Majalisar Kasa Ta Rasha Ta Amince Da Yarjeniyar Dangantaka Ta Musamman Tsakanin Iran Da Kasar
Published: 17th, April 2025 GMT
Majalisar kasa ta kasar Rasha ta amince da yarjeniyar dangantaka ta musamman tsakanin kasar da JMI a ranar 8 ga watan Afrilun da muke ciki sannan ana saran shugaban kasa Vladimir Putin zai sanyawa yarjeniyar hannu a nan gaba.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa yarjeniyar ta musamman mai kuma dogon zango na shekaru 20 zai bawa kasashen biyu damar tallafawa juna da kuma aiki tare da bangarori daban-daban wadanda suka hada da tsaro makamashi kimiyya da fasaha da sauransu.
Labarin ya kara da cewa idan yarjeniyar ya fara aiki kasashen biyu suna da damar kyautata dangantaka a tsakaninsu, wanda zai rage dogaro da suke yi da kasashen yamma a bangarori da dama.
Dangantakar Tehran da Mosco tana kara karfi ne a dai dai lokacinda al-amuran tsaro suke kara tabarbarewa a yanking abas ta tsakiya. Har’ila yau a dai dai lokacinda kasashen biyu suke fama da takunkuman tattalin arziki mafi muni daga kasashen yamma saboda yaki tsakanin Rasha da Ukraine da kuma shirin makamashin nukliya na kasar Iran da kuma siyasarta a kudancin Asiya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Faransa Ta Yi Allah Wadai Da Harin Ta’addancin Da Aka Kai Birnin Zahedan Na Kasar Iran
Gwamnatin kasar Faransa ta yi kakkausar suka tare da tofin Allah tsine kan harin ta’addancin da aka kai birnin Zahidan na kasar Iran
Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan harin ta’addancin birnin Zahidan na kasar Iran, tare da jaddada adawar kasarta kan duk wani harin ta’addanci da aka kai kan fararen hula.
Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta fitar da wata sanarwa inda ta ce, birnin Paris na matukar yin Allah wadai da harin ta’addanci da aka kai a birnin Zahidan na kasar Iran a ranar 26 ga watan Yuli, wanda ya yi sanadin mutuwar fararen hula da dama ciki har da uwa da kuma ‘yarta.
Sanarwar ta kara da cewa, “A yayin da take mika ta’aziyyarmu ga iyalan wadanda suka mutu, suna fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata a wannan harin ta’addanci.”
Wani abin lura a nan shi ne cewa, a safiyar ranar Asabar 26 ga watan Yuli ne wasu ‘yan ta’adda suka kai hari kan ginin hukumar shari’a ta cibiyar birnin Zahidan, fadar mulkin lardin Sistan da Baluchestan a kudu maso gabashin kasar Iran, inda suka kashe da kuma jikkata wasu Iraniyawa.