2025-06-15@13:46:11 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1724

«Karamar Sallah»:

    Ya ce, “Muna matukar godiya ga gwamnatin Amurka saboda dorewar kawancen dabarun hadin gwiwa da Nijeriya.” Ya kara da cewa, sayan jirage masu saukar ungulu na AH-1Z Viper zai kara inganta yakin da NAF ke yi, da kwazon aiki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
    Kungiyar ‘Abokan Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya’ ta yi Allah wadai da harin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai kan Iran Kasashe mambobin kungiyar aminan yarjejeniyoyin Majalisar Dinkin Duniya sun fitar da wata sanarwa ta musamman inda suka yi kakkausar suka kan wuce gona da irin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran....
    Wasu Hare-haren da gwamnatin Isra’ila ta kai ya haddasa gobara a wasu matatun mai a lardin Bushehr da ke kudancin kasar Iran. Gobarar ta tashi ne a wurin a ranar Asabar bayan da wasu kananan jiragen yakin Isra’ila guda biyu suka kai hare-hare a kan kayayyakin sarrafa iskar gas da ke yankin kudancin Pars. Hare-haren...
    Kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO, ta gudanar da taron shekara-shekara na biyu, na hukumar zartaswar cinikayyar hidimomi a birnin Geneva dake kasar Switzerland a jiya Juma’a, inda bangaren Sin ya yi nuni da cewa, matakin Amurka game da harajin kwastam na tattare da rashin fahimta da rashin gaskiya a wasu fannoni, don haka ya...
    Hukumar Kula da Yanayi (NiMet), ta sake fitar da gargaɗi game da yiwuwar ambaliyar ruwa a wasu jihohin a daminar bana. A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, hukumar ta bayyana cewa Jihar Akwa Ibom ce ke fuskantar barazana mafi tsanani a halin yanzu. Gwamnan Kaduna ya bai wa sabon Sarkin Moro’a...
    Aƙalla Mutane biyar sun kwanta dama wasu huɗu kuma sun jiggata sakamakon tsinkewar igiyar lantarki bayan dawo da wutar lantarkin mai ƙarfi a unguwar Tudun Wadan Pantami, ta jihar Gombe. Kamar yadda wani mazaunin yankin Adamu Abubakar Kulani, ya shaidawa manema labarai, mummunan lamarin ya faru ne a daren ranar Juma’a yayin da aka kawo...
    Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bai wa sabon Sarkin Moro’a, Mai Martaba Isiaku Tagwai Sambo sandar mulki, a wani biki da aka gudanar a garin Manchok da ke Ƙaramar Hukumar Kaura. Gwamna Sani, ya bayyana cewa sarakunan gargajiya na taka muhimmiyar rawa wajen zaman lafiya, haɗin kai da kuma ci gaban al’umma. Ya kamata...
    An rufe taron ministocin Sin da Afirka mai tabbatar da ci gaban hadin gwiwar da aka samu a dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afirka wato FOCAC, wanda aka gudanar daga ranekun 10 zuwa 12 a birnin Changsha na lardin Hunan, matakin da ya bayar da sabbin damammaki ga kasashen Afirka, bisa shirin “manyan ayyuka...
    Ba tare da saninmu ba, yawancin al’ummar Afirka musamman ma naYammacin Afirka suna fama da abinda ake kira da suna irin hali ko yanayin da aka shiga sanadiyar lamarin cinikin Bayi.Bayan shekara 100 da aka yi daga shekarar 1801 zuwa 1901, an yi wani kokarin da ake yi ma kallon tamkar wani takune na yadda...
    Aƙalla mutum 26 ne suka rasu sakamakon wasu sabbin hare-haren da aka kai wasu ƙauyuka a Jihar Binuwai. Hare-haren sun faru ne a yankunan Ƙaramar Hukumar Makurdi da Katsina-Ala tsakanin ƙarfe 12 na dare zuwa 2 na daren ranar Alhamis. Farashin fetur ya tashi a kasuwar duniya bayan harin Isra’ila a Iran An kashe masu...
    Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyar ɗaukar matakai masu tsauri kan duk wanda aka samu da hannu a harkar fasa bututun mai da satar ɗanyen mai a yankin Niger Delta. Daraktan Tsaron Makamashi a Ofishin Mai baiwa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro (ONSA), Hon. Ojukaye Flag-Amachree, ne ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da...
    Ma’aikatar Gona da tsaron abinci ta tarayya ta sanar da gudanar da addu’a da azumi na kwanaki uku domin neman taimakon Allah wajen kare ƙasar nan da kuma tabbatar da wadatar abinci. Wannan na ƙunshe ne a wata takarda da aka fitar a ranar 11 ga Yuni, 2025, wadda Daraktar Gudanarwa, Mrs. Adedayo Modupe O.,...
    Jami’in kungiyar Hamas ya bayyana cewa: Kakkausan martanin da Iran ta mayar ya tabbatar da cewa babu mai girman kai da ba zai fuskanci mayar da martani ba Izzat al-Rishq mamba na ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya jaddada cewa: Kakkausan martanin da Iraniyawa suka mayar ya tabbatar da cewa; babu mai...
    Ya kuma bukaci da a ci gaba da hada hannu da masu ruwa da tsaki a fannin, musamman domin dakile kalubalen da ake fuskanta na rashin amfana da albarkatun da ke madatsar ruwan, musamman domin kara bunkasa fannin aikin noma da kuma kara samar da wadataccen abinci. A nasu martanin daban-daban, wasu daga cikin manoman...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya yi karin haske game da taron koli na Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya karo na biyu, wanda shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarta a Kazakhstan, yana mai cewa, Sin na da yakininta hanyar taro, ita da sauran kasashen yankin tsakiyar Asiya biyar, za su...
    Da yake magana kan muhimmancin bikin Ranar Dimokiraɗiyya ta bana, Idris ya ce wannan ba lokacin murna kaɗai ba ne, har ma lokaci ne na nazari kan cigaban ƙasar wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya da farfaɗowar tattalin arziki.   Ya bayyana cewa ana amfani da kuɗaɗen da aka tara daga cire tallafin man fetur wajen gina muhimman...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a yi koyi daga akidun dan mazan jiya, kuma jagora na gari Chen Yun, tare da kara azamar dorar da kyawawan dabi’unsa cikin himma da kwazo, don gina kasar Sin mai matukar karfi. Shugaba Xi, wanda shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar...
    Farashin Man Fetur ya tashi a kasuwar duniya bayan harin da Isra’ila ta kai wa Iran, lamarin da ya tayar da hankalin masu zuba jari. Ana fargabar cewa rikicin da ke ƙara taɓarɓarewa tsakanin ƙasashen biyu zai iya kawo tangarɗa wajen samar da man fetur daga yankin Gabas ta Tsakiya. An kashe masu garkuwa da...
    Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta Lebanon Sheikh Na’im Kassim ya yi Allawadai da harin da HKI ta kai wa Iran, wanda ya bayyana shi da cewa; Yana da hatsarin gaske, kuma ‘yan sahayoniyar sun yi hakan ne bisa cikakken goyon bayan Amurka. Sheikh Na’im Kassim ya kuma bayyana cewa; Harin na ‘yan sahayoniya ba shi...
    Sabon kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Birgadiya Muhammad Pakphur ya aike wa da jagoran juyin musulunci na Iran wasika da a ciki ya bayyana cewa: ” Laifukan ta’addanci da HKI ta aikata, wanda ya yi sanadiyyar shahadar manyan kwamandojin  da kuma  malaman Nukiliya, haka nan  mata da kananan yara da ba...
    Da yake maida martani, Mokwa ya ce gwamanti ta fara biyan bashin tallafin rage radadin ga ma’aikata. Ya ce za a ci gaba da biyan kudin ne kashi-kashi har zuwa nan da watanni hudu masu zuwa. “Mun fara biyan bashin nira 35,000 ga ma’aikata. Illar kawai wasu ma’aikatu da suka kasance masu cin kashin kansu...
    Ya ce Jihar Kurus Ribas ita ce ta farko a yankin kudu da ta shiga a dama da ita a harkar noman alkama, lamarin da ke nuni da gayar nasara wajen samar da abinci a kowani sassa na kasar nan. Kyari ya kara da cewa shirin rabar da takin zamani ya taimaka wajen bunkasa samar...
    A cewarsa, dukkanin takardar neman kirkirar sabon masarauta ko sarki ko gunduma dole ne a aike zuwa addireshin gwamnan jihar ta hannun babbar sakatariyar ma’aikatar kananan hukumomi da kula da masarautu na jihar. Kazalika, ya ce dole ne masu nema su gabatar da takaitaccen tarihin al’ummar da suke nema wa masarauta ko sarki ko gudunmawa...
    Ya kuma tuna irin muhimmiyar rawar da Majalisar tarayya ta taka a lokuta masu sarƙaƙiya a tarihin Nijeriya, ciki har da daƙile shirin ƙara wa’adi na uku da kuma kafa “Dokar Bukata” lokacin rasuwar tsohon shugaban ƙasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
    Sai dai, ya sanar da cewa, ya janye kurin ne, bayan ya tuntubi daidaikun mutane da sauran kungiyoyi a daukacin fadin kasar. Halin girma da dakkun da Shugaba Abba ya nuna na janye wannan kurin bayan korafe-korafen alummar asar kasar, babu shakka janyewar abu ne, da ya dace, musamman duba da cewa, tursawa ‘yan kasa...
