2025-06-15@11:55:55 GMT
إجمالي نتائج البحث: 18
«Ibrahim Ado Kurawa»:
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baghae ya zargin gwamnatin Amurka da yin ba daidai ba saboda karin takunkuman tattalin arziki wanda ta dorawa kasar, wanda kuma yake nuna irin kiyayyar da takewa mutanen kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Esmael Baghae yana fadar haka a jiya Asabar, ya kuma...
Gwamnatin kasar Amurka ta kara yawan takunkuman tattalin arzikin da take dorawa JMI dangane da shirinta na makamashin Nukliya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a wannan karon takunkuman sun shafi mutane 10 da kuma kamfanoni 27. Wadansu daga cikin kamfanonin suna kasar hadaddiyar daular Larabawa wasu kuma a Hong kong....
Dakarun gwagwarmayar kasar Yemen sun bayyana cewa: Za su mayar da jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila abin ba’a Shugaban majalisar koli ta siyasar kasar Yemen Mahdi al-Mashat, ya tabbatar da cewa: Tsaron sararin samaniyar sojojin kasar Yemen zai iya tunkarar jiragen saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila da suke kai hare-haren wuce gona da iri...
Gwamnatin kasar Amurka tana takurawa JMI ne don ta dakatar da shirinta na makamashin nukliya. Don haka ne Amurka take barazana ga Iran a kan cewa idan bata amince a cimma yarjeniya da ita a kan shirinta na makamashin Nukliya ba to ba abinda ya rage sai zabinb soje don wargwaz cibiyotyin makamashin nukliya na...

Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Sha Alwashin Mayar Da Martani Cikin Gaggawa Kan Duk Wani Hari Kan Kasarta
Jamhuriayar Musulunci ta Iran ta sha alwashin mayar da martani cikin gaggawa ga duk wani kasadan ‘yan Sahayoniyya da Amurka kan kasarta Jakada kuma zaunannen wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani ya jaddada cewa: Duk wani kasadan harin soji da Amurka ko wakilliyarta gwamnatin ‘yan sahayoniyya suke yi, ko...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin JMI ba zata amince da tattaunawa tare da kara tsuge takunkuman tattalin arziki na koli da aka dorawa kasar ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a yau Jumma’a ya kuma kara da cewa yin haka sabawa...
An fara kasuwar baje koli na kayakin kasuwancin da ake samarwa a cikin Iran ko IRAN EXPO 2025, karo na 3 a nan Tehran. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kasuwar baje koli na Iran EXPO 2025 zai jawa masu zuna jari daga kasashen Afirka. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas...
Shahararren masanin tarihin nan na Jihar Kano, Ibrahim Ado Kurawa, ya bayyana cewa soke hawan Sallah da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya yi tamkar wani wasan kwaikwayo ne. A makon jiya ne dai Sarki Aminu Ado ya sanar da janye hawan Sallar da ya ce zai jagoranta kan abin da ya kira...

A Jiya Laraba Ce Iran Take Bukukuwan Cika Shekaru 78 Da Kwatar Kamfanin Man Fetur Na Kasar Daga Hannun Turawan Burtaniya
A ranar 19 ga watan Maris na ko wace shekara ne mutanen Iran suke gudanar da bukukuwan tunawa da ranar da mutanen kasar tare da taimakon gwamnatin lokacin suka sami nasarar kwace kamfanin haka da sarrafa man fetur na kasar, daga hannun wani kamfanin mai na kasar Burtaniya suka maida shin a kasa. Kamfanin dillancin...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran a shirye take ta shiga tattaunawa da kasashen Turai bisa mutunta juna. A wata tattaunawa ta wayar tarho, Araghchi da Ministan Harkokin Wajen Netherlands Caspar Veldkamp sun tattauna hanyoyin inganta alakar juna da sabbin abubuwa dake faruwa a yankin da na kasa da kasa. Babban jami’in...
Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris ya tabbatar wa mutanen da hare-haren Lakurawa a ƙaramar hukumar Arewa ya raba da muhallansu cewa gwamnatinsa za ta ɗauki matakan gaggawa domin mayar da su garuruwansu. Nasir Idris ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai ziyarar jaje ga mutanen da hare-hare ya raba da garuruwansu a sananin...
Mataimakin ministan harkokin wajen a kan al-amuran siyasa, dole ne Amurka ta daukewa kasarsa wadannan takunkuman tattalin arziki wanda suke cutar da mutanen kasar Iran da al-adunsa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto TakhtaRawanchi yana fadar haka a shafinsa na X ko twitter a da, a kuma jiya Talata, Mataimakin ministan ya...
A yau Talata, kasar Sin ta bakin ma’aikatar kula da harkokin kasuwanci ta kasar ta bayyana rashin jin dadinta game da karin harajin da Amurka ta yi ikirarin sanyawa kayayyakin kasar, bisa kafa hujja da maganin Fentanyl. Kamar yadda kakakin ma’aikatar ya bayyana, Sin tana daya daga cikin kasashe mafiya tsauraran matakan yaki da miyagun...
Gwamnatin kasar masar ta tabbatarwa gwamnatin Falasdinawa kan cewa tana goyon bayan falasdinawa a cikin dawo da hakkinsu, na kafa kasarsu mai cikekken yanci wacce take da gabacin birnin Qudus a matsayin babban birnin Kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mostafa Madbouly ministan harkokin wajen kasar Masar yana fadar haka a...
Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya bayanna cewa, Turawa za su iya shiga cikin shirin warware rikicin Ukraine, yayin da kungiyar EU ke fargabar cewa za a mayar da ita saniyar ware tun bayan fara tattaunawar kai tsaye tsakanin Moscow da Washington. “Turawa, amma har da sauran kasashe, suna da hakki kuma suna da damar...
Jaridar Wall Satreet Journal ta ambaci cewa kasashen Faransa da Birtaniya suna shirya yiyuwar aikewa da sojojin tabbatar da zaman lafiya a cikin kasar Ukiraniya idan an tsagaita wutar yaki. Jaridar ta Amurka ta kuma kara da cewa; Idan an kai ga cimma tsagaita wutar yaki to da akwai yiyuwar turawan za su aike da...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa kasashen Turai basa cikin tattaunawar tsagaita wuta a Ukraine. Jaridar Daily Mail ya bayyana cewa hankalin shuwagabannin kasashen turai ya tashi a lokacin da JD Vance mataimakin shugaba Trump ya fada masu cewa ba wani shugaba daga cikin shuwagabannin kasashen Turai da zasu halarci taron tsagaita wuta...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi, a lokacin da yake maida martani ga jawabin shugaban kasar Amurka Donal Trump a jiya Laraba, ya ce takurawa mai tsanani ya karya. Abbas Aragchi ya fadi haka a jiya Laraba , ya kuma kara da cewa bayan takuarawa masu tsanani Amurka tana bukatar tattaunawa da Iran. Harma...