, a’a rashi ne ga illahirin masarautar Bauchi da ma jihar Bauchi baki ɗaya. Gwamna Muhammad ya misalta Alhaji Garba a matsayin babban basaraken gargajiya wanda aka sani da hikima, tawali’u, da sadaukar da kai ga hidimta wa al’ummarsa....
Akalla Falasdinawa 38 ne suka rasa rayukansu a wani jerin hare-haren jiragen yaƙin Isra’ila da aka kai a sassa daban-daban na Gaza cikin rabin sa’a da dare, in ji likitocin Falasɗinawa. Rahotanni daga hukumar agajin gaggawa da ke ƙarkashin Hamas sun ce jiragen yaƙin Isra’ila sun kai hari a wurare da dama, ciki har da...
Masu sharhi na ganin cewa ko da Rasha na nuna amincewar sulhu, dole ne a fuskanci ƙalubale da dama kafin a kai ga cikakkiyar yarjejeniya, musamman dangane da yankunan da Rasha ta mamaye. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yayi tattaunawa ta wayar tarho mai aramashi da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, inda suka tattauna kan batutuwa da dama ciki har da yunkurin fara tattaunawar tsagaita bude wuta nan da nan tsakanin Rasha da Ukraine. Kamfanin dillancin labaran Rasha na RIA shi ma ya ambato, shugaban Kremlin...
Kungiyar Hizbullah Ta ce Marigayi Shahid Ra’isi Ya Kasance Mai Taimakawa Kasar Lebanon Da Kuma Falasdinawa Ne
Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Na’im Kasim a wani jawabinda da ya gabatar don tunawa da cika shekara guda da shahadar shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi da abokan tafiyarsa, ya bayyana cewa shugaban ya kasance mai kaunar falasdinawa ne har cikin zuciyarsa. Sheikh Qasim ya kara da cewa, shugaba Ra’isi ya rike...
Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya aika ta’aziyya ga iyalan mutane 37 da hatsarin kwale-kwalen Gbajibo ya rutsa da su daga jihar Neja a karshen mako. A cikin sanarwar gwamna AbdulRazaq ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Neja kan wannan lamari mai ban tausayi. Gwamnan ya bukaci ma’aikatan jirgin da fasinjoji da su...
Fira ministan gwamnatin rikon kwaryar Libiya ya bayyana cewa: Babu wata cibiyar tsaro a Libya sai dai cibiyoyi na yau da kullum da suka hada da sojoji da ‘yan sanda Abdul Hamid Dbeibah, shugaban gwamnatin rikon kwaryar gwamnatin hadin kan kasa, ya ce: “Babu wani wuri a kasar Libya, sai dai cibiyoyi na yau da...
A kokarin da yake yi na jigilar maniyyatan aikin hajjin bana, Kamfanin jiragen sama na Max Air yace zai kwashe daukacin Alhazan Jihar Jigawa cikin kwanaki biyu. Mataimakin mai kula da ofishin kamfanin dake jihar kano, Mr Barnabas Anderson ya bayyana haka a lokacin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a shelkwatar...
Dubban falasdinawa ma zauna Amurka ne suka fito gagarumar zanga-zanga don tunawa da zagayowar Ranar musiba a jiya Al-Hamis a birnin NewYork. Inda suka bukaci a kawo karshen kisan kiyashi a Gaza da gaggawa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan shi ne musiba na shekaru 77 da suka gabata. Wato...
Majiyar kiwon lafiya a zirin Gaza ta bayyana cewa daga safiyar jiya Alhamis zuwa karfe 12 dare HKI ta kashe falasdinawa 143 tare da amfani da jiragen saman yaki tankunan yaki ta kasa da kuma jiragen ruwa yaki. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa bayan tsakiyar dare ma sojojin yahudawan sun...
Jakadan JMI a MDD ya bayyana cewa ranar Nakba ko musiba ga Falasdinawa, abin bakinciki ba karshen musubar ba ce sai faraway ne, don a yau shekaru 77 da suka gabata kenen da musibar da ta faru da Falasdinawa tana ci gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Amir Sa’id Iravani yaana...
