Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Bayyana Makasudin Rubuta Sakon Jagora Ga Shugaban Kasar Rasha
Published: 17th, April 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Sakon jagora ga shugaban kasar Rasha yana da alaka da ci gaban kasa da kasa da na yanki
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana hakan ne a yau Alhamis a birnin Moscow na kasar Rasha cewa: Abu ne da ya dace a rubuta sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya aikewa shugaban kasar Rasha dangane da ci gaban kasa da kasa da na yanki da kuma batutuwan da suka shafi kasashen biyu.
Araqchi ya bayyana hakan ne a lokacin da ya isa filin tashi da saukar jiragen sama na Vnukovo da ke birnin Moscow a yau, yayin da yake amsa tambayar da wakilin IRNA ya yi masa kan abubuwan da ke cikin sakon jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei zuwa ga shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya kara da cewa: Ziyarar tasa tana da manufofi daban-daban, yana mai bayanin cewa, tun da farko an shirya ziyarar ne domin isar da rubutaccen sako daga Jagoran juyin juya halin Musulunci ga shugaban kasar Rasha, kuma ta zo daidai da abubuwan da suka faru a baya-bayan nan da kuma tattaunawa ta kai tsaye.
Ya kara da cewa, tun a baya, har ya zuwa yanzu, a ko da yaushe Iran tana gudanar da shawarwari na kut-da-kut da abokanta na kasar Rasha kan batun makamashin nukiliya, yana mai cewa, suna kuma tattaunawa da Rasha da China, kuma a yanzu da aka samu damar da ta dace, za a iya yin shawarwari tare da jami’an Rasha.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: shugaban kasar Rasha
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Wajabcin Kawo Karshen Ayyukan Ta’addanci A Kasashen Yanki
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Dole ne a kawar da ta’addanci ta hanyar hadin kan kasashen yanki
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin ta’addancin da aka kai a birnin Pahalgam na kasar Indiya, tare da nuna alhini da juyayinsa ga gwamnati da al’ummar kasar Indiya, yana mai jaddada bukatar hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin domin yakar ta’addanci da kuma tsayawa tsayin daka kan wannan barazana ta bai daya.
Pezeshkian ya zanta ta wayar tarho a yammacin jiya Asabar da fira ministan kasar Indiya Narendra Modi, inda suka tattauna kan sabbin al’amuran da suke faruwa a yankin na Indiya, da kuma alakar da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasar Indiya.