Araqchi ya mika rubutaccen sakon Jagora ga Shugaba Putin na Rasha
Published: 18th, April 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya mika rubutacciyar wasikar jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ga shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.
Araghchi, wanda ya je birnin Moscow a matsayin shugaban tawagar diflomasiyya don ganawa da wasu manyan jami’an Rasha, ya gana da Putin a yammacin ranar Alhamis.
Ministan ya gabatar da sakon Jagoran ga shugaban kasar Rasha tare da bayyana ra’ayoyi da matsayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da batutuwan da suka shafi ajandar huldar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma ci gaban yanki da sauran batutuwa na kasa da kasa.
Araghchi ya tabo yarjejjeniyar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare da shugaba Putin da takwaransa na Iran, Masoud Pezeshkian suka rattabawa hannu a birnin Moscow a watan Janairu.
Ya kira wannan yarjejeniya a matsayin “aiki mafi mahimmanci ta fuskar hadin gwiwa” tsakanin kasashen biyu, yana mai jaddada aniyar Iran na karfafawa da fadada huldar dake tsakaninta da tarayyar Rasha a dukkan matakai.
Shugaba Putin ya isar da gaisuwa da fatan alheri ga Jagoran juyin juya halin Musulunci tare da jaddada muhimmancin kara karafa kawance tsakanin Iran da Rasha bisa manyan tsare-tsare.
Ya kara da cewa, karfafa alaka a tsakanin kasashen biyu, tare da hadin gwiwa kan batutuwan da suka shafi gabas ta tsakiya da na kasa da kasa, zai yi amfani da moriyar kasashen biyu, da taimakawa wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Baya ga hakan kuma sun duba sauran batutuwa da suka shafi yakin Ukraine da kuma tattauna batun shawarwari kan nukiliyar Iran.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire
Cikin jadawalin GII na 2025, kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga 17, sun taka rawar gani fiye da yadda aka yi hasashe, bisa matsayin ci gabansu, yayin da kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara ke kan gaba, cikin kasashe mafiya samun ci gaban kirkire-kirkire, inda kasashen Afirka ta Kudu, da Senegal da Rwanda ke kan gaba a jerin kasashen shiyyar. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp