Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Gyara Kuskurenta Na “Kakaba Haraji Ramuwar Gayya”
Published: 3rd, April 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana yau Alhamis cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta gyara kuskuren da ta yi na kakaba “harajin ramuwar gayya,” kana ta magance sabanin dake tsakaninta da kasar Sin da sauran kasashen duniya dangane da tattalin arziki da cinikayya, ta hanyar yin shawarwari bisa daidaito, da mutunta juna ta yadda bangarorin za su ci moriyar juna.
Guo ya bayyana hakan ne a taron manema labarai na yau, a matsayin martani ga wata tambaya game da sanarwar da Washington ya yi na kakaba “harajin ramuwar gayya” kan manyan abokan cinikiayya. Yana mai cewa, a karkashin manufar “ramuwar gayya”, Amurka ta sanya karin harajin fito kan kayayyakin da ake fitarwa daga kasar Sin da sauran kasashe, wanda hakan ya sabawa ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya da matukar yin illa ga tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban, kana ya nanata cewa, babu wanda zai yi nasara a takaddamar cinikayya ko harajin fito, kuma kariyar cinikayya ba za ta samar da mafita ba.
A wani ci gaban kuma, kakakin ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin He Yadong ya bayyana a taron manema labaru na yau Alhamis cewa, kasar Sin a shirye take ta warware damuwar da ke tsakaninta da Amurka ta hanyar yin shawarwari bisa daidaito da tuntubar juna. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Jiragen Yakin Amurka Sun Kashe Mutane Da Dama A lardin Sa’ada Na Kasar Yemen
Mutane da dama daga nahiyar Afirka ne suke cikin mutane kimani 50 wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kai kan wani gidan kaso a lardin Sa’ada na kasar Yemen.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran Al-Masirah yana cewa makaman Amurka sun fada kan wani gidan yarin da aka kebewa yan Afrika, kuma yawansu ya kai 115, amma har yanzun ba’a san yawan wadanda suka rasa rayukansu a gidan yari.
Labarin ya kara da cewa har yanzun ma’aikatan agaji suna aikin ceto a wurin, sannan hotunan da suka fara bayyana sun nuna gawaki da dama. Amma Al-Masirah ta bayyana cewa akalla mutane 68 sun rasa rayukansu.