    Abdulazeez pleaded not guilty to the two-count charge. Abdulazeez ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da su biyu. Bayan rokon da ta yi, lauyan ICPC, Hamza Sani, ya bukaci kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 13 ga watan Yuni, 2025, domin masu gabatar da kara su gabatar da shaidu. Sai dai daga baya...
    Baya ga haka, Sojojin sun kashe ƙarin ‘yan ta’adda goma da suka taru kusa da wani gidan mai a Danjibga, waɗanda ake zargin sun kasance cikin wata tawagar da Dogo Sule ya tara domin kitsa hari. Manjo Janar Kangye ya jaddada cewa rundunar Soji za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare...
    A wani bayani na hadin gwiwa da hukumar makamashin Nukiliya ta Iran da kuma ma’aikatar harkokin wajen Iran su ka fitar, sun bayar da umarnin a bude wani wuri na daban na sirri domin ci gaba da tace sanadarin Urani’um, sannan kuma a maye gurbin bututu tace sanadarin mai  mataki na daya, da mai mataki...
    Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Manjo Janar Hussain Salami ya fada a yau Alhamis cewa; Abokan gaba suna yi mana barazana da yaki, sannan ya tabbatar da cewa a shirye suke su fuskanci duk abinda zai faru. Manjo janar Salami wanda ya gabatar da jawabi ga taron dakarun sa-kai na “Basiji...
    Wata mummunar guguwa ta yi sanadin mutuwar mutum shida sannan ta jikkata wasu 30 a garin Garba-Chede da ke karamar hukumar Bali a jihar Taraba. A cewar wani mazaunin yankin wanda guguwar ta lalata wa gida mai suna Abubakar Dodo, an shafe shekaru masu yawa ba su ga irin ta ba a yankin saboda munin...
    Majiyar tsaron kasar ta Kamaru sanar da cewa, da dama daga cikin sojojin kasar sun rasa rayukansu sanadiyyar wani hari da kungiyar Bokoharam ta kai musu ta hanyar amfani da manyan bindigogi da kuma jirgin sama maras matuki akan iyaka da Najeriya. Majiyar ta ce an kai harin ne a yankin Sagami dake kusa da...
    Haka kuma, ya zargi Matawalle da karɓar Naira miliyan 300 daga tsohon gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, don a sako ɗaliban, amma ya bai wa ‘yan bindiga miliyan 30 kacal. APC ta ƙaryata wannan zargi. Ta kuma bayyana cewa zargin Kaura yana shafar wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar kamar tsohon Gwamna Abdulaziz Yari, wanda yanzu ke...
    Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), ta kama mutane 11 da ake zargi da aikata damfara a Intanet a Jihar Kaduna. Kakakin hukumar EFCC, Dele Oyewale, ya bayyana cewa an kama waɗanda ake zargin ne a unguwannin Mahuta da Barnawa bayan samun sahihan bayanai game da ayyukansu na yaudara ta...
    A cewarsa, gobarar na iya kasancewa ta samo asali ne daga wani gini da ke bayan gidan man. Rahotanni sun nuna cewa gobarar na iya tashi ne daga tankunan mai da ke ƙasa, kafin ta bazu zuwa cikin gidan man gaba ɗaya. Hukumar kashe gobara ta jihar ta yi gaggawar killace wajen domin hana cunkoso...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba An ayyana 12 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin Ranar Dimokuradiyya a Najeriya don tunawa da ranar da aka gudanar da zaben da aka yi amanna cewa shi ne mafi sahihanci da inganci a tarihi. Sai dai bayan fiye da shekara 30 da wannan zabe da fafutukar...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas aragchi da tokwransa na kasar Masar Badr Abdullati da kuma tokwaransu na kasar Omman Badr ben Hamad Al-Busaidi sun tattauna a tsakaninsu a birnin Oslo inda suka halattar taron tattaunawa ta 22th da ake gudanarwa a birnin na Oslo babban birnin kasar Norway. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar...
    A Shenzhen dake kudancin Sin ma, ana amfani da jiragen marasa matuka wajen jigilar kayayyakin kiwon lafiya ta yadda hakan ke magance tsaikon da ake samu saboda cunkoson motoci a tituna da kuma taimakawa wajen ceto rayukan marasa lafiya da ke bukatar daukin gaggawa. Bugu da kari, an samar da tsarin sufurin jirage masu tafiya...
    Wani ganau mai suna Kespan Iliya wanda shi ma mazaunin unguwar ne ya shaida wa manema labarai cewa, ‘yan unguwar na cikin barci lokacin da ‘yan bindigar suka iso cikin shigar kwamandoji, inda suka rika harbe-harbe kan mazauna unguwar.   LEADERSHIP ta fahimci cewa, sama da gidaje 96 ne kuma aka kone a Gyenbwas, al’ummar...
    Rayukan aƙalla mutum 15 sun salwanta a wasu sabbin hare-haren da aka kai  wasu ƙauyuka biyu na ƙaramar hukumar Mangu a Jihar Filato. Shugaban ƙaramar hukumar, Emmanuel Bala, ya shaida wa manema labarai cewa, a daren ranar Talata ce aka kashe mutum bakwai a kauyen Bwai sai kuma mutane takwas a kauyen Chinchim duk a...
    Cherki ya buga wasansa na farko a Lyon yana da shekara 16 a watan Oktoban 2019 kuma ya bar kungiyar inda ya ci kwallaye 29 sannan ya taimaka aka jefa 45 a wasanni 185 da ya bugawa kungiyar ta Faransa. Cherki ya wakilci kasar Faransa kuma ya lashe lambar azurfa a gasar Olympics da aka...
    Don haka, a cikin sanarwar da aka fitar a wannan karo, kasashen Afirka sun nuna yabo kan jajircewar kasar Sin, da kuma kudurin da kasar ta dauka na kare adalci, da kuma ingancin tsare-tsaren tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa. Har ila yau, kasar Sin ita ma ta nuna godiya ga kasashen Afirka,...
    Majalisar Dokokin Jihar Kuros Riba, ta dakatar da shugabar Ƙaramar Hukumar Bekwara, Hon. Theresa Ushie, na tsawon wata uku, domin a gudanar da bincike kan wasu zarge-zarge da ake mata. An ce kimanin wakilan ƙaramar hukumar 10 daga cikin 11 ne suka yi ƙarar shugabar, inda tara daga cikinsu suka rattaba hannu suna goyon bayan...
    Bayanai sun nuna cewa, harin na faruwa, aka sanar da jami’an tsaro. Sun isa cikin gaggawa da motocinsu da jirgin sama mai saukar ungulu. Amma maharin ya ƙi miƙa wuya, hakan ya sa aka bindige shi. Daga cikin waɗanda suka mutu, mata shida ne, maza uku, sannan wasu da dama sun jikkata sakamakon harbin bindiga....
    Kamfanin Dakon Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da cewa za a dauke wutar lantarki a ilahirin jihohin yankin Arewa maso Gabas guda shida na tsawon kwana hudu. A cikin wata wasika da ya aike wa kamfanonin rarraba wutar lantarki da ke kula da jihohin shida, TCN ya ce yayin da a wasu jihohin...
    Kungiyar kwallon kafa ta Iran ta sami nasarar akan abokiyar karawarta ta kasar Korea Ta Arewa da kwallaye uku masu kyau a wasan da aka yi a filin wasa na “Azadi” na Tehran. Kasashen biyu dai suna a karkashin; bangare na uku  a Asiya saboda share fagen kai wa ga shiga gasar cin kofin kwallon...
    Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta yi fatali da bukatun Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio kan dakatacciyar Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, sannan ta ci shi tarar Naira 100,000. Kotun, wacce ke karkashin jagorancin Mai Shari’a Hamman Barka dai ta yi watsi da bukatun ne kan karar da aka shigar ranar 21 ga...
    Akpabio ya shigar da buƙatu a gaban kotun inda ya nemi ƙarin lokaci don ɗaukaka ƙara a kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke a ranar 10 ga watan Maris, 2025. Wannan shari’a ta haɗa da Sanata Natasha da ke ƙarar Sakataren Majalisar Tarayya da wasu mutane uku kan dakatar da...
    Sojojin kasar Yemen sun bada sanarwan kai hare-hare da makamai masu linzami kan tashar Jiragen sama na Bengerion a birnin Yafa (telaviv) a safiyar yau Laraba. Kuma makaman sun sami inda ake bukata. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta kara da cewa sojojin sun yi amfani da makamai masu linzami samfurin Bilistet a...
    Gwamnatin kasar Burtaniya ta bada sanarwan kakabawa ministocin HKI guda biyu takunkuman tattalin arziki saboda ra’yinsu na wuce gona da Iri wanda zai bata duk wani shirin da kasashen duniya suke da shin a tabbatar da zaman lafiya a yanking abas ta tsakiya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kira-kirayen ministocin...
    Ma’aikatar leken asiri ta kasar Iran ta fidda farkon bayanan sirra wanda ta samo daga HKI wadanda kuma suke tabbatar da dangantakar da hukumar IAEA take da shi da HKI da kuma sauran kasashen yamma da hukumomin tsaronsu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran tace a cikin bayanan da ma’aikatar ta wallafa ya zuwa...