2025-08-13@20:50:03 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2252
«Shugaban karamar hukuma»:
Gwamnatin Tarayya ta yanke shawarar dakatar da ƙirƙirar sabbin manyan makarantu har na tsawon shekaru bakwai masu zuwa a duk faɗin Nijeriya. Dakatarwar ta shafi ƙirƙirar sabbin jami’o’i, kwalejojin ilimi da kuma kwalejojin kimiyya da fasaha na tarayya kamar yadda Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta tabbatar. Tinubu zai tafi ziyarar ƙasashe 3 An naɗa...
Tinubu ya yi kira da a sake duba kudaden gudanar da aikin NNPC da ake cire kashi 30 cikin 100 wanda doka ta tanadar a karkashin dokar masana’antar mai. Shugaban ya bayyana godiya ga mambobin majalisar bisa jajircewarsu da aiki tukuru wajen aiwatar da gyare-gyare masu tsauri da wahala wadanda suka dabaibaye ci gaban...
Shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran wato (AEOI) Muhammad Eslami ya bayyana cewa babu jada bayana a shirin nukliyar kasar iran, duk tare da takurawar kasashen yamma. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Eslami yana fadar haka a wani taro nay an jarida a nan Tehran a jiya Talata. Ya kuma...
Alausa ya ce dakatarwar, wacce ta shafi dukkan nau’o’in manyan makarantun gwamnatin tarayya an yi hakan ne da nufin dakatar da maimaici da barnatar da dukiyar gwamnati, inda za a yi amfani da kudin domin inganta makarantun da ake da su. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...
Wasu daga cikin zarge-zargen da ake yi wa shugaban sun hada da kara farashin kudin takin gwamnati daga ₦20,000 zuwa ₦22,000 kan kowane buhu; hada rikici tsakanin shugabannin Siyasar yankin; raba kan Kansilolin karamar hukumar; tsunduma cikin harkokin siyasa masu raba kan jama’a ta hanyar bayar da dukiyar gwamnati ga abokan siyasarsa kawai; da dai...
Ƙungiyar Ci Gaban Masarautar Jama’a (JEDA), ta roƙi Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, da ya kammala manyan titunan Birnin Kafanchan, wanda aikin ya tsaya tun zamanin Nasir El-Rufai. Muƙaddashin shugaban ƙungiyar, Ahmad Usman Husain, ya ce waɗannan tituna na da muhimmanci wajen bunƙasa tattalin arziki da rayuwar yau da kullum a Kudancin Kaduna. Majalisar Kano...
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Rano, Alhaji Muhammad Naziru Ya’u, na tsawon watanni uku sakamakon zarge-zargen aikata ba daidai ba. An yanke wannan hukunci ne a zauren majalisa ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar, Alhaji Jibril Isma’il Falgore, bayan kwamitin majalisar kan ƙorafe-ƙorafe ya gabatar da rahoton bincikensa. Yayin gabatar da rahoton,...
Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta dakatar da Shugaban Ƙaramar Hukumar Rano, Muhammad Nazir Yau, na tsawon wata uku domin gudanar da bincike kan zargin yin amfani da kujerarsa ba bisa ƙa’ida ba. Kansilolinsa sun zarge shi da karkatar da kayayyaki da kuma almundahana wajen tafiyar da dukiyar jama’a. Kullum a Kamaru muke kwana, mu yini...
An yi kira ga kwararrun kafafen yada labarai da su tabbatar da madogararsu domin tabbatar da samar da kyakykyawan rahoton abubuwan da ke faruwa a cikin al’umma. Babban Limamin Masallacin Al-Waheed Central, Imam Mustapha Luqman ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake jawabi a wajen taron hadin gwiwa da kungiyar ‘yan jarida...
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatinsa na samar da kyakkyawar alaka da kafafen yada labarai. Gwamna Yusuf ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ), Kwamared Alhassan Yahaya, da ‘yan majalisar zartaswar NUJ na kasa (NEC) da suka je Kano domin...
Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (SSANU), Jami’ar Jihar Taraba Jalingo, ta bayar da wa’adin makonni biyu ga gwamna Agbu Kefas da shugabannin jami’ar da su gana da ita ko kuma ta shiga yajin aikin. A cikin sanarwar da aka fitar a karshen taron majalisar da aka gudanar a ranar 7 ga wata. Agusta 2025,...
Biyo bayan wani rahoto da ma’aikatar lafiya ta tarayya ta fitar na cewa sama da likitoci 16,000 ne suka bar Najeriya a cikin shekaru bakwai da suka gabata domin neman aiki a wasu kasashe, gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani sabon shiri na cike gurbin da likitocin suka haifar. Da yake zantawa da manema...
