Gwamna Abdulrazaq Ya Bukaci Kiristoci Da Su Tuna Da Darussan Lokacin Ista
Published: 19th, April 2025 GMT
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bukaci Kiristoci da su yi tunani a kan darussa, muhimmaci, da kuma kyawawan dabi’u na makon Easter.
Gwamna AbdulRazaq a wani sako da ya aike a Ilorin, ya taya mabiya addinin kirista a jihar da ma fadin Najeriya murnar bikin Easter.
Gwamnan ya ce nasarar da Yesu Kiristi ya samu a fuskantar wahala, wanda bikin Ista ke alamta, ya kamata ya fitar da imani ga Allah da kuma yuwuwar da ba su da iyaka da ke zuwa tare da samun bangaskiya mara girgiza cikin ikonsa.
Ya yi addu’ar Allah ya sa lokacin Easter ya kawo farin ciki da jin daɗi mara iyaka ga kowane gida a jihar da kuma bayansa
REL/ALI MUHAMMAD RABIU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kwara
এছাড়াও পড়ুন:
Gidauniyar IRM Da KADCHMA, Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna
Da yake kaddamar da shirin, Darakta Janar na IRM, Alhaji Anas Muhammad, ya ce an kirkiro da shirin ne domin karfafa zaman lafiya da hadin kai ta hanyar tallafa wa Musulmai da Kiristoci ta bangaren samar da kiwon lafiya da bayar da tallafin kayan abinci da jari.
Ya ce: “Kalubalen lafiya ba sa bambance addini ko kabila, don haka bama bambantawa wajen bayar da tallafin. in sha Allah zamu ci gaba da aiwatar da irin wannan shiri a fadin jihar Kaduna baki daya.”
A nasa jawabin, Shugaban hukumar KADCHMA, Malam Abubakar Hassan, ya bayyana cewa wannan hadin gwiwa tana nuna muhimmancin dangantaka tsakanin gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu wajen cimma dorewar tsarin inshorar lafiya ga kowa.
Ya kara da cewa kaddamar da inshorar lafiya kyauta na shekara guda babban ci gaba ne a cikin gyaran fannin lafiya da ake gudanarwa a jihar, inda ya yaba da kokarin gidauniyar IRM wajen tallafawa rayuwar al’ummar Kaduna – Musulmai da Kiristoci.
Wasu daga cikin wadanda suka amfana da shirin daga Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) reshen Kaduna da kuma kungiyar ci gaba ta Darikar Tijjaniyya ta jihar Kaduna sun bayyana farin ciki da godiya ga gidauniyar da kuma gwamnatin jihar, inda suka ce inshorar lafiya kyauta za ta rage musu nauyin kashe kudin magani tare da karfafa hadin kai a tsakanin al’umma da samar da zaman lafiya.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA