2025-07-08@11:14:05 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1918

«Karamar Hukumar Sanga»:

    Ministan tsaron cikin gida na HKI Itamar Ben-Gvir ya yi kira ga babban murya kan cewa dole ne HKI ta mamaye dukka zirin gaza ta kuma kori falasdinawa da suke cikinsa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalato Ben Gafir yana fadar haka a jiya ya kuma kara da cewa mamaye gaza da...
    Jaridun kasar Amurka sun bayyana cewa; Isra’ila ta kasa cimma manufofin da ta ayyana a yaki da Iran, sannan kuma ta kara zama saniyar ware a duniya. Mujallar “Foreign Policy” ta yi ishara da sakamakon yakin da take cewa, ya zamarwa Amurka da kawarta   Isra’ila juyewar reshe da mujiya,domin harin da su ka kai wa...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yau Laraba a taron manema labaru da aka gudanar cewa, kayayyakin Sin sun shiga kasuwar duniya, inda suka kara baiwa masu sayayya na kasa da kasa damar samun zabi. Jami’ar ta yi tsokacin ne bisa yadda batun wasu kayan shayi na kasar Sin ya...
    Tsangayar Kwalejin koyar da aikin Jinya ta Jihar Jigawa dake garin Birnin kudu ta gudanar da bikin kaddamar da sabbin dalibai 116 da za su yi karatun difloma ta kasa da babbar difloma ta kasa karon farko na shekarar karatu ta 2024 zuwa 2025. A jawabinsa wajen taron kaddamar  da daliban,  kwamishinan ma’aikatar lafiya na...
    Shugaban hukumar kula da makarantun kiwon lafiya da bada lasisi ga likitoci kula da lafiya a matakin farko ta kasa Alhaji Dr Bashir Idiris Lifidin Jama’a ya hori ma’aikatan kiwon lafiya a matakin farko da dukkannin masu ruwa da tsaki a bangaren lafiya su rubanya kokari fuskar tabbatar da kwarewa domin inganta ayyukan kula da...
    Iran ta nuna makamai masu linzami wadanda suka bude kofofin jahannama kan ‘yan sahayoniyya A martanin da gwamnatin yahudawan sahayoniyya suka kai wa Iran, sojojin Iran da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar sun nuna karfinsu na soji a matsayin wani bangare na “Alkawarin Gaskiya na 3”, inda suka harba daruruwan makamai masu...
    Jagoran sabuwar jam’iyyar ADC, Ralph Nwosu, ya bayyana cewa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, zai jagorance su wajen karɓar mulki daga hannun Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027. Jam’iyyar haɗakar, wacce ta ƙunshi fitattun ’yan siyasa, ta naɗa David Mark a matsayin Shugaba, tare da tsohon Gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola, a matsayin Sakatare....
    Shugaban Karamar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara, Alhaji Bello Mohammed Jabaka, ya yi kira ga al’ummar yankin da su dauki matakan kariya domin dakile yaduwar cutar kwalara da sauran cututtukan da ke yaduwa cikin sauri a yankin. Ya yi wannan kiran ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Gusau, babban birnin jihar, kan...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hare-haren HKI da Amurka a yankin yammacin Asiya ya kara rashin zamn lafiya a yankin. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadin haka ne a lokacinda yake zantawa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Girka a jiya talata ....
    Gwamnatin shugaban Donal Trump na Amurka ta bada sanarwan rage yawan wasu makaman da take aikawa kasar Ukraine. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran na nakalto majiyar Fadar Majiyar fadar white House na bayyana cewa pentagon ko ma’aikatar tsaron kasar ta bada rahoton cewa rumbun ajiyar makaman kasar yayi kasa sosai don haka akwai...
    Rundunar ’sanda ta jihar Delta ta ja kunnen matasan jihar a kan yin shigar banza, inda ta ce duk wanda aka kama za a iya cin shi tarar da ta kai ta naira 50,000. A cikin wata sanarwa da Kakakin rundunar a jihar, SP Bright Edafe ya fitar ranar Talata, ya ce yin shigar banzan...
    Wani rikicin gado a kan fili da ya ɓarke tsakanin wasu ahali biyu a ƙauyen Kopkopshe na gundumar Tunkus da ke Ƙaramar Hukumar Mikang ta Jihar Filato, ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya tare da ƙone gidaje da dama. Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, bayan aukuwar rashin jituwa tsakanin ɓangarorin biyu wanda sun...
    Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin zai gudanar da taron manema labarai a ranar Alhamis mai zuwa, da misalin karfe 10 na safe domin yin bayani kan shagulgulan al’adu da za a yi na bikin cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiyar jama’ar kasar Sin kan zaluncin Japanawa da kuma yakin duniya...