Majalisar Dokokin Jihar Zamfara karkashin jagorancin Bashar Aliyu Gummi, ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta hada kai da ayyukan tsaro a Jihar domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, kamar yadda babi na biyu na kundin tsarin mulki ya tanada. A zaman taron na ranar Talata, mambobin sun yi zargin cewa, ‘yan bindiga...
Sojojin Yemen sun sanar da cewa: Sun kai hari kan muhimman wurare hudu na haramtacciyar kasar Isra’ila da jirage marasa matuka guda shida Sojojin Yemen sun sanar a yammacin jiya Talata cewa: Sun kai farmakin soji ta hanyar amfani da jiragen sama marasa matuka ciki guda shida, inda suka kai hari kan wasu muhimman wurare...
An ce ya amsa cewa an aikata fashi da makami sau biyu da shi, kuma yanzu hakan ana shari’arsu a kotun jihar Gombe. An miƙa shi tare da kayan da aka gano ga Sashen Yaƙi da Tashin Hankali domin ƙara gudanar da bincike. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Nijeriya da Isra’ila sun sake jaddada aniyarsu ta karfafa haɗin gwiwar tsaro a fannoni daban-daban, kamar batun yaƙi da ta’addanci, musayar bayanan sirri, samar da kuɗin tsaro da kuma bayar da horo na musamman ga jami’an tsaron Nigeria. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwar haɗin gwiwa wadda Ƙaramar Ministar Harkokin Wajen Nijeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, da...
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga LEADERSHIP a ranar Talata, Kakakin Rundunar ’Yansandan Jihar Bauchi, CSP Ahmed Wakil, ya ce rundunar ‘yansandan ta samu kiran waya da misalin karfe 9:20 na safe daga CLO, inda ya ce Chukwuebuka mai lambar jiha BA/25A/2069 bai farka ba daga barcinsa, yayin da sauran ’yan uwansa Kiristocin ke...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta cafke wani matashi mai shekaru 18, Hassan Aminu Sadiq, bisa zargin aikata fashi da makami a lokuta daban-daban, bayan wani samame da aka kai unguwar unguwar Yelwa da ke garin Kwadon a Karamar Hukumar Yemaltu Deba. Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce an kama wanda...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta cafke wani basarake, Mohammed Tukur mai shekaru 55, a kauyen Sabon Gari da ke yankin Zambuk na Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe. Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya...
Hukumar Kwastam Najeriya ta kama kwantainoni 16 ɗauke da makamai da miyagun ƙwayoyi da magungunan da wa’adin aikinsu ya ƙare da wasu haramtattun kaya na kimanin Naira 10 a Tashar Jiragen Ruwa ta Apapa da ke Jihar Legas a ranar Litinin. Hukumar ta bayyana cewa ta kama mutane shida dangane da wannan haramtattun kaya da...
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar da za ta tsawaita dakatar da harajin da ya ƙaƙaba wa ƙasar China na tsawon kwanaki 90. Trump ya sanar da hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Truth Social, sa’o’i kaɗan kafin wa’adin farko...
Hukumomin Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Gwamnatin Tarayya sun ufe makarantar a sakamakon zanga-zangar da dalibai suka gudanar domin nuna fushinsu kan harin da ’yan fashi suka kai dakunan kwanansu. Daliban sun tayar da tarzoma ne da sanyin safiyar Talata bayan harin ’yan fashin ya ya yi sanadiyyar jikkatar wasu dalaibai da dama, suna mazu...

Ministan Harkokin Wajen Iraki Ya Bukaci Zaman Tattaunawa Tsakanin Kungiyar Larabawan Yankin Tekun Gulf Da Iraki Da Kuma Iran
Ministan harkokin wajen kasar Iraki ya ba da shawarar gudanar da taron kasashen Larabawan yankin tekun Pasha da Iraki da kuma Iran Ministan harkokin wajen kasar Iraki Fuad Hussein ya gabatar da shawarar gudanar da taron hadin gwiwa tsakanin kasashen Iraki, Iran, da kuma kasashen larabawan yankin Gulf, a tsarin na 6+2, a gefen taron...
Kasar Italiya ta janye jirgin ruwanta daga tekun Bahar Maliya bayan gazawarta a fage kwamawa da kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Kasashen Turai sun ci gaba da janye jiragen ruwa da jiragen yaki daga tekun Bahar Maliya, lamarin da ke tabbatar da hukuncin da kasashen nahiyar suka dauka na cewa ci gaba da zamansu a...
Rijistaran makarantar, Alhaji Kasimu Salihu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa an rufe makaranta kuma an umarci ɗalibai su bar harabar makarantar har sai an bayar da sanarwa ta gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
Majalisar dokokin jihar Kano ta karbi karin kudirin kasafin kudi na shekarar 2025 daga bangaren zartarwa na jihar domin tantancewa. Bukatar, wacce aka mika ta wata wasika daga bangaren zartarwa, ta nemi amincewar majalisar ta kara kasafin kudi naira biliyan 169,522,463,294.82 domin daukar muhimman ayyukan raya kasa a fadin jihar. Kakakin majalisar Alhaji...
Dakarun Operation FANSAN Yamma (OPFY) sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta’adda da dama a wani hari da suka kai ta sama da kasa a yankin Makakkari da ke dajin Gando a karamar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara. Wannan farmakin wanda ya gudana a ranar 10 ga watan Agustan shekarar 2025, ya biyo bayan wasu...
Yajin aikin sai baba-ta-gani da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC reshen jihar Taraba, da kungiyar Kwadago (TUC) reshen jihar Taraba suka kaddamar a ranar Litinin da ta gabata, ya gurgunta ayyukan gwamnati a ma’aikatu da hukumomin gwamnati a jihar. Matakin wanda ya fara da tsakar daren litinin, ya kasance tare da hadin gwiwar shugabannin...
Hukumar Kwastam Najeriya ta kama kwantainoni 16 ɗauke da makamai da miyagun ƙwayoyi da magungunan da wa’adin aikinsu ya ƙare da wasu haramtattun kaya na kimanin Naira 10 a Tashar Jiragen Ruwa ta Apapa da ke Jihar Legas a ranar Litinin. Hukumar ta bayyana cewa ta kama mutane shida dangane da wannan haramtattun kaya da...
Wani dattijo ya rasu a sakamakon hatsari da gobarar tankokin sakon iskar gas da ta auku a yankin Zariya da ke Jihar Kaduna. Aliyu Ramalan Babbale mai shekara sama da 70 ya rasu ne a lokacin da yake ƙokarin tsira da ransa a sakamakon hatsarin tankokin a safiyar ranar Litinin. Dattijon ya gamu da ajalinsa...
Sojoji sun samu nasarar kai wani gagarumin farmaki kan maboyar ’yan ta’addan da suka addabi manoma da mazauna wasu ƙauyuka a Jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Nijeriya. Bayanai sun ce dakarun sojin na sama da ta ƙasa, waɗanda ke ƙarƙashin rundunar Operation Fasan Yamma da ke sintiri a Arewa maso Yamma domin kawar...
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta shawarci maniyyata aikin Hajjin shekarar 2026 da su fara shirin biyan kudaden ajiya. Kiran ya biyo bayan taron da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta gudanar tare da hukumomin Alhazai na jihohi, inda aka bayar da shawarar ajiyar naira miliyan 8 da rabi ga...
Kakakin NAF ya ce harin, an kai ne tare da hadin gwiwar runduna ta kasa, wanda ya yi sanadin mutuwar wasu fitattun ‘yan bindiga rundunarsu da dama. Daraktan ya kuma jadadda cewa hadin kai tsakanin sassan sama da na kasa na Operation Fasan Yamma ya sa farmakin ya zama na musamman. Daga kanmu,...
Wasu da ake zargin ‘yan ta’addar ISWAP ne sun kashe shugaban kungiyar mafarauta a kauyen Garjang da ke karamar hukumar Damboa a jihar Borno. Majiyoyi, a cewar Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da ‘yan tada kayar baya, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na safiyar Lahadi. Kungiyoyin Kwadago Sun Tsunduma...
Wani mutum ya ba da kyautar motarsa da ita kadai gare shi ga wani mai jan baki (alaramma) saboda ƙwarewarsa a haddar Al-kur’ani. Malam Yusuf Ɗan-Birni, ya kyautar da motar ce a taron wa’azin wata-wata da Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Iƙamatis Sunna (JIBWIS) ta shirya a garin Kubwa da ke yankin Babban Birnin Tarayya....
Kungiyar Kwadago da ta ‘yan kasuwa ta Nijeriya (NLC da TUC) reshen jihar Taraba sun bayyana shirin fara yajin aiki tun daga karfe 12 na daren Litinin 11 ga watan Agusta, 2025. Wannan mataki ya biyo bayan sakamakon taron majalisar zartarwa ta jihar da kungiyoyin biyu suka yi a ranar Lahadi a Jalingo, babban birnin...