Rasha da Ukraine sun tabbatar da aikewa da tawaga dukkansu domin gudanar da tattaunawa ta kai tsaye tsakanin kasashen dake rikici da juna. Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya aike da tawagar Ukraine zuwa birnin Istanbul na kasar Turkiyya domin ganawa da wakilan Rasha domin tattaunawa kan zaman lafiya, amma shi da kansa ba zai...
Majalisar dattawa a ranar Talata ta yi kira ga rundunar sojin Nijeriya da ta gaggauta tura jami’anta da sabbin kayan yaki na zamani zuwa jihohin Borno da Yobe sakamakon sabon hare-haren da mayakan Boko Haram suka kai a yankin. An yi wannan kiran ne biyo bayan sabbin hare-haren ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas, ciki...
Sabbin alkaluma da cibiyar sanya ido kan yadda ake raba mutane da muhallansu da kuma hukumar kula da yan gudun hijira ta Norweian Refugee Council suka fitar sun bayyana cewa yanzu haka akwai sama da mutum miliyan 80 da aka raba da muhallansu a fadin duniya, kuma wannan ne mafi yawa da aka taba samu...
Gwamna Zamfara Ya Raba Katin ATM Ga Mutane 400,000 Da Suka Ci Gajiyar Shirin ‘Cash Transfer’ A Jihar
A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya sake jaddada cewa bikin ya nuna wani muhimmin mataki a ƙoƙarinsa na ƙarfafa wa al’ummar Zamfara masu ƙaramin ƙarfi. “Saboda haka, cikin farin ciki na tsaya a gabanku domin ƙaddamar da wannan muhimmin shiri. “Ya ku jama’a, da baƙi, an tsara wannan shiri ne domin bayar da...
Mahaifin tsohon Gwamnan Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero ya riga mu gidan gaskiya kamar yadda Masarautar Zazzau ta tabbatar. Alhaji Ramalan Yero, wanda ɗaya ne daga cikin dattawa kuma mai riƙe rawanin Turakin Dawakin Zazzau ya rasu ne da yammacin wannan Litinin ɗin bayan fama da doguwar jinya. Marigayi Alhaji Ramalan Yero mahaifi ne ga tsohon...
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Iran ba zata taba yin watsi da haƙƙinta na makamashin nukuliya na zaman lafiya ba a kowane yanayi Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Iran da gaske take yi wajen gudanar da tattaunawa domin neman cimma matsaya da zata gamsar da kowane bangare, amma neman yin watsi...
Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da sabbin Kwamishinonin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) kafin fara taron Majalisar Zartaswa ta Tarayya a fadar gwamnati da ke Abuja. Sabbin Kwamishinonin INEC din da aka rantsar su ne Mallam Tukur Yusuf, mai wakiltar yankin Arewa maso Yamma, da Farfesa Sunday Aja, mai wakiltar Jihar...
Shugaba da mataimakinsa an tsige su ne kan zargin almundahana, rashin ɗa’a, rashin mayar da hankali kan aiki da kuma cin zarafin ofisoshinsu. Kafin masa wannan naɗin riƙon kwarya, Wali ya kasance Kansila da ke wakiltar gundumar Tumfafi kuma shi ne ya kasance shugaban Kansiloli na ƙaramar hukumar. Gwamnatin jihar Bauchi ce ta...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bukaci shugaban kasar Ukraine ya amince da tayin shugaban Putin na Rasah na sun hadu a birnin Istambul na kasar Turkiya don tattauna yiyuwar tsagaita budewa juna wuta. Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya nakalto shugaban Trump yana fadar haka a jiya Asabar ya kuma bayyana cewa...
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ba da shawarar yin tattaunawa “kai tsaye” ba tare da sharadi ba” tsakanin kasarsa da Ukraine a ranar 15 ga Mayu a Istanbul. A martanin da ya mayar, shugaban na Ukraine ya ce a shirye ya ke don tattaunawa kai tsaye, amma ya zama dole a tsagaita bude wuta...