    Ya samu munanan raunuka a harin da aka kai masa, wanda daga baya ya mutu. Janar Kangye ya ƙara da cewa Danbokolo ya fi Bello Turji tsabibanci, shi ne ya jagoranci harin watan Disamban 2021 a ƙaramar hukumar Shinkafi ta Jihar Zamfara, inda ya ƙone fasinjoji da ransu a cikin mota. Hakazalika, ya bayyana cewa...
    Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya amince da kafa kwamitin mambobi 41 da nufin kafa sabbin masarautu a faɗin jihar. Wata sanarwa da kakakin gwamnan, Mukhtar Gidado, ya fitar ta bayyana cewa kwamitin ya ƙunshi fitattun mambobi 41 da aka zabo daga ɓangarori daban-daban, ciki har da sarakunan gargajiya, ƙwararru, malaman jami’a, wakilan ƙungiyoyin...
    Dukkaninsu sun je ne domin girmama marigayi Dantata tare da halartar jana’izarsa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Nijeriya ta karɓi bashin daga ƙasashen duniya da cibiyoyin kuɗi kamar Bankin Duniya, Bankin Raya Ƙasashen Afirka (AfDB), Exim Bank na ƙasar Sin, da kuma daga Japan da wasu ƙasashen. Ta kuma karɓi bashin kasuwanci kamar na Eurobond. Bashin cikin gida kuwa wanda gwamnati ke karɓa daga cikin ƙasar ya kai Naira tiriliyan 78.76, kwatankwacin...
    Tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi ya ce zai yi takarar shugabancin Nijeriya a 2027 domin ba zai shiga duk wata yarjejeniyar haɗakar takara da kowa ba. Obi wanda ya yi takarar shugabancin Nijeriya a Zaben 2023 a karkashin inuwar jam’iyyar Labour (LP), ya tabbatar wa magoya bayansa cewa babu gudu babu ja da baya dangane...
    Dalibai 29 ne suka rasa rayukansu sakamakon turmutsitsin a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya yayin tserewa fashewar taransifoma Akalla dalibai 29 ne suka mutu a birnin Bangui na kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a wani turmutsutsu sakamakon fashewar tiranfomar lantarki a lokacin jarrabawar sakandare, a cewar ma’aikatar lafiya ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Wata takarda daga...
    Gwamnatin Zamfara ta bayyana cewa jami’an sa-kai sun kashe wani riƙaƙƙen ɗan bindiga da ya addabi wasu yankunan jihar mai suna Kacalla Ɗanbokolo. Mai bai wa gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Ahmad Manga wanda ya tabbatar da hakan ya bayyana kisan Ɗanbokolo a matsayin gagarumin nasara a yaƙi da matsalar tsaro. “Ɗanbokolo mutum ne...
    Ya ce a tare da shi a cikin tawagar, akwai Ministan shari’a, Antoni-janar na tarayya, Yarima Lateef Fagbemi, SAN; Ministan yaɗa labarai, Alhaji Mohammed Idris, da ƙaramin Minista a ma’aikatar gidaje, Hon. Yusuf Abdullahi Ata. Tawagar ta kuma haɗa da wasu manyan Malamai, waɗanda suka ƙunshi, Dr Bashir Aliyu Umar, Sheikh Aminu Ibrahim...
    Muna sane da wuraren da ake yaki masu taba zuciya: Gaza, Sudan, Ukraine da sauran wurare. Rikicin baya-bayan nan tsakanin Iran da Isra’ila, wani abin tunatarwa ne ga raunin zaman lafiya musamman a yankin Gabas ta Tsakiya mai fama da tashe-tashen hankula.   Duk da haka, a cikin wannan tashin hankali, mun yi nasarar dakile...
    Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi Uwargida Oluremi Tinubu wacce ta ba da Naira miliyan 110 ga iyalan marigaya. An kuma yi alƙawarin cewa gwamnati za ta ɗauki nauyin ilimin yaran waɗanda suka rasu da kuma taimaka wa matansu da iyayensu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Fitaccen ɗan kasuwar nan, Alhaji Dahiru Bara’u Mangal, ya bayar da tallafin Naira miliyan 80 don taimaka wa mutane masu fama da cutar mafitsara da matsalar gwaiwa domin yi musu tiyata kyauta. An gudanar da tantance marasa lafiyar a Asibitin Ƙashi na Amadi Rimi kafin a fara aikin tiyatar a ranar Asabar da ta gabata....