’Yan ta’adda sun kashe mutum 24 tare da sace wasu akalla 144 a cikin mako guda a sassan Jihar Zamfara. Kungiyar Al’ummar Zamfara mai suna Zamfara Zamfara Circle Community Initiative ta bayyana cewa ’yan ta’addan sun kai hare-haren da suka kai kan kauyuka 15 inda suka jikkata mutane 16 a kananan hukumomi daban-daban. Ta bayyana...
Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta cafke wasu mutane shida da ake zargin ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane ne a karamar hukumar Doma da ke jihar. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar SP Ramhan Nansel ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai...
Mahalarta taron masu ruwa da tsaki na yini daya don tabbatar da sakamakon bincike kan al’amuran zamantakewa da suka shafi ilimin ‘ya’ya mata a jihar Zamfara, sun bukaci iyaye, shugabannin al’umma, da gwamnati a dukkan matakai da su magance matsalolin da ke hana yara mata zuwa kammala karatun sakandare. Kungiyar AGILE da ke Jihar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wata kotu a kasar Chadi ta daure tsohun firai ministan kasar Succes Masra shekaru 20 a gidan kaso da taran caifa biliyon guda a jiya Asabar. Shafin yanar gizo na Labarai Afrika Newas ya kara da cewa kotun ta tabbatar da laifin kan dan siyasar, kuma dan adawa da gwamnatinn Debi, da laifin watsa wasu...
A kokarin ta na ci gaba da kula da harkokin ilimi a yankin, Karamar Hukumar Birnin Kudu dake Jihar Jigawa ta kaddamar da aikin tantance malaman makaranta na B teach da kuma ma’aikatan lafiya na wato B health. A jawabin sa wajen fara tantance malaman da ma’aikatan lafiyar, Shugaban karamar hukumar, Dr Muhammad Uba...
Jami’an Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), sun kai samame a Ɗakin Karatun Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, a Jihar Ogun, inda suka kama wasu matasa da ake zargin ’yan damfara ne. Samamen ya faru ne da safiyar ranar Lahadi a sashen otal na ɗakin karatun. ’Yan bindiga sun kashe gomman...
An sake shiga tashin hankali a Jihar Sakkwato bayan wani sabon mummunan hari da ’yan bindiga suka kai a wasu kauyuka, lamarin da ke ƙara tsananta matsalar tsaro a faɗin jihar. Rahotanni sun nuna cewa duk shekara musamman a lokacin damina, ’yan bindiga sukan ƙara ƙaimi wajen kai hare-haren da ke tarwatsa jama’a a garuruwansu...
Gwamnan ya kuma umurci jami’an tsaro da su rufe gidan rediyon tare da nemo bayanan mai gidan rediyon, inda ya zarge ta da haddasa tashin hankali. Sai dai a kara mai lamba FHC/L/CS/1587/2025 da aka shigar a ranar Juma’ar da ta gabata a babban kotun tarayya da ke Legas da SERAP da kuma NGE...
“Baya ga alaƙa da Ruwa, ƙasashen da ke Afirka ta Gabas da kuma waɗanda ke a Afrika ta Tsakiya, da suke yi musharaka da irin ƙalubalensu da kuma sauran damarmakinsu, dole ne mu zage mu amfana da tattalin arzikin da ake da shin a Tekuna, musamman ta hanyar haɗa kanmu da kuma yin haɗaka, wanda...
Don haka, kwamishinan ya gode wa ƙungiyar bisa wannan ziyara tare da bayyana shirin Ma’aikatar na yin haɗin gwiwa da haɗin gwiwa ta fuskar horarwa, wayar da kan jama’a, da wayar da kan jama’a game da SGBƁ. Tun da farko, Misis Achimugu ta bayyana cewa ziyarar bayar da shawarwarin ita ce kashi na biyu na...
Ali Akbar Velayati mashawarcin jagoran juyin juya halin Musulunci da Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan harkokin kasa da kasa ya tabbatar da cewa “Jamhuriyar Musulunci tana adawa da shirin kwance damara na kungiyar Hizbullah” yana mai jaddada cewa Iran a ko da yaushe tana goyon bayan al’ummar kasar Labanon da kuma gwagwarmayarsu. Da yake magana...
Kyari ya ce, a yanzu ana noma Waken Soya da ya kai kimanin tan miliyan 1.35, wanda kuma buƙatar da ake da shi a ƙasar ya wuce tan miliyan 2.7. Ya sanar da cewa, wanan tsari zai kuma amfani tattalin arziƙin ƙasar da ƙara samar da ayyuakn yi da kuma ƙara haɓaka samar da wadataccen...