Hukumar Alhazai Ta Jihar Neja Ta Fara Rabon Unifom da Jakunkunan Hannu Ga Maniyya
Published: 16th, April 2025 GMT
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Neja ta kaddamar da rabon sutura da jakunkunan hannu masu nauyin kilo 8 ga maniyyatan bana, a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen aikin Hajji na shekarar 2025.
A lokacin da yake jawabi yayin kaddamar da rabon, Shugaban Hukumar, Sheikh Muhammad Awwal Aliyu, ya bayyana cewa rabon kayayyakin na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da sauƙin tafiya da kuma aikin Hajji ba tare da wata tangarda ba ga maniyyatan jihar.
Shugaban wanda Daraktan Gudanarwa, Babani Aliyu Yahaya, ya wakilta a yayin bayar da kayan ga Jami’in Alhazai na Ƙaramar Hukumar Chanchaga, ya ce kayayyakin na maniyyatan da suka kammala biyan kuɗin kujerunsu ne.
Daraktan Gudanarwar ya kuma yi kira ga waɗanda har yanzu ba su kammala biyan kuɗinsu ba da su gaggauta, tare da buƙatar waɗanda ke da niyyar zuwa Hajji da su hanzarta biya domin gudanar da aikin cikin tsari.
A nasa jawabin bayan karɓar kayayyakin, shugaban karamar hukumar Chanchaga, Alhaji Abu Sufyanu ya yi alkawarin raba kayan yadda ya dace, tare da tabbatar da cewa za su gudanar da ayyukansu bisa nagarta da gaskiya.
Daga Aliyu Lawal
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
NSCDC Ta Kama Wadanda Ake Zargi Da Lalata Kadarorin Gwamnati A Kaduna
Hukumar Tsaro ta Najeriya (NSCDC) ta sake jaddada kudirinta na ci gaba da kare muhimman kadarorin gwamnati a kokarinta na cimma manufar kafa ta.
Kwamandan hukumar a Jihar Kaduna, Malam Panam Musa, ya bayyana haka yayin da yake gabatar da wasu mutane uku da ake zargi da lalata kayayyakin gwamnati a gaban manema labarai a hedikwatar hukumar da ke Kaduna.
Kwamanda Musa ya bayyana cewa jami’an hukumar sun cafke wadanda ake zargin ne yayin wani sintiri a kusa da hanyar NNPC da ke Kakau, Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.
Ya ce binciken farko ya nuna cewa wadanda ake zargin an kama su ne suna kokarin lalata igiyoyin wutar lantarki na musamman da ke da alaka da wata cibiyar sadarwa a yankin.
A cewarsa, kama su ya biyo bayan sabon umarni daga Babban Kwamandan NSCDC na kasa, Dakta Ahmed Abubakar Audi, wanda ya umurci dukkanin kwamandojin jihohi da su kara tsaurara tsaro da kuma fatattakar masu lalata kadarorin jama’a.
Kwamandan ya tabbatar da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike, tare da gargadin masu aikata irin wannan laifi da su daina, ko kuma su fuskanci hukunci mai tsanani.
Haka kuma ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba hukumar hadin kai ta hanyar samar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen dakile ayyukan ta’addanci da barnata kadarorin kasa.
Kwamandan ya kara da cewa hukumar za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaron muhimman wuraren gwamnati a fadin Jihar Kaduna da ma kasa baki daya.
Daga Usman Sani