Tsohon jami’in harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Josep Borrell ya yi kakkausar suka ga kungiyar kan rashin daukar mataki game da kisan kiyashin da gwamnatin Isra’ila ke yi a zirin Gaza yana mai cewa “rabin bama-baman da aka jefa a zirin Gaza ne muke kawowa.” Da yake jawabi bayan karbar lambar yabo ta Carlos V...
Jakadan JMI a MDD ya musanta zargin kamfanin dillancin labaran reuters dangane da rotohonsa na cewa JMI tana aika makamai masu linzami zuwa kasar Rasah don taimakawa kasar Rasha yakin da take fafatwa da kasar Ukraine fiye da shekaru 3 da suka gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ofishin jakadancin JMI...
Aragchi: Muna Bukatar Rage Zaman Daradar Da Kuma Tabbatar Da Zaman Lafiya A Tsakanin Pakisatan Da Indiya
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa akwai bukatar kasashen Indiya da Pakisatan su daure su daina musayar wuta a tsakaninsu saboda tabbatar da zaman lafiya a yankin Asiya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a safiyar yau Alhamis bayan isarsa birnin News Delhi. A...
Bisa kididdigar da kamfanin layin dogo na kasar Sin ya fitar, daga fara zirga-zirgar hutun ranar ma’aikata a ranar 29 ga Afrilu zuwa ranar 4 ga Mayu, jiragen kasa na kasar Sin sun yi jigilar fasinjoji miliyan 112, adadin da ya karu da kashi 10.5 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara,...
Jami’ar siyasar waje ta tarayyar turai Kaja Kallas ta bayyana cikakken goyon baya ga warware batun makamashin Nukiliyar Iran ta hanyar diplomasiyya. Jami’ar ta wallafa a shafinta na X cewa: Na tattauna da ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci domin tabbatar da goyon bayan kungiyar tarayyar turai akan aiki da hanyar diplomasiyya domin warware batun...
Assalamu alaikum masu sauraro, sharhin bayan labarammu zai yi magana ne a kan Aya. Shahid Mttahari, shahidi na farko daga cikin malamai jagororin juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran a shekara 1979. A jiya Jumma ce 2 ga watan Mayu na wannan shekara ta 2025 aka yi juyayin shahadar malami na fadrko wanda...
Bishop Joseph Osifuwa, Bishop na jihar Kwara, ya ce Nijeriya za ta iya magance matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a sassan kasar nan idan har ta dauki matakin magance masu tada kayar baya. Bishop Osifuwa ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen babban taron cocin karo...
Layukan Dogo Na Kasar Sin Sun Gudanar Da Sufurin Miliyoyin Fasinjoji A Ranar Farko Ta Hutun ‘Yan Kwadago
Layukan dogo na kasar Sin sun gudanar da sufurin kusan fasinjoji miliyan 23.12 a jiya Alhamis, ranar farko ta bikin ranar ‘yan kwadago ta duniya da aka saba yi duk shekara a watan Mayu, kamar yadda kamfanin sufurin layin dogo na kasar Sin ya bayyana. A cewar alkaluman da kamfanin ya fitar a yau...
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen gina jihar da ma’aikata za su bunkasa, samar da ayyukan yi masu nagarta, da baiwa kowane bangare damar bayar da gudunmawa mai ma’ana ga ci gaban jihar. Gwamna AbdulRazaq a cikin sakonsa na bikin ranar ma’aikata ta duniya na shekarar 2025, a Ilorin,...
Ranar Maleriya Ta Duniya: ‘Yan Nijeriya Na Kashe Naira Tiriliyan 1.156 Duk Shekara Wajen Sayen Magunguna
Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa, duba mara lafiya guda daya tak da ke dauke da cutar Maleriyar da ba ta yi karfi sosai ba a asibitin gwamnati, na lashe kimanin Naira 17,000, tsakanin ganin likita, yin gwaje-gwaje da kuma magunguna. Wadannan kudade sun kai kimanin Naira tiriliyan 1.156 da ake kashewa a kan wannan...
