Rasha Ta Sanar Da Kashe Manyan Kwamandojin Sojin Ukraine Fiye Da 60 A Birnin Sumy Na Kasar Ta Ukraine
Published: 15th, April 2025 GMT
Ma’aikatar tsaron Rasha ta sanar da yin luguden wuta kan zaman taron shugabannin sojojin Ukraine a birnin Sumy da ke arewa maso gabashin Ukraine
Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da cewa, ta kai hari kan wani ofishin rundunar sojojin Ukraine da ke dauke da makamai masu linzami na Iskander a yayin wani zaman taron manyan sojojin kasar a birnin Sumy, inda aka kashe jami’ai sama da 60.
Ma’aikatar tsaron Rasha ta kara da cewa sojojin na Ukraine na ci gaba da amfani da fararen hula a matsayin garkuwa gare su, tare da kafa cibiyoyin soji da kuma shirya tarurruka tare da halartar sojoji a tsakiyar birni mai yawan jama’a, tare da yin nuni da cewa; Rasha ta kai harin ne kan wani taron kwamandojin sojojin Ukraine.
Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya ce kasarsa na da shaidun da ke nuna cewa ana gudanar da taron shugabannin sojojin Ukraine da na yammacin Turai ne a wurin da aka kai hari a birnin Sumy.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: sojojin Ukraine
এছাড়াও পড়ুন:
An kashe Falasdinawa kusan 30 a wani sabon kisan kiyashin Isra’ila a Gaza
Bayanai daga Falasdinu na cewa akalla Falasdinawa 35 dane suka hada da kananan yara aka kashe a wanisabon kisan kiyashi na Isra’ila a zirin Gaza.
A cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza, wadannan hare-haren sun yi sanadin mutuwar mutane 35 tare da jikkata 109 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
Adadin wadanda sukayi shahada sakamakon yakin kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a yankin da aka yi wa kawanya ya zarce 52,400.
Adadin wadanda suka jikkata kuma ya kai kusan 118,014 tun daga watan Oktoban 2023.
Majalisar Dinkin Duniya dai ta yi gargadin barkewar ayyukan jin kai a Gaza.
Hukumar samar da abinci ta duniya (WFP) ta fitar da wani kakkausan gargadi game da matsalar jin kai da ke kara tabarbarewa a Gaza a dai dai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-haren bama-bamai da kuma killace fararen hula da ke fama da yunwa.
Tun cikin watan Maris ne Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya haramta kai kayan agaji zuwa Gaza, a wani mataki da ya ce na da nufin tursasa Hamas ta amince da tsawaita matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Isra’ila.