    Fitaccen ɗan kasuwar nan, Alhaji Dahiru Bara’u Mangal, ya bayar da tallafin Naira miliyan 80 don taimaka wa mutane masu fama da cutar mafitsara da matsalar gwaiwa domin yi musu tiyata kyauta. An gudanar da tantance marasa lafiyar a Asibitin Ƙashi na Amadi Rimi kafin a fara aikin tiyatar a ranar Asabar da ta gabata....
    Hasarar da gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi a hare-haren da ta kai wa kasar Iran ya kai dala biliyan uku Kafar watsa labaran Bloomberg ta Amurka ta yi kiyasin cewa: Hasarar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi a yakin da ta yi da Iran ya kai kusan dala biliyan 3, saboda gyaran gine-gine da...
    Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Rwanda sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya bayan shafe shekaru 30 suna rikici Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Rwanda sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, shekaru talatin bayan rikicin da ya barke a shekara ta 1994 da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane daga bangarorin biyu. An rattaba hannu kan...
    Kakakin ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ya ce kasarsa na adawa da duk wata yarjejeniyar yafe haraji da Amurka za ta kulla da wata kasa, wadda ka iya illata moriyar Sin, tare da baiwa kasar da aka kulla yarjejeniyar damar samun yafiyar haraji daga Amurka. Kakakin wanda ya bayyana hakan a jiya Asabar, lokacin da...
    Tashin farashin man fetur a kasuwannin duniya ci-gaban mai hakar rijiya ne ga Nijeriya wadda ke kan gaba wajen fitar da mai ta yadda za ta samu makuddan kudin shiga sai dai gagarumar matsala ce ga ‘yan kasa wadanda za su fuskanci karin mai a cikin gida wanda zai zama silar karin kunci a dalilin...
    Masanan sun kuma bayyana cewa, kashi 25 cikin 100 na manya a Nijeriya na dauke da kwayar cutar Sikila. Ana bikin ranar Sikilar ne a kowace shekara, ranar 19 ga Yuni, domin wayar da kan jama’a game da cutar da kuma yadda ake sarrafa ta. Wasu iyayen da suka bayyana irin abubuwa na renon yara...
    “Abin da muke son cimma shi ne, a duk shekara mu tabbatar da ganin mun rubanya yawan madarar da ake samarwa kasar a kasar daga tan miliyan 700,000 zuwa tan miliyan 1.4 daga nan zuwa shekara biyar masu zuwa”, a cewar Ministan. “A Nijeriya akwai sama da Shanu miliyan 20.9, Tumaki sama da miliyan 60,...
    Masu bincike sun gano cewa sojojin HKI sun kashe Falasdinawa akalla 100,000 tun bayan fara yakin tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekara 2023. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kan cewa farfesa Michael Spagat da kuma Khalil Shikaki  Bafalasdine masanin masanin fasahar siyasa a Jami’ar London na kasar Burtania...
    Gwamnatin kasar Faransa ta nawa JMI barazana kan cewa idan bata amince da yarjeniyan da Amurka take so ba to za’a sake dawo da takunkuman MDD a kanta. Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Faransa Jean-Noel Barrot yana fadar haka, ya kuma kara da cewa idan Iran ta...
    Alhaji Ahmad Manga ya ce, “an ɗauki matakin ne da haɗin gwiwar gwamnatin jiha da gwamnatin tarayya”.   Jami’an CPG na Zamfara sun kuma samu goyon bayan dakarun Civilian JTF na jihar Borno, inda suka ƙaddamar da harin a-yi-ta-ta-ƙare na bazata ga maɓoyar ta Bello Turji.   Gwamnatin jihar Zamfara ta ce artabun na ranar...
    Jiya Jumma’a 27 ga watan Yuni ne, aka kaddamar da wani aikin hadin-gwiwar kafafen yada labaran kasar Sin da kasashen waje daban-daban, mai taken “Ziyara a jihar Xizang don tunkarar zamanantarwa” dake karkashin jagorancin cibiyar watsa labarai ta harsunan Asiya da Afirka ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, da...
    Iran ta yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa kuma a hukumance kan zaluncin ‘yan sahayoniyya da Amurka Mataimakin babban jami’in kula da harkokin kasa da kasa na ma’aikatar shari’a kuma sakataren hukumar kare hakkin bil’adama ta Iran ya yi la’akari da matakin wuce gona da iri na baya-bayan nan da yahudawan...
    Darakta Janar na hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA ya bayyana cewa: Ba zai iya tabbatar da cewa Iran na kera makamin nukiliya ba! A wata hira da tashar talabijin ta Faransa LCI, Darakta Janar na hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA Rafael Grossi ya bayyana cewa: Ba zai iya tabbatar da cewa...