Masifar Gobara Tana Kara Bunkasa A Haramtacciyar Kasar Isra’ila Tare Da Fara Raba Yahudawa Da Muhallinsu
Ana sa alamar tambayar cewa: Shin gobarar da ta tashi a birnin Kudus… shin sako ne na ranar tunawa da kafuwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya? Gobarar da ta tashi a tsaunin Kudus da aka mamaye ta bazu zuwa manyan yankuna a cikin haramtacciyar kasar Isra’ila, inda ta kewaye wani sansanin soji tare da cinye filayen masu...
Gwamnatin Amurka da kuma kasar Ukraine daga karshe sun rattaba hannu kan yarjeniyar hakar ma’adinai masu karanci na kasar Ukraine, don bawa kasar damar biyan basussukan da Amurka ta ke binta sanadiyyar yakin da take fafatawa da kasar Rasha fiye da shekaru 3 da suka gabata. Jaridar ‘The Nation” ta kasar Amurka ta kara dacewa...
Gwamnatin Nijeriya ta ayyana gobe Alhamis 1 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu ga ma’aikatan ƙasar albarkacin bikin murnar Ranar Ma’aikata ta Duniya. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Ministan Harkokin Cikin Gida na ƙasar, Olubunmi Tunji-Ojo, ya fitar a yammacin wannan Larabar. AU ta janye takunkumin da ta ƙaƙaba wa Gabon Tsoffin...
Kakakin ma’aikatar sharia a nan JMI ya bada sanarwan cewa,ma’aikatar za ta bayyanawa mutanen sakamakon bincken da suka gudanar kuma suke ci gaba da yi, dangane da fashewa da kuma gobatar da ta tashi a tashar jiragen ruwa ta Shahid Rajaee a cikin yan kwanakin da suka gabata. . Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar...
Kakakin kwamitin tsaron kasa a majalisar shawarar musulunci ta Iran ya bayyana cewa; ” Ya zuwa yanzu ba za mu iya yin hukunci akan dalilan da su ka haddasa fashewar abubuwa a tashar ruwa ta Shahid Raja’i ba, amma za mu iya cewa babu hannu waje a ciki. Kakakin kwamitin tsaron kasar ta Iran Ibrahim...
Shugaban Putin Na Rasha Ya Bada Sanarwan Tsagaita Wuta Da Ukraine Na Bangaren Guda kuma na sa’o’ii 72 ko kwanaki 3, daga 8-10 na watan Mayu mai zuwa. Jaridar Daily Trust ta Najeriya nakalto jakadan kasar Rasha a Abuja yana fadar haka a wani taro baje kolin hotinan yaki Rasah da Nazi a dai dai...
Fadar Kremlin ta kasar Rasha ta ayyana tsagaita wuta na kwana biyu ita kaɗai a yakinta da kasar Ukraine. Shugaba Vladimir Putin ya sanar a ranar Litinin cewa Rasha za ta aiwatar da tsagaita wutar ne daga tsakar dare na 8 ga Mayu zuwa tsakar dare na 10 ga Mayu. A ranakun da za a...
A cewarsa, tuni aka shirya wuraren kwana da abinci ga maniyyatan a kasar Saudiyya. Abdulkadir ya tabbatar da cewa, ana shirye-shirye, inda za a yi alluran rigakafi a ranar 28 ga Afrilu, za a raba tufafi a 30 ga Afrilu, sannan kuma za a raba jakunkuna a ranar 1 ga Mayu. Ya kara...
Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae, a karon farko da yayi magana dangane da fashewar tashar jiragen ruwa na Shahida Rajae ya gabatar da Ta’ziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu ko suka jikata a wannan hatsarin. Ya kuma bukaci a gudanar da bincike mai mai zurfi don gano musabbabin fashewar. Kamfanin...
Mataimakin ministan harkokin waje mai kula da bangaren siyasa, ya bayyana cewa; Ko kadan ba a bijiro da batun dakatar da tace sanadarin uranium a Iran ba, ko kuma batun makamanta masu linzami. Mataimakin ministan harkokin wajen na Iran ya tabbatar da cewa, wadannan abubuwan biyu wato dakatar da ci gaba da tace sanadarin uranium...