An Kashe Sojojin Yahudawa A Gaza A Yayinda Wasu Da Dam Suka Ji Rauni
Published: 15th, April 2025 GMT
Majiyar Falasdinawa a Gaza sun bada labarin kissan wasu sojojin HKI a unguwar Shuja’iyya kusa da Gaza a jiya Litini, inda wasu kuma suka ji rauni.
Kafafen yada labarai da yahudawan da kuma larabawa sun bayyana cewa kungiyar Jihadul Islami a Gaza ta ce nayakanta masu farautar yahudawa daga nesa sun bayyana cewa suk halaka wasu yahudawa wadanda suka boye a wani gida a garin Rafah kudancin Gaza, inda suke halakasu.
Sannan a sauran wuraren kuma sojojin yahudawan da dama ne suka ji rauni. Kuma sun ga jiragen yakin masu sauran ungulu na yahudawan sun zo sun tafi da wadanda abin ya shafa.
Wannan dai kadan Kenan daga hare-haren maida martanin da dakarun falasdinawan suke mayarwa ga sojojin yahudawan, tun lokacinda suka koma yaki kimani watanni biyu da suka gabata. Ya wan Falasdinawan da suka yi shahada tun bayan fara yakin Tufanul Aksa a ranra 7 ga watan Octoban shekara ta 20230 dai sun kai mutun 51,000 a yayinda wadanda suka ji rauni kuma suka kai fiye da 120,000. Mafi yawan wadanda abin ya shafa mata da yara ne.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Falasdinawa 40 Sun Yi Shahada A Cikin Sa’oi 24 A Gaza
A yau Laraba sa jijjifin Safiya an sami shahidai 3 a Gaza da hakan ya kara yawan shahidai zuwa 40 a cikin sa’o’i 24.
Bugu da kari, baya ga shahidan da suke faduwa a kowace rana, ana fama da matsananciyar yunwa a cikin yankin, bayan karewar kayan abincin HKI ta sake komawa yaki kwanaki 44 da su ka gabata.
A cikin sansanin ‘yan hijira na “Nusairat” mutane 3 sun yi shahada da su ka hada da karamar yarinya sanadiyyar harin da sojojin na HKI su ka kai wa yankin.
A gabashin birnin Khan-Yunus ma dai wasu Falasdinawa sun yi shahada.
Daga ranar 7 ga watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu adadin wadanda su ka yi shahada sun wuce 52,000,wadanda su ka jikkata kuma sun haura 100,000.