    Wani mummunan hatsari ya afku a Masar inda ‘yan mata 18 suka mutu sakamakon fashewar wata motar dakon mai Wani mummunan hatsarin mota ya afku a kasar Masar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wasu mata 18 da direban bas a kan hanyarsu ta zuwa gonar inabin domin girbin inabin. Hatsarin ya afku ne a...
    Masana da jami’ai a Nijeriya, sun yaba wa ci gaba na a-zo-a-gani da karin kuzarin da ake samu a hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Nijeriya, suna masu bayyana kokarin da aka yi zuwa yanzu a hadin gwiwar bangarorin biyu a tafarkin zamanantar da kansu. Masanan sun bayyana haka ne yayin taro na biyu na...
    Ya ci gaba da cewa, Hukumar ta NPA, ta yi kasafin da dara haka, na wannan adadin, musaman ganin cewa, ta na burin, kara inganta ayyukanta, yadda za su yi dai-dai, da yadda ake gudanar da ayyukan, a sauran Tashoshin Jiragen Ruwa na duniya. Shugaban Hukumar ya kuma sanar da cewa, a shekarar 2024, Hukumar...
    Duk ana dora alhakin yadda lamarin cinikin Bayi ya bunkasa kan wani mutum dan asalin kasar Birtaniyya da ake kira da suna,John Hawkins. Hawkins  shi ne mutumin da ya kara daukaka, bunkasa,da zamanan har da lamarin cinikin Bayi”manufa anan yayi  gyare- gyare daga yadda Turawan kasar Fotugal suka fara da barinsa,ya yi masa kwaskwarima,zuwa lamarin...
    A safiyar yau ne aka gudanar da tattakin jana’izar shahidai kimani 60 a nan Tehran, wadanda suka hada da kwamandojin sojojin kasar da da masana fasahar Nukliya da sauran mutane maza da mata. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto cewa, an fara tattakin Jana’izar ne daga danganlin inkilabi ko juyin juya hali...
    An ji karar jiniyoyin gargadi a wurare da dama a HKI suna tashi bayan sun hango malamai masu linzami wadanda sojojin Yemen suka cilla daga kasar zuwa haramtacciyar kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kafafen yana labaran yahudawan na cewa sun yi shirin kakkabo makaman kafin su isa. Amma basu bada...
    Indomie , shahararriyar kampanin taliyar indomie a Najeriya, ta sanar da kaddamar da sabon gangamin ta mai taken Ingantaccen Abinci Domin Nasara. Wannan gangamin yana jaddada rawar da abinci mai gina jiki kamar Indomie ke takawa wajen ciyar da nasarar iyalai da Karin lafiyar su a Arewacin Najeriya. Shekaru da dama kenan da aka san...
    Tallan na talabijin ya bayar da labarin rayuwar Binta, ya kuma mayar da hankali akan irin tasirin da abinci mai kyau ya ke da shi wajen tallafawa iyali. Da labarin ya yi nisa, mun gano Binta tun daga ƙuruciya zuwa shigarta makarantar koyon aikin likitanci. Hakan ya nuna yadda abinci mai kyau da goyon bayan...
    Hukumar samar da bunkasa da hadin gwiwar kasa da kasa ta kasar Sin ta gabatar da taron manema labarai a yau Juma’a, inda aka yi karin haske game da yadda Sin take baiwa kasashen Afirka tallafi da samun bunkasa tare da su cikin hadin gwiwa. An ce, ya zuwa yanzu, Sin tana taimakawa kasashen Afirka...
    Aƙalla mutum ɗaya ne aka tabbatar da mutuwarsa tare da wasu biyar suna jinya bayan da wata babbar mota ƙirar tirela ta ƙwace ta kutsa cikin kasuwar Mile Six da ke Jalingo babban birnin Jihar Taraba. Shaidun gani da ido a wurin sun bayyana cewa, duk ƙoƙarin da direban motar ya yi na hana afkuwar...
    Wasu gungun ƙudan zuma sun kai hari tare da tarwatsa ɗaliban da ke rubuta jarrabawar Hukumar da ke shirya jarrabawar kammala sakandare ta ƙasa ta Najeriya (NECO) a makarantar sakandaren kimiyya ta Mairi da ke Maiduguri a Jihar Borno. Wannan hari na ba-zata da gungun ƙudan zumar suka kai ya tilastawa ɗalibai da malaman makarantar...
    “Yunwa da talauci ba wai abubuwa ne da suka shafi al’umma ba ne kawai, su ne ke haifar da rashin tsaro, laifuka, tashin hankali, da kuma wargajewar al’umma, wadannan al’amura suna haifar da mugun yanayi, talauci yana haifar da rashin tsaro da rashin tsaro, sannan kuma ya kara zurfafa talauci. “Wadannan yunkurin a bayyane suke...