Gwamnan Zamfara Ya Yi Jajen Rasuwar Dan Majalisa Aminu K/Daji
Published: 10th, April 2025 GMT
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya nuna kaɗuwar sa bisa rashin da aka yi na ɗan Majalisar Dokokin jihar, Hon. Aminu Ibrahim Kasuwar Daji, ɗan Majalisa mai wakiltar mazaɓar Ƙauran Namoda ta Kudu.
Iyalai sun bayyana cewa Hon. Aminu Kasuwar Daji ya rasu ne a cikin barcin sa da asubahin ranar Larabar nan a Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana cewa gwamnan ya miƙa ta’aziyyar sa ga Majalisar Dokokin jihar da Iyalan mamacin.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta aika da tawaga ta musamman, ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar, Mallam Mani Mummuni a yayin jana’izar ta marigayi Aminu K/Daji in Kauran Namoda.
“A madadin gwamnatin jiha,muna miƙa saƙon ta’aziyyar mu ga shugaban Majalisar Dokokin, sauran shugabanni a Majalisar, iyalai da al’ummar Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda ta Kudu.
“Muna kuma yin addu’a Allah ƙara ma iyalai jimirin jure wannan rashi. Muna kuma addu’ar Allah gafarta wa marigayin kurakuran sa.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma November 7, 2025
Manyan Labarai Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah November 7, 2025
Manyan Labarai Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump November 7, 2025