Ukraine na Fuskantar Wata Barazana, Dangane Da Bukatar Amurka Na Kwace Iko Da Cibiyar Gas Na Rasha A cikin Kasar
Published: 13th, April 2025 GMT
Labaran da suke fitowa daga kasar Ukraine sun bayyana cewa, gwamnatin kasar tana son karban iko da bututun iskar gas na kasar Rasha wanda yake yammacin kasar da Turai, wanda kuma yake kai iskar gasa zuwa kasashen Turai.
An gina bututun tun zamanin tarayyar Soviet kuma kasashen biyu suna samun kudade masu yawa daga wannan bututun.
Gwamnatin kasar Amurka dai tana son ta dawo da kudaden da ta kashewa kasar Ukraine na makamai wacce ta karba a likacin shugaban Biden. Daga cikin dai Amurka ta bukaci Ukraine ta bada ma’adinanta na kimani dalar Amurka biliyon $500.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa jami’an gwanatocin kasashen Amurka da Ukraine sun tattauna wannan batun a ranar jumma’an da ta gabata, don tattauna batun irin ma’adinan da kasar Ukraine zasu bawa Amurka saboda biyan kudaden da take binta basgi. Har’ila yau Amurkawan sun gabatar da shawarar kasashen biyu su hada giwa don samun riba tare a aikin hakar Ma’adinan.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
ICC ta ki amincewa da bukatar Isra’ila na soke sammacin kama Netanyahu
Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) ta yi watsi da bukatar Isra’ila na soke ko kuma ta dakatar da sammacin kama firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan harkokin sojin kasar Yoav Gallant.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, kotun ta ICC ta ce ta amince da daukaka karar da Isra’ila ta shigar na sake duba hurumin kotun kan laifukan da aka aikata a yankunan Falasdinu.
A watan Nuwamba 2024, kotun ICC ta bayar da sammacin kame Netanyahu da tsohon ministansa na harkokin soji, Yoav Gallant, bisa laifukan cin zarafin bil’adama da laifukan yaki da suka shafi kisan kare dangi da Isra’ila ke ci gaba da yi kan Falasdinawa a zirin Gaza.
Hukuncin ya tilastawa dukkan kasashe 125 da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar Rome da ta kafa kotun ta ICC, su cafke ko kuma su mika su ga kotun da ke Hague.
Firaministan Isra’ila ya je kasar Hungary, wadda mamba ce a kotun ICC, a farkon wannan watan.
Kotun ta ICC ta bukaci gwamnatin kasar Hungary da ta kama shi, amma Budapest ta yi biris da bukatar, kuma nan take ta sanar da cewa ta fice daga kotun.
ICC ta yi Allah wadai da kasar Hungary saboda kin kama Netanyahu.
Isra’ila ta kaddamar da yakin kisan kare dangi a Gaza a ranar 7 ga Oktoba, 2023, wanda ya kashe Falasdinawa akalla 51,355, galibi mata da kananan yara, tare da jikkata wasu 117,000, a cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza.