2025-11-28@00:13:08 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4174
«Ammar dan Yasir»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya mayar da martani ga shugaban Amurka Trump cewa: su ci gaba da mafarkinsu! Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a yayin da yake tsokaci kan kalaman shugaban Amurka a yayin ziyarar da ya kai yankunan da aka mamaye, ya ce Trump cikin alfahari ya ce kasarsa ta yi luguden bama-bamai tare da lalata cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, yana mai mayar msa da martani cewa: “To, su ci gaba da yin mafarkinsu!” A yayin ganawarsa da safiyar yau da zakaran wasanni kuma wadanda suka lashe gasar Olympics ta kasa da kasa, Jagoran ya kara da cewa: Duk abin da kuke yi ana danganta shi da Iran da kuma al’ummar kasar ne, kuma...
Babban sakataren majalisar kolin tsaron kasar Iran ya karbi bakwancin takwaransa na kasar Iraki a birnin Tehran Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani, ya karbi bakwancin mai baiwa kasar Iraqi shawara kan harkokin tsaro, Qasim al-Araji. A yau litinin ne mai baiwa kasar Iraqi shawara kan harkokin tsaro, Qasim al-Araji, ya iso birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran, inda yake jagorantar wata babbar tawaga ta tsaro. Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya gana da mai baiwa kasar Iraqi shawara kan harkokin tsaro Qasim al-Araji, inda suka tattauna batutuwa da dama musamman kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen biyu da muhimman mu’amalar da ke tsakaninsu. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify...
Wakilin Amurka Na Musamman A Siriya Ya Matsa Don Ganin Kasashen Saudiyya Da Lebanon Da Kuma Siriya Sun Kulla Alaka Da Isra’ila
Wakilin Amurka na Musamman a kasar Siriya ya matsa kaimi domin ganin kasashen Saudiyya da Lebanon da kuma Siriya sun kulla alakar jakadanci da haramtacciyar kasar Isra’ila Wakilin Amurka na musamman a Siriya Tom Barrack, ya gabatar da manufofinsa na sake fasalin yankin Gabas taTsakiya a siyasance bayan kawo karshen yakin Gaza. A cikin dogon hangen nesa, wanda ya wallafa a shafinsa na Twitter, Barrack ya yi ikirarin cewa abu mafi muhimmanci shi ne samar da zaman lafiya a yankin, da kwance damarar Hizbullah, da shigar da kasashen Labanon da Siriya cikin yarjejeniyoyin kyautata alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila. Ya kara da cewa Saudiyya ma tana dab da kyautata alakarta da haramtacciyar kasar Isra’ila. Barrak ya bayyana cewa: Taron Sharm...
Kungiyar kare hakkin dan Adama ta Amnesty International ta ce: Gwamnatin Tanzaniya ta wurga yanayin tsoro tare da tsananta danniya gabanin babban zaben kasar Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta zargi mahukuntan Tanzaniya da haifar da yanayin tsoro da kuma tsananta danniya gabanin babban zaben da aka shirya yi a ranar 29 ga watan Oktoba, tare da yin amfani da dabarun yaki da ‘yan adawa, ‘yan jarida, kungiyoyin farar hula, da masu kare hakkin bil’adama. Amnesty International ta bayyana cewa: Gwamnatin shugaba Samia Hassan na ci gaba da ayyukanta na danniya da suka hada da kama mutane ba bisa ka’ida ba, tilasta bacewar mutane, da kuma kashe-kashen ba bisa ka’ida ba, ba tare da hukunta wadanda suka...
Gwamnan ya kuma buƙaci mambobin majalisar da su kasance masu aiki da faɗakarwa, su kasance kusa da jama’ar yankunansu da kuma shugabannin ƙananan hukumomi. Ya umarce su da su riƙa isar da rahotanni na yau da kullum ga Kwamishinan Tsaro, tare da yin addu’a ga waɗanda suka rasa rayukansu wajen kare al’umma da zaunar da zaman lafiya a jihar. Bugu da ƙari, Gwamna Lawal ya ƙarfafa mambobin majalisar su ƙara haɗin kai da sauran jami’an gwamnati domin tabbatar da ingantacciyar tafiyar da al’amuran mulki da gudanar da ayyukan ci gaba cikin nasara. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta October 20, 2025 Ra'ayi...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ‘Yansanda Sun Kama Alburusai 400 A Delta October 20, 2025 Manyan Labarai Ɗan Jarida Ibrahim Ɗan’uwa Rano Ya Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Tsare Shi October 19, 2025 Manyan Labarai Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jarida A Kano Bisa Zargin Ɓata Suna October 19, 2025
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Alkalan Najeriya su kasance masu gaskiya, rikon amana da tsoron Allah wajen yanke hukunci. Ya ce duk wata al’umma tana fara rushewa ne idan bangaren shari’a ya lalace. Ya bayyana cewa gwamnati na kokarin inganta walwala da albashin Alkalan domin karfafa ikon cin gashin kansu. Da yake bude taron bita na EFCC da NJI a Abuja, Shugaban wanda Mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta ya ce adalcin Alkalai ne ginshikin ci gaban kasa. Ya nuna damuwa kan yadda ake jinkirta shari’o’in manyan laifukan rashawa, yana mai cewa an fi hanzarta shari’ar masu laifin yanar gizo. Shugaba Tinubu ya jaddada cewa ba a taba kare kowa saboda siyasa a gwamnatinsa ba, inda ya bayyana cewa EFCC...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Alkalan Najeriya su kasance masu gaskiya, rikon amana da tsoron Allah wajen yanke hukunci. Ya ce duk wata al’umma tana fara rushewa ne idan bangaren shari’a ya lalace. Ya bayyana cewa gwamnati na kokarin inganta walwala da albashin Alkalan domin karfafa ikon cin gashin kansu. Da yake bude taron bita na EFCC da NJI a Abuja, Shugaban wanda Mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta ya ce adalcin Alkalai ne ginshikin ci gaban kasa. Ya nuna damuwa kan yadda ake jinkirta shari’o’in manyan laifukan rashawa, yana mai cewa an fi hanzarta shari’ar masu laifin yanar gizo. Shugaba Tinubu ya jaddada cewa ba a taba kare kowa saboda siyasa a gwamnatinsa ba, inda ya bayyana cewa EFCC...
Morocco ta ɗaga Kofin Duniya na FIFA U20 a karon farko a tarihin gasar, bayan ta doke Argentina da ci 2 da nema, tawagar da ta fi kowace ƙasa a duniya lashewa a tarihi Wannan gagarumar nasara ya sa ta zama ƙasar Afirka ta biyu da ta ɗaga wannan kofi bayan Ghana, wadda ta yi nasara a shekarar 2009. Gwamnonin Kano, Katsina da Jigawa sun ƙulla yarjejeniyar bunƙasa wutar lantarki Kano Pillars ta dakatar da Kocinta A yammacin jiya Lahadi ce aka gudanar da wasan ƙarshe a filin wasa na Estadio Nacional Julio Martínez Prádanos da ke birnin Santiago na Chile, gidan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Universidad de Chile da kuma babbar tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar. ‘Yan wasan tawagar ƙwallon...
Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada kudirinta na inganta harkar kiwon lafiya a fadin kasar nan, daidai da manufar sabunta kudiri na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wato Renewed Hope Agenda. Wannan tabbacin ya fito ne daga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, yayin da yake ziyarar duba ayyukan gine-gine da ke gudana a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), wanda shi ne ya tallafa wajen samar da su. Yayin da yake magana da ’yan jarida a lokacin ziyarar, Sanata Barau ya ce wadannan ayyuka na da nufin kara karfin cibiyoyin kiwon lafiya a cikin gida, tare da rage yawan tafiyar da ake yi zuwa kasashen waje domin neman magani, ta hanyar samar da ingantattun kayan aiki a asibitocin cikin gida....
Don haka, an nada “tsohon kaftin din kungiyar kuma mataimakin koci, Gambo Muhammad, tare da mai horar da masu tsaron gida, Suleiman Shuaibu, su maye gurbin wadanda aka sallama na dan wucin gadi. Bugu da kari, Koci Garzali Muhammad (Kusa) daga Junior Pillars zai taimakawa wadanda aka nada na dan wucin gadin”. LEADERSHIP ta ruwaito cewa, kungiyar mai taken ‘Sai Masu Gida’ tana fama a ‘yan makonnin nan. Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya ta kuma ci tarar kungiyar tarar kudi sama da Naira miliyan 9 biyo bayan rikicin da ya ɓarke a yayin da suke karawa da wata kungiya a filin wasa na Sani Abacha. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A...
A yau ne Tsohon shugaban kasar faransa Nicola sarkozi zai fara zama a gidan yari na tsawon shekara biyar, bayan da da aka same shi da laifin hada baki a watan da ya gabata kan badakkalar kudaden yakin neman zabe daga kasar libiya a zaben shugaban kasa na shekara ta 2007 wanda ya sanya ya zama tsohon shugaban kasa na farko daga wata kasa ta tarayyar turai da zai taba zama a ginda yari, Wanan hukumcin dai ya faro ne daga zargin da aka yi wa gwamnatin muammar ghaddafi ta libiya na bada wasu kudade ba bisa ka’ida ba a yakin neman zaben Sarkozy a shekara ta 2007 , Alkalan faransa sun yanke wannan hukumcin cewa tsohon shugaban kasar ya...
An ce wanda ake zargi da kisan, sananne ne a garin Zing saboda yawo a kan tituna, sanye da fararen kaya yana yin kamar yana wa’azi. Wakilinmu ya ruwaito cewa, lamarin da ya faru da misalin karfe 11 na daren ranar Asabar, ya jefa al’ummar garin Zing da kewaye cikin rudani kan hakikanin yanayin lafiyar wanda ake zargin. “Daga cikin wadanda suka jikkata akwai ’yan banga guda biyu, wadanda a baya suka yi kokarin hana wanda ake zargin shiga jama’a saboda irin halayyarsa,” in ji wani ganau. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ‘Yansanda Sun Kama Alburusai 400 A Delta October 20, 2025 Labarai Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC October...
“Rundunar ‘yansandan sashi ‘C’, Asaba, karkashin jagorancin CSP Ogbe Emmanuel, sun samu nasarar tare wata mota ɗauke da alburusai da aka nufi jihar Edo da su. “A yayin da jami’an suke gudanar da binciken motoci na yau da kullum a kan babbar gadar Asaba, jami’an sun yi nasarar tare wata mota kirar ‘Toyota Hiace Hummer Bus’ mai lamba NGK 16 XB, wacce wani Ozoemenam Sylvanus ke tukawa. “Yadda Direban, ke amsa tambayoyi cikin rashin nutsuwa, ya jawo jami’an suka fahimci cewa, ba shi da gaskiya inda suka gudanar da bincike sosai a kan motar, inda aka gano alburusai 400 da aka ɓoye a cikin motar. “Wanda ake zargin da farko ya yi karyar cewa makullai ne aciki,...
Gwamnatin kasar Yemen ta kama wasu ma’aikatan MDD a ranar Lahadi a cikin kasar a wani sumamen da Jami’an tsaron kasar suka yi kan sansaninsu, inda suka kama ma’aikatan suka kuma kawace kayakin aikinsu. Shafin yada labarai na Yanar Gizo ArabNews na kasar Saudiya sun ya nakalto kamfanin dillancin labaran Associated Press yana cewa a jiya Lahadi ne jami’an tsaron yemen suka kama yemenawa 11 da kuma yan kasashen waje 15 a wani wurin aikinsu a unguwar Hada na birnin San’a babban birnin kasar. Labarin ya kara da cewa sun sallami 11 daga cikinsu bayan tambayoyi masu yawa. Jean Alam kakakin MDD a yemen ya tabbatar da wannan labarin ya kuma kara da cewa hukumarsa ta tuntubi jami’an gwamnati a...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan fara shari’ar Nnamdi Kanu a shekarar 2021 mutane da dama suke bayyana ra’ayoyinsu a kan sake shi ko a kyale shari’a ta yi halinta. Hasali ma har zanga-zanga wasu ‘yan Najeriya suka kira don bayyana bukatar sakin shugaban na ‘yan aware. NAJERIYA A YAU: Yadda Cire Darasin Lissafi Zai Taimakawa Dalibai Shiga Jami’a DAGA LARABA: Shin Ko Jam’iyyar PDP Ta Fara Gushewa Ne? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan ko ya dace a saki Nnamdi Kanu? Domin sauke shirin, latsa nan
An saki ɗan jarida, Ibrahim Ɗan’uwa Rano, bayan da ƴansanda suka tsare shi a shalƙwatar Rundunar Ƴansanda ta Zone 1 Kano bisa zargin batanci ga wani mutum. Sakin nasa ya biyo bayan suka da matsin lamba daga ƙungiyoyin fararen hula irinsu Cibiyar Fasahar Bayanai da Ci Gaban Jama’a (CITAD), da Amnesty International, da sauran ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam, waɗanda suka bayyana tsarewar tasa a matsayin mataki na keta haƙƙin ɗan Adam da kuma yunƙurin danne ƴancin ƴan jaridu. Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jarida A Kano Bisa Zargin Ɓata Suna Fitatccen Ɗan Jarida A Kano Aliyu Abubakar Getso Ya Rigamu Gidan Gaskiya Ƙungiyoyin sun buƙaci a sake shi ba tare da wani sharaɗi ba, suna mai cewa tsarewar ta saɓawa...
Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim ya mika sakon ta’aziyyar shahadar babban hafsan hafsoshin sojan kasar Yemen Birgediya janar Muhammad Gumari ya shugaban Ansarullah Sayyid Abdulmalik al-Husi. Shekh Na’im Kassim ya bayyana alhininsa mai zurfi na rashin Shahid al-Gumari tare da bayyana shahada a matsayin wata daukaka bayan doguwar tafiya akan tafakin jihadi.Haka nan kuma ya bayyana cewa;shahidin na Yemen ya jagoranci sojojin kasar cikin jarunta, ya kuma taimakawa Gaza wajen fuskanta laifukan ‘yan sahayoniya da Amurka. Haka nan kuma babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya ce; yin shahadar jagorori wani alfahari da daukaka ne ga al’ummar musulmi, domin jinanensu sun hade a wuri daya, daga Yemen zuwa Lebanon da Iraki da Iraki. Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya...
Tashar talabijin din ‘aljazira’ ta bayar da labarin da yake cewa, sojojin na HKI sun yi kutse cikin yankin Qunaidhara da motoci 10 da safiyar yau Lahadi. Majiyar ta kara da cewa; sojojin na HKI sun shiga cikin kauyen al-Hanut dake yankin na Qunaidhara a kudancin kasar ta Syria tare da kafa shinge a tsakanin wannan kauyen da kuma Saidah a Julan. Bugu da kari sojojin na HKI sun rika binciken motocin mutanen Syria da suke wucewa ta wannan yankin, tare da yi wa wasu samari da dama tambayoyi. Tun bayan kifar da gwamnatin Basshar Asad Sojojin HKI suke yin kutse a cikin kasar Syria a duk lokacin da su ka ga dama, bayan da su ka rushe kaso 80%...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xinjiang Ta Janyo Karin Jari A Rubu’i Uku Na Farkon Shekarar Nan October 19, 2025 Daga Birnin Sin Tawagar Likitocin Sin Ta Samar Da Tallafin Jinya Ga Kananan Yara Kyauta A Togo October 19, 2025 Daga Birnin Sin An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin October 18, 2025
’Yan Sanda sun saki ɗan jaridar Kano, Ibrahim Ɗan Uwa Rano, bayan tsare shi da suka yi kan zargin ɓata sunan hadimin Gwamnan Jihar, Abdullahi Ibrahim Rogo. An tsare Rano a Shiyyar ’Yan Sanda ta Ɗaya da ke Kano, bisa zargin ɓatanci. Talauci ne babban maƙiyin ɗan Adam — Atiku ’Yan sanda sun tsare ɗan jarida kan zargin ɓata sunan hadimin gwamnan Kano Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun bayyana tsare shi a matsayin saɓa doka da kuma ƙoƙarin danne ’yancin ’yan jarida.
Sunana Aisha Isah Abubakar (Mai Waka) Gama: A gaskiya bawa yara kanana kudi wannan ba dabi’a ce mai kyau ba, saboda wata rana idan babu wannan kudi da aka sabawa yaro da shi wallahi illa ce babba. Sabida yau da gobe sai Allah idan suka rasa wannan kudi komai zai iya faruwa za su iya saka hannu su diba ako’ina, saboda su biya wa kansu bukatar su. Shawara ya kamata masu dabi’ar aiken yara su basu kudi dan Allah su daina, gara ku siyi ‘sweet’ idan yaro ya dawo a bashi ya fi a dauki kudi a bashi. Allah ya sa mu dace. Sunana Aminu Adamu, Malam Maduri A Jihar Jigawa: To magana ta gaskiya sam-sam hakan bai dace...
’Yan sanda sun kama ɗan jarida Ibrahim Ishaq Dan’uwa Rano, kan zargin ɓata sunan Babban Hadimin Gwamnan Kano kan Al’amuran Fadar Gwamnati, Abdullahi Ibrahim Rogo. Rahotanni sun bayyana cewa jami’an ’yan sanda daga Hedikwata ta Ɗaya ne suka kama Dan’uwa Rano a ranar Asabar yayin da yake aiki a ofishinsa da ke Kano. Magidanci na neman shawarar ’yan sanda kan ƙara aure a Kano Gwamnati ta ɗauki matakin rage shan gishiri a Nijeriya Shaidu sun ce an kama shi ba tare da gabatar da takardar izinin kama shi ba. Ana tsare da ɗan jaridar ne bisa zargin ɓata sunan hadimin cikin wani shirin barkwanci mai suna ‘Imalu’ da yake wallafawa a shafinsa na YouTube mai suna ‘Dan’uwa TV‘. An ce...
Abubuwan bukata: Tafarnuwa, Kanunfari, Kurkum, Citta danya, Kajiji, Kimba, Bagaruwa, Masoro, Aiden fruit, Cinnamon sticks, Lemon tsami, Ruwa Lita 6 Yadda za a hada: Hade su ake yi a tafasa a rika sha kofi daya safe da yamma na kwanaki bakwai, In sha Allah za a samu lafiya. A kiyaye Ban da maza marasa aure, Ban da mata masu ciki, Ban da masu Olsar da ta yi tsanani. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Adon Gari Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki? October 12, 2025 Adon Gari Ko Kin San… Dalilin Da Ke Sa Mata Ke Ganin Farin Ruwa Kafin Ko Bayan Al’adarsu? August 31, 2025 Ado Da Kwalliya Hanyoyin Da Za A Bi...
Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa, wanda ake zargin wanda aka ce shi ne Shugaban kungiyar ‘yan acaɓa reshen Ejiba, ya amsa cewa, ya siyo ƙwayoyin ne a wani shagon sayar da magunguna da ke Egbe domin kai wa abokan hulɗar sa da ke cikin dajin. Babban sakataren yaɗa labarai na shugaban karamar hukumar Yagba ta yamma, Adeyemi Babarinde Sunday, ya ce an kuma samu wanda ake zargin da kuɗi har ₦600,000, wanda ake zargin kudaden hada-hadar ta’addanci ne. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza October 19, 2025 Labarai Gwamnatin Nijar Ta Yaye Tsofaffin Mayaka 369 Da Aka Bai Wa Horon Sauya Tunani October 19, 2025 Manyan...
A ta bakin shugaban bikin, kuma gwamnan Jihar Tillabery Maina Boukar, taron na wannan karo ya shaida aniyar gwamnatin Nijar, ta bai wa wadanda suka rungumi shirin ajiye makamai damar sauya rayuwarsu, da taimaka musu wajen cimma nasarar komawa cikin al’umma cikin mutunci. Boukar ya ce, “Wannan muhimmin zabi, ya nuna aniyar gwamnatin Nijar ta kare ikon mulkin kai, da wanzar da tsaro, da tabbatar da zaman lafiya karkashin kyawawan manufofin kasa, ba tare da dogaro ga wasu ajandoji daga ketare ba.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi October 19, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki October 18, 2025...
Haka zalika, an yi zargin cewa; bai kammala karatun digirinsa na farko ba, sannan kuma takardar shaidar yi wa kasa hidima (NYSC) da ya mika wa majalisar dokokin kasar da shugaban kasa ta bogi ce. Sai dai, ya zargi Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, da daukar nauyin zarge-zargen da ake yi masa na takardar shedar bogin, sakamakon dalilai na siyasa. Da yake magana ta bakin mai magana da yawunsa, Dakta Robert Ngwu, ministan ya ce; zargin da suke na siyasa ne, inda ya yi zargin cewa; gwamnan yana shirin shiga jam’iyyar APC mai mulki ne, wadda shi Nnaji ke da karfi a cikinta. Ya kara da cewa, “Mbah yana so ya fitar da Nnaji daga tsarin ne kwata-kwata, domin kuwa...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Kuduri mai lamba 2231 ya ƙare aiki a yau A cikin wata wasika da ya aike wa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da shugaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ministan harkokin wajen kasar Iran ya tabbatar da cewa a karshe kuduri mai lamba 2231 ya kare a yau, kuma duk wani kira na farfado da shi ko dawo da wa’adin kudirorin da ya kare, ba shi da wani tushe na shari’a, kuma ba zai iya haifar da wani tasiri na tilasta aiki da shi ba. Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Sayyid Abbas Araqchi ya aike da wasika zuwa ga babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da kuma shugaban kwamitin sulhu...
Makami mai linzami na Iran kirar “Ghadr-H” ya aika da sako mai muni ga gwamnatin mamayar Isra’ila Wani masani kan harkokin tsaro da tsare-tsare Kanar Abdul Karim Khalaf ya bayyana cikakkun bayanai masu inganci da siffofi na musamman na makami mai linzamin na Iran “Ghadr H”, yana mai jaddada cewa; Makamin ya aike da sako mai karfi ga gwamnatin mamayar Isra’ila saboda karfin da take da shi na kutsawa cikin mafi tsauri na tsaron iska da kuma gujewa radar. Khalaf ya bayyana a cikin bayanansa cewa: “Ghadr” ya bambanta da sauran hasken wadda da ba a taba ganin irinsa ba a cikin yaki da kuma karfin da yake da shi na barna saboda fasahar da ke dauke da shin a...
Jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Ruguza Gaza “ba abin da za a gaskata ba ne” domin an rusa yankin gaba daya Mataimakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya mai kula da harkokin jin kai, Tom Fletcher, ya ce: Girman barnar da aka yi a zirin Gaza abu ne da ba za a taba mantawa da shi ba, yana mai jaddada cewa, “an ruguza komai tare da mai da yankin baraguzai,” yana mai nuni da irin barnar da aka yi wa ababen more rayuwa, da gidaje, da kashe fararen hula. A cikin wata sanarwa ga gidan talabijin na Al Jazeera, Fletcher ya nuna cewa an riga an fara shirin ba da agajin jin kai na kwanaki 60. Shiri ne mai...
Tsohon Shugban Kasar Dimokaradiyyar Kwango Ya Koma Kasarsa Domin Kalubalantar Hukuncin Kisa Da Aka Yanke Kansa
Tsohon shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango ya dawo kasarsa daga Nairobi domin kalubalantar hukuncin kisa da aka yanke masa A wani gagarumin ci gaba na siyasa, tsohon shugaban kasar Kwango Joseph Kabila, ya bayyana a bainar jama’a a Nairobi babban birnin kasar Kenya, bayan da a makonnin da suka gabata wata kotun soji a kasarsa ta yanke masa hukuncin kisa bisa zargin “cin amanar kasa da laifuffukan yaki. Wannan lamari ya faru ne kwatsam da ya haifar da cece-kuce a fagen siyasa da kafofin watsa labarai, musamman ma dai a daidai lokacin da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango ke fama da rikicin tsaro da na siyasa. Kabila wanda ya mulki kasar a tsakanin shekarar 2001 zuwa 2019, ya jagoranci wani taron da aka...
Bayan dawowarsa kasar Sin, Yang ya ci gaba da koyarwa a jami’ar Tsinghua, inda cikin sama da shekaru 20 ya bayar da muhimmiyar gudummawa wajen kyankyashe, da horar da sabbin masu hazaka, da yayata musayar ilimi tsakanin sassan kasa da kasa. (Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai October 18, 2025 Daga Birnin Sin Mataimakin Firaministan Sin Ya Zanta Da Sakataren Baitul-mali Da Wakilin Cinikayyar Amurka October 18, 2025 Daga Birnin Sin Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO October 17, 2025
“Wannan mummunan lamari da ya faru a ranar 11 ga Oktoba, 2025, a Wawa Cantonment, Jihar Neja, ya haifar da yanayi mai cike da tashin hankali, inda mazauna sansanin suka shiga cikin mamaki kan yadda irin wannan abin takaici zai iya faruwa,” in ji wani bangare na sanarwar. A cewar rundunar sojoji, an gano gawarwakin Lance Corporal Femi da matarsa a cikin gidansu dake gini na 15, daki mai lamba 24, Corporals and Below Kuarters, a cikin sansanin. Binciken farko ya nuna cewa sojan yana kan aiki a lokacin kuma ya nemi izini daga babban jami’i domin ya kula da wasu harkokin kansa kafin ya dawo aiki. “Rundunar Sojin Nijeriya tana matukar bakin ciki kan wannan lamari,...
Kakakin ya kuma jaddada matukar adawa, da tanade-tanaden dokar, yana mai cewa, batun Taiwan shi ne jan layi na farko da ba za a iya tsallakewa ba a dangantakar Sin da Amurka. Daga nan sai ya yi kira ga Amurka, da ta mutunta cikakkiyar manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, da kuma sanarwa uku na hadin gwiwa da Sin da Amurka suka amincewa, ta yadda za ta cika alkawarin da ta dauka na kin goyon bayan duk wani yunkuri na neman ’yancin kan Taiwan, kana Amurka ta kaucewa mika sakwanni na kuskure ga ’yan aware masu rajin neman ’yancin kan yankin na Taiwan, ko shiga duk wata cudanyar ayyukan soji da yankin Taiwan na kasar...
Mataimakin firaministan kasar Sin, kana jagoran tawagar kasar mai tattauna batutuwan tattalin arziki da cinikayya da tsagin Amurka He Lifeng, ya zanta ta kafar bidiyo da sakataren baitul-malin Amurka Scott Bessent, da wakilin cinikayyar kasar Jamieson Greer a jiya Asabar. Yayin zantawar tasu, jami’an sassan biyu sun amince da gudanar da sabon zagayen tattaunawa game da batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayya nan ba da jimawa ba. Kazalika, sassan biyu sun yi musayar ra’ayoyi bisa sahihanci, da zurfafa tattaunawa, da musaya mai ma’ana dangane da yadda za a aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, yayin tattaunawarsu ta wayar tarho a farkon shekarar nan, da ma muhimman batutuwa masu nasaba da dangantakar tattalin arziki da cinikayya...
Majalisar Dattawa ta shiga tsakani don warware rikici tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), a wani yunkuri na kawo karshen yajin aikin gargadi na makonni biyu da malaman jami’ar ke yi. A sakamakon haka, kwamitocin Majalisar Dattawa kanKwadago da kuma Ilimi mai zurfi za su gana da Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, da Sakatare-Janar na hukumar Jami’o’i ta kasa (NUC), Farfesa Abdullahi Yusuf Ribadu, a ranar Talata mai zuwa. . A nasa jawabin kafin taron sirrin, shugaban ASUU na kasa, Farfesa Christopher Piwuna, ya ce bukatar kungiyar ita ce gwamnati ta inganta kudaden gudanar da jami’o’i kamar yadda aka amince a yarjejeniyoyin baya. Ya bayyana cewa zuba jari mai dorewa a fannin ilimi ne kadai zai kawo karshen...
Gwamna Radda ya jaddada cewa hukumomin tsaro kadai ba za su iya fada da ‘yan ta’adda ba, sai dai da gudummuwar ‘yan kasa. Ya yi kira ga ‘yan Nijeria da su zama masu sanya ido da kai rahotanni cikin gaggawa da bayar da ingantattun bayanai ga jami’an tsaro. Ya yaba wa gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu bisa inganta tsaro da maido da martabar tattalin arzikin kasar nan. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Yajin Aikin ASUU: Majalisar Dattawa Ta Tsoma Baki, Za Ta Gana Da Ministan Ilimi October 18, 2025 Labarai Fitar Da Kudi Ta Haramtacciyar Hanya Na Kara Dagula Matsalar Tattalin Arziki – IMF October 18, 2025 Labarai Majalisar Wakilai Ta Gayyaci CBN Da...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnatin Kano Ta Kai Ƙarar Ganduje Da Wasu Kotu Kan Zargin Almundahanar N4.4bn October 17, 2025 Manyan Labarai Dantawaye Ya Karɓi Ragamar Aiki A Matsayin Sabon Kwamishinan Ƴansandan Abuja October 17, 2025 Manyan Labarai Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura October 17, 2025
An gudanar da bikin bayar da lambar yabo ta wasan kwallon kafa na Asiya da Futsal na shekarar 2025 a birnin Riyadh na kasar Saudiyya. A bangaren mata kuwa, Marzieh Jafari, shugabar kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasar Iran, ita ce babbar mai horar da mata, yayin da Salar Aghapour ta lashe kyautar ‘yar wasa mafi nuna kwazo a wasan Futsal a wannan shekara. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran: Kudurin Kwamitin Tsaro Kan Yarjeniyar JCPOA Ya Kawo Karshe A Yau...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fidda bayani kan cewa daga yau Asabar 18 ga watan Octoban shekara ta 2025, kudurin kwamitin tsaro na MDD wanda aka samar don goyon bayan aiwatar da yarjeniyar Nukliyar kasar Iran wacce aka fi sani da JCPOA ya kawo karshe. Don haka daga yau shirin Nukliyar kasar Iran ta koma karkashen yarjeniyar NPT, kuma za’a yi mu’amala da shirin kamar sauran kasashen karkashin kula na hukumar IAEA. Tsahar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar na bada wannan sanarwan a safiyar Asabar ta kara da cewa dama kudurin na tsawon shekaru goma ne daga yau ta gama aiki. Daga yau shirin Nukliyar JMI zai ci gab aba tare da wani karin ka’idojin...
Tawagar sun gabatar da kansu ga babban sakataren hukumar gudanarwar ci gaban Jihar Katsina, Dakta Mustapha Shehu. Tawagar sun ce ziyarar wani bangare ne na shirye-shiryen gudanar da aikace-aikace domin inganta zaman lafiya da kuma sanar da tallafin jin kai ga ‘yan gudun hijira. Gwamnan Katsina ya yaba wa Bankin Duniya da ya yi hadin gwiwa da Jihar Katsina don fuskantar matsalolin tsaro da kuma tallafa wa ‘yan gudun hijira. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Hukumar Gidan Yarin Kano Ta Tabbatar Da Dauke Abduljabbar Zuwa Abuja October 17, 2025 Rahotonni Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya October 17, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Kano Ta Kai Ƙarar Ganduje Da Wasu...
Shugaban ya kara da cewa, aana sa ran aikin za a fara gudanar da shi ne, a zangon farko na shekarar 2026. Ya ci gaba da cewa, aikin na yiwa wadannan Tashoshin garanbawul, na daga cikin kudurorin Gwamnatin Tarayya na zamantar da Tashoshin Jiragen Ruwa na kasa, musamman ta hanyar samar da kayan aiki na zamia da kuma ci gaba da janyo hankalin masu son zuba hannun jari zuwa ga fannin, wanda hakan zai kuma kara sanya gasa a cikin wadanda suke a cikin fannin. Ya bayyana cewa, masu son zuba hannun jari a fannin suna ci gaba da nuna shawarsau, musamman saboda sauye-sauyen da Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinbu ta kirkiro da su, a fannin kara...
Shin menene makasudin shirya irin wannan taro na masu ruwa da tsaki akan sha’anin ilimi da aka gudanar a yau? Makasudin wannan taro shi ne a fadakar da mutane ayyukan wannan hukuma ta TETFUND da take yi, sannan kuma a yi magana da wadanda suka fi amfana da shi wannan tsari na TETFUND. Kamar jami’ai da makarantu da kuma dalibai sannan kuma a karbi shawarwari ga jama’a akan yadda za a bunkasa wannan aikin na hukumar tallafawa manyan makarantu na gaba da Sakandire a Nijeriya. Wannan shi ne makasudi kuma na farko da ake san a jawo al’umma a ciki su dan abinda ake yi da yadda ake kashe kudaden da kuma yadda ake tarawa da makasudin tara su...
Kwamandan Dakarun Sa Kai Na Iran Ya Bayyana Cewa: Iran A Yayin Yaki Da Isra’ila Ta Tarwatsa Wasu Muhimman Wurare 21
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar da tarwatsa wasu muhimman wurare 21 na ‘yan sahayoniyya a lokacin yakin 12 Kwamandan Dakarun sa-kai na Basij Birgediya Janar Gholamridha Sulaimani ya bayyana cewa: Tunanin kawar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a cikin yakin kwanaki 12 da aka yi, wauta ce ta makiya yahudawan sahayoniyya, wadanda suka gaza a yunkurin da suka yi. Ya jaddada cewa: Iran ta lalata muhimman wurare 21 na ‘yan sahayoniyya da makamanta masu linzami a yakin karshe. Birgediya Janar Gholamreza Soleimani ya bayyana a wurin taron tunawa da shahidai a Isfahan cewa: Makiya sun yi tunanin cewa za su iya kawar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran nan da kwanaki 10, kuma sun yi niyyar haifar da hargitsi da...
Rundunar ’Yan sandan Jihar Gombe ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka, inda ta gudanar da samame a wata maɓoya da ake zargi da aikata ayyukan ta’addanci da safarar ƙwayoyi a cikin jihar. A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar, ta bayyana cewa jami’an da ke ƙarƙashin Gombe Division ne suka gudanar da samamen da misalin ƙarfe 9:00 na dare a ranar Alhamis 10 ga Oktoba, 2025. Dantawaye ya zama sabon kwamishinan ’yan sandan Abuja Wani mutum ya ƙona tsohuwar budurwarsa a Oyo A cewar sanarwar, jami’an sun kai samamen wata maɓoya da ke bayan jerin shagunan Ƙaramar hukumar Gombe, (Local Government Shopping Complex), inda ake zargin...
Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, ta sanar da nadin CP Dantawaye Miller a matsayin sabon Kwamishinan ’Yan Sandan Abuja. Ya karɓi ragamar aikin ne a ranar Juma’a, 17 ga watan Oktoba, 2025, daga hannun CP Ajao Adewale, wanda Babban Sufeton ’Yan Sanda na Ƙasa, Kayode Egbetokun, ya sauya wa wajen aiki. Wani mutum ya ƙona tsohuwar budurwarsa a Oyo Ba mu ji dadin yi wa mahaifinmu afuwa tare da riƙaƙƙun masu laifi ba – Iyalan Herbert Macaulay A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar, sabon kwamishinan ya bayyana cewa zai ci gaba da inganta tsaro tare da bunkasa haɗin kai tsakanin ’yan sanda da al’ummar Abuja. Ta ce CP Miller ya yi alkawarin...
Dantsoho ya sanar da haka ne, bayan kaddamar dashi a matsayin Mataimakin Shugaban Kungiyar a kwanan baya a wani taro kan harkokin Tashoshin Jiragen Ruwa na duniya da aka gudanar. Kazalika, Dantsoho ya ci gaba da cewa, zai mayar da hankali ne, kan wanzar da tsarin da NPA, ta sanya a gaba da kara karfafa hadaka, musaman domin a habaka samar da sauki a fannin gudanar da hada-hadar Tashohin Jiragen Ruwa da ke a Afrika ta Yamma. Idan za a iya tunawa, harkar gudanar da Tashoshin Jiragen Ruwa na Afrika ta Yamma na fuskantar kalubale da suka hada da, yin aiki da kayan da suka dade da rashin samar da dawamammen tsari da kuma rashin rungumar yin aiki...
Abin da ya rage yanzu shi ne za a zuba ido don ganin irin sauyin da zai kawo na tsaro a birnin tarayyar, sakamakon taɓarɓarewar tsaro da ya addinin garin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura October 17, 2025 Manyan Labarai Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa October 16, 2025 Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC October 16, 2025
Majalisar koli ta sisaya ta kasar yamen ta sanar da nada major janaral Yousef hassan al-Madani a matsayin sabon babban hafsan hafsoshin sojin na kasar Yamen , inda ya gaji Janaral Mohammad Abdulkarim Al-Ghumari wanda yayi shahada a baya bayan nan sakamakon Harin da sojojin HKI suka kaddamar kan kasar ta yamen. Wannan sabon nadi ya kara tabbatar da karfin guiwa game da jagoranci tsakanin dakarun sojin kasar Yamen a dai dai lokacin da kasar ke ci gaba da gwagarmaya kan dakarun hadin guiwa da Saudiya ke jagoranta, kuma sun kara jaddada matsayarsu ta gwagwarmayar yanto dukkan yankunan dake karkashin yan mamaya ciki har da birnin Qudus, Janaral Ali Ghumari yana daya daga cikin mayan kwamandoji masu hazaka acikin dakarun...
Baya ga yi masu afuwa, Shuagaba Tinubu, ya kuma karama su da lambar yabo ta kasa. ‘Yan Ogonin su tara, sun dai fuskanci shari’a ne, bisa zarginsu da kitsa kisan sarakunan Ogoni Albert Badey, Edward Kobani, Theophilus Orage da kuma Samuel Orage. Kotu ta tuhumi ‘yan Ogonin su tara, ta kuma yanke masu hukuncin rataya a ranar 10 ga watan Numambar 1995. Hukucin na Kotun, a wancan lokacin, ya haifar da hatsaniya tare da yin suka daga bangaren manyan shugabannin kasasshen duniya, daidaikun mutane da sauran kungiyoyi, musaman duba da cewa, an yanke masu hukuncin ne, a lokacin da ‘yan kasar ke nuna tsanar mulkin soji, biyo bayan soke zaben shugaban kasa, da ake da yakinin an yi sahihin zabe...
Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa, taron goron gayyata ne na kafa Nijeriya a matsayin cibiyar samar da makamashi tare da sabuntawa a Afirka, sannan kuma sauyin da aka samu na makamashi Nijeriya, ya bayar da damar zuba jari na sama da dala biliyan 410, daga tsakanin yanzu zuwa shekarar 2060. Ya kara da cewa, “Daga cikin wannan, ana kuma bukatar sama da Naira biliyan 23, domin fadada hanyoyin samar da makamashin da kuma hada miliyoyin ‘yan Nijeriya, wadanda har yanzu suke rayuwa cikin matsalar wutar lantarki, amma yanzu babban burinmu shi ne, samar da tsarin samar da wutar lantarki mai karfin mega wat 277, nan da shekarar 2060. Cikar wannan buri, ya wuce batun zuba hannun jari kadai, domin...
Manyan malamai, shugabanni na addini, gargajiya da siyasa daga sassan Arewacin Najeriya sun hallara a Kaduna domin Taron Musamman na Malaman Arewa (Special Northern Ulamah Summit), wanda ya mayar da hankali kan nemo mafita ta dindindin ga matsalolin tsaro da ƙalubalen tattalin arziki da ke addabar yankin. Taron ya tattauna kan ƙarfafa haɗin kai tsakanin malamai, amfani da kafafen sada zumunta ta hanyar da ta dace, da kuma ƙarfafa hulɗa tsakanin shugabannin addini, gargajiya da na siyasa domin dawo da zaman lafiya da daidaito a al’umma. Da yake jawabi, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na Uku, wanda Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya wakilta, ya kira malamai da shugabanni su haɗa kai wajen...
A baya- bayan nan ‘yan ta’addan wadanda suka daura damarar hanawa al’umma kwanciyar hankali sun kashe daruruwan mutane, kona gidaje tare da garkuwa da mutane ciki har da mata da kananan yara. Rahotanni daga yankunan sun tabbatar da yadda al’umma suka gaji suka kosa da jin alkawura marasa adadi daga gwamnati wadda ke kasa cikawa a yayin da hare-hare ke karuwa a duk shekara duk da karin kudaden tsaro da ake warewa.. A Sakkwato, kauyuka da dama kamar Giyawa, Kurawa, da Unguwar Lalle a gabascin Sakkwato hedikwatar gawurtaccen dan ta’adda Bello Turji sun fuskanci hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama a baya- bayan nan. A Karamar Hukumar Sabon- Birni, wasu mazauna yankin sun tsere domin tsira da...
Tsohon ɗan majalisar wakilai daga jihar Bayelsa, Israel Sunny-Goli, ya shawarci tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan da ya guji duk wata matsin lambar da wasu ƴan siyasa ke yi masa na ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027. Sunny-Goli ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin halartar shirin Politics Today na tashar Channels, inda yake mayar da martani kan ficewar gwamnan Bayelsa, Douye Diri, daga jam’iyyar PDP. Ya ce, “Ina ganin Jonathan zai karɓi wannan lamari da zuciya ɗaya saboda mutum ne mai son cigaban jiharsa. Duk da maganganun da ake yi kan zai tsaya takara, bana ina ganin zai yi kuskuren hakan saboda lokaci ya riga ya wuce.” Maƙiyan Jonathan Ne Kaɗai Za Su Zuga Shi Ya...
Shugaban kasar ta Sudan Janar Abdulfattah al-Burhan ya ziyarci Masar inda ya gana da takwaransa Janar al-Sisi, inda su ka tattauna halin da ake ciki a Sudan, da kuma matsalolin da yankin yake fuskanta. Haka nan kuma bangarorin biyu sun yi musayar ra’ayi akan madatsar ruwan kasar Habasha da Masar take da sabani da Addis Ababa akai, da kuma yadda za a fuskanci wannan matsala. Kasar Sudan dai ta fada cikin yakin basasa ne tun a tsakiyar watan Aprilu na 2023 wanda ya zuwa yanzu ya ci rayuka da dama da kuma mayar da wasu miliyan 14 zama ‘yan hijira. Shugabannin biyu na kasashen Masar da Sudan sun kuma tattauna daukar mataki na bai daya akan madatsar ruwan na kasar...
A jiya Alhamis jiragen yakin HKI sun kai hare-hare na wuce gona da iri garuruwa mabanbanta na kudancin Lebanon da hakan ya yi sanadiyyar shahada da kuma jikkatar mutane da dama. Majiyar tsaro daga kudancin Lebanon ta ambaci cewa, mutum daya ya yi shahada yayin da wasu 7 su ka jikkata. Hare-haren sun shafi garin Kafar-Tabinet da kuma akan hanyar Kausariyyah al-siyadah. Haka nan kuma jiragen na ‘yan sahayoniya sun kai wasu hare-haren a garin Ansariyyah, da hakan ya yi sanadiyyar jikkatar mutane 6. Hare-haren na HKI suna a karkashin keta yarjejeniyar tsagaita wutar yaki. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label...
Jaridar Wall Street Jouranl ta kasar Amurka ta buga labarin da yake cewa, kasar Amurka ta fada girke makamai a kusa da tekun Caribbean da kuma wasu jiragen sama a arewacin kasar Venezuela. Labarin ya kara da cewa;Rundunar da ma’aikatar yakin Amurka ta “Pentagon” ta girke ta zaratan mayakan kundunbala ce wacce ta kashe Usama Bin Ladan a kasar Pakistan. Wani sashe na rundunar ya hada jirage masu Angulu da ake iya amfani da su wajen kai hari. A cikin kwanakin bayan nan dai Amurka ta kara matsin lamba akan kasar Venezuela ta hanyar kai wa jiragen ruwan da suke fitowa daga kasar hare-hare, bisa zargin cewa suna dauke da muggan kwayoyi zuwa Amurka. Gwamnatin Venezuela da kasashen yankin masu...
A yammacin jiya Alhamis ne sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya gana da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a birnin Moscow inda ya isar da sakon jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ga shugaban na Rasha. Bangarorin biyu sun tattauna batutuwa da dama da suka hada da huldar dake tsakanin kasashen biyu, da hadin gwiwar tattalin arziki, da ci gaban yankin, da kuma sauran batutuwa na kasa da kasa. A makon da ya gabata, Putin ya ce mahukuntan Isra’ila sun bukaci ya isar da sako ga Iran cewa ba su niyar sake kaddamar da wani hari a kan kasar ta Iran. “Muna ci gaba da samun sakonni daga jagorancin Isra’ila suna neman...
Aƙalla jami’an tsaro takwas, ciki har da ɗan sanda guda ɗaya da masu tsaron al’umma bakwai, sun rasa rayukansu a wani harin kwanton bauna da aka kai musu a hanyar Gusau–Funtua da ke Jihar Zamfara a ranar Alhamis. Lamarin ya faru ne a lokacin da gamayyar jami’an tsaro, waɗanda suka haɗa da ’yan sanda da mambobin rundunar tsaro ta jihar Zamfara ke amsa kiran gaggawa daga kauyen Tungawa da ke ƙaramar hukumar Tsafe. An ceto mutane 3 da aka yi garkuwa da kama wasu a Bauchi Majalisar Dattawa ta amince da Amupitan Shugaban INEC “Maganar da nake yanzu haka, an kwashe gawarwakin jami’an da suka mutu zuwa Gusau domin jana’iza,” in ji wani shaida da aka bayyana sunansa da Tsafe....
Ya ce kamar ko da yaushe, kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan muhimmiyar rawar da FAO ke takawa a bangaren aikin gona da samar da abinci a duniya. An kafa hukumar FAO ne a ranar 16 ga watan Oktoban shekara ta 1945, kuma Sin na daya daga cikin kasashe mambobi da suka kafa ta. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Wane Ci Gaba Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza Ta Haifar? October 16, 2025 Daga Birnin Sin Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin October 16, 2025 Daga Birnin Sin Masu Bincike Na Sin Sun Kera Wani Dan Karamin Mutum Mutumin Hannu Da...
An dage ci gaba da binciken har sai ranar 20 ga wata. Maris na shekara mai zuwa, a makon da ya gabata, dubban mutane ne suka yi jerin gwano a kan titunan birnin Manchester domin gudanar da jana’izar Hatton, wanda ya kasance shahararren dan wasan dambe a kasar Ingila. Dan wasan gaban Oasis Liam Gallagher, tsohon dan wasan Ingila da Manchester United Wayne Rooney da kuma tsohon zakaran ajin masu nauyi na duniya Tyson Fury na daga cikin taurarin duniya na wasanni da suka halarci jana’izar Hatton. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Da Ɗumi-ɗumi: Ladan Bosso Ya Ajiye Aikin Horar Da Barau Fc October 15, 2025 Wasanni Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Benin A Uyo October 14,...
Sashen kashe radadi domin gudanar da aikin tiyata ga marasa lafia na asibitin gwamnatin tarayya FMC da ke garin Birnin Kudu a jihar Jigawa ya gudanar da bikin ranar bada maganin radadi ta duniya ta bana. Kungiyar ma’aikatan bada maganin kashe radadi dan yin aikin tiyata ta Duniya ce ta kebe ranar 16 ga wata Oktobar kowacce shekara domin bikin wannan rana. Shekaru 170 ke nan da fara amfani da maganin kashe radadi, inda wasu likitoci su ka yi gwajin wannan magani a asibitin birnin Massachusetts na kasar Amurka, abin da ya kawo sauyi wajen yi wa marasa Lafia aikin tiyata daga shekara 1846. Malam Aliyu Umar Yusuf na sashen bada maganin kashe radadi na asibitin gwamnatin tarayya FMC...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya amsa wasika daga daukacin malamai da daliban jami’ar nazarin aikin gona ta kasar Sin, inda ya taya dukkan malamai da dalibai da ma’aikatan jami’ar, da kuma wadanda suka kammala karatu a jami’ar murnar cika shekaru 120 da kafuwar jami’ar. Xi ya yi fatan jami’ar za ta ci gaba da tafiyar da harkokinta yadda ya kamata, da kudurce aniyar inganta aikin gona don amfanin kasa, da kuma zurfafa yin gyare-gyare kan hanyoyin koyarwa da ilmantarwa, da kara kokarin bincike, da kirkire-kirkire a fannin aikin gona, da kuma amfani da sakamakon binciken yadda ya kamata, ta yadda za a kai ga horar da karin kwararrun masana a fannin aikin gona, don ba da sabuwar gudummawa ga...
Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa a koda yaushe makiya suna neman haifar da rikici tsakanin kasashen musulmi domin raunana su, yana mai nuni da barkewar tashin hankali tsakanin Pakistan da Afghanistan. Mr. Pezeshkian ya bayyana haka ne a yayin wani taro inda ya fayyace matsayin kasar Iran dangane da takun saka tsakanin kasashen musulmi a gabashin kasar Iran. Shugaban ya kara da cewa rikicin baya-bayan nan tsakanin Afghanistan da Pakistan ya haifar da damuwa sosai a tsakanin dukkanin kasashen yankin ciki har da Iran da ke da iyaka da kasashen biyu. Ya kara da cewa, Iran za ta yi iyakacin kokarinta na ganin an rage zaman dar-dar, da inganta tattaunawa, da karfafa dankon zumunci a tsakanin...
“Muna roƙon Allah (T) Ya kawo mana ƙarshen wannan matsala ta tsaro a duk faɗin Jihar Zamfara, Arewa da ma Nijeriya baki ɗaya.” Lamarin ya jawo damuwa daga al’umma da shugabannin siyasa, yayin da hukumomin tsaro ke ƙara ƙoƙari wajen gano waɗanda suka aikata wannan mummunan laifi da tabbatar da zaman lafiya a yankin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC October 16, 2025 Labarai Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zaman Kurkuku October 16, 2025 Manyan Labarai Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 16, 2025
Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi
Haka kuma, shugabar kasar Iceland Halla Tomasdottir ta ce, a matsayin wata babbar kasa, kiran da kasar Sin ta yi yana da muhimmanci ga sauran kasashen duniya. Ayyukan da kasar Sin ta yi a fannin tabbatar da ci gaban mata da daidaiton jinsi, sun kasance abin koyi ga kasashen duniya. Bugu da kari, shugabar kasar Dominica Sylvanie Burton, ta ce jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi a yayin taron kolin mata na duniya, ya samar da sabon karfi ga raya ci gaban mata bisa dukkan fannoni, kuma kasarta na fatan ci gaba da yin hadin gwiwa da kasar Sin a fannoni da dama. (Mai Fassara: Maryam Yang) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Ɗaga...
Hichilema ya kuma jinjinawa kamfanonin Sin, bisa yadda suke inganta darajar albarkatun dake kasarsa ta hanyoyin zuba jari, kana ya godewa Sin bisa yadda ta bude kasuwanninta ga Zambia da ma sauran sassan nahiyar Afirka baki daya. (Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sashen Cinikayyar Kamfanonin Sarrafa Hajoji Na Sin Ya Bunkasa Da Kaso 4.7 Bisa Dari Cikin Watanni Tara Na Farkon Shekarar Nan October 15, 2025 Daga Birnin Sin Nazarin CGTN: Jamaar Duniya Sun Yi Ammana Amurka Za Ta Fi Jin Jiki Daga Yakin Haraji October 15, 2025 Daga Birnin Sin Shugaban Zaunannen Kwamitin Majalisar Wakilan Jama’ar Sin Ya Gana Da Mukaddashin Shugaban Majalisar Dattawan Kasar Liberia October 15, 2025
An fara tantancewar da misalin ƙarfe 12:55 na rana, inda ake sa ran Farfesa Amupitan zai gabatar da tarihinsa da kuma amsa tambayoyin da ‘yan majalisar za su yi masa, kafin yanke shawara kan tabbatar da shi a matsayin sabon shugaban INEC. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 16, 2025 Manyan Labarai Baba-Ahmed Ya Zargi El-Rufai Da APC Kan Haifar Da Rashin Tsaro Don Neman Mulki October 16, 2025 Manyan Labarai An Kashe Mutum 13 A Wasu Sabbin Hare-Hare A Ƙauyukan Filato October 16, 2025
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson October 16, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP October 15, 2025 Manyan Labarai 2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa October 15, 2025
Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta kama gungun mutane 11 da ake zargi da kasancewa ’yan fashi da makami da ke addabar matafiya a kan hanyar Katsina zuwa Kano. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Abubakar Aliyu, ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba a Katsina cewa waɗanda ake zargin sun kware wajen tare hanyoyin zuwa Sha’iskawa-Charanchi da Katsina-Kankia-Kano, suna kwace dukiyoyin matafiya. DSS ta cafke tsoffin jami’anta 2 kan aikata zamba Kotu ta daure kocin kwallon kafa a Kano shekara 8 saboda aikata luwadi Ya bayyana sunayen waɗanda aka kama da suka haɗa da Dikko Ma’aru, Dardau Kabir, Muntari Musa, Labaran Amadu, Usman Ma’aru, Lawal Zubairu, Nasiru Sanusi, da Adamu Kabir. Sauran sun haɗa da Abdullahi Zubairu, Muhammad...
Ma’aikatar masana’antu da ma’adinai ta kasar Iran ta bayyana cewa na sami karin ci gaba a yawan karfen da kasar ke sayarwa ga kasashen waje a rabin farko na wannan shekara ta 2025 zuwa dalar Amurka billion $4. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa duk tare da takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma suka dorawa kasar ta bunkasa amfani da karfe ko a cikin gida sannan da wasu dabarbarun don saida su ga kasashen duniya. Labarin ya kara da cewa yawan karshen da ake samarwa a cikin gida ya karo da kasha 34% a cikin watanni 6 da suka gabata na wannan shekara ta 2025, sannan yawan karfen da iran take satarwa zuwa kasashen wajen ya...
Majiyar hukumar fursinoni ta Falasdinawa ta bada sanarwan cewa masu gida a gidajen yarin HKI sun daki Marwan Barghouti a cikin makon da ya gabata har ya suma, kuma sun karya masa awaza har guda 4 sanadiyyar haka. Jaridar ‘The National’ ta kasar Amurka bayyana cewa Barghouti yana daga cikin shuwagabannin Falasdinawan da Hamas ta bukaci a sakeshi a musayar fursononi na baya bayan nan. Dansa Arab Barghouti ya ce ya samu labarin irin halin da mahaifinsa yake ciki a hannun HKI daga bakin falasdinawa guda 5 da aka saka sannan aka koresu zuwa kasar Masar. Barghouti dan shekara 66 a duniya ya fara gwagwarmaya da HKI tun yana dan shekara 15 a duniya. A shekara 1987 yahudawa sun koreshi...
Baba-Ahmed, ya bayyana cewa, abin da danginsa suka fuskanta a hannun masu garkuwa da mutane a bara ya tabbatar masa da cewa rashin tsaro a yanzu yana da nasaba da siyasa. Ya kuma danganta kisan jama’ar da aka yi wa mabiya Shi’a a Zariya a shekarar 2015 da wani shiri na gwamnati don murƙushe masu sukarsu a wancan lokaci. Ya jaddada cewa El-Rufai da jam’iyyar APC ba za su iya tserewa daga alhakin halin da Nijeriya ke ciki na rashin tsaro ba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Kashe Mutum 13 A Wasu Sabbin Hare-Hare A Ƙauyukan Filato October 16, 2025 Manyan Labarai Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson October...
Ministan Harkokin Cikin Gida Ya Yi Watsi Da Shelanta Samun Nasara Da Dantakara Isa Bakari Ya Yi Ministan harkokin cikin gidan kasar Kamaru Paul Atanga Nji ya yi watsi da yadda dan takarar shugabancin kasar Isa Tchiroma Bakari ya shelanta kansa a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa, ya kuma yi kira ga shugaban kasar Paul Biya da ya amince da shan kaye. Ministan harkokin cikin gidan na kasar Kamaru ya zargi Issa Bakari da cewa yana da wani shiri na kokarin kona kasar Kamaru ta hanyar taimakon kasashen waje. A makon da ya shude ma dai Atanga Nji ya yi gargadi kar wanda ya fitar da sakamakon zaben, domin yin hakan zai zama daidai da cin amanar kasa....
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Sanata Ahmed Wadada Aliyu murnar zagayowar ranar haihuwarsa, inda ya bayyana shi a matsayin ma’aikaci mai tawali’u, mai aminci, kuma mai kishin kasa wanda irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban kasa abin a yaba ne. Shugaban ya yaba wa Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Yamma kuma shugaban kwamitin majalisar dattijai kan asusun gwamnati bisa “kishin sa na gaskiya, rikon amana, tsarin kasafin kudi, da dokoki masu tasiri da ke magana kan makomar kasarmu.” Da yake karin haske kan tarihin Sanata Wadada a Majalisar Dokoki ta kasa, Shugaba Tinubu ya lura cewa “a cikin shekaru biyu kacal a Majalisar Dattawa, kun bambanta kanku a cikin doka, wakilci, da kuma kulawa...
Sashen Cinikayyar Kamfanonin Sarrafa Hajoji Na Sin Ya Bunkasa Da Kaso 4.7 Bisa Dari Cikin Watanni Tara Na Farkon Shekarar Nan
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Nazarin CGTN: Jamaar Duniya Sun Yi Ammana Amurka Za Ta Fi Jin Jiki Daga Yakin Haraji October 15, 2025 Daga Birnin Sin Shugaban Zaunannen Kwamitin Majalisar Wakilan Jama’ar Sin Ya Gana Da Mukaddashin Shugaban Majalisar Dattawan Kasar Liberia October 15, 2025 Daga Birnin Sin An Bude Bikin Baje Kolin Kasuwanci Na Kasa Da Kasa Na 138 A Guangzhou October 15, 2025
A yayin shari’ar, wanda ake tuhumar ya musanta zargin, sai dai kotun ta ce masu gabatar da kara sun gabatar da shaida wadda ta gamsar da ita ba tare da wata shakka ba. Mai shari’a Dahiru ya ce laifin ya ci karo da sashe na 284 na kundin laifuffuka, wanda ya haramta yin jima’i ba bisa ka’ida ba, don haka ya yanke wa Hayatu Muhammad hukuncin daurin shekaru hudu a kan kowanne daga cikin tuhumomin biyu, wanda zai fara ne tun ranar da aka kama shi. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Sojoji Sun Yi Juyin Mulki A Ƙasar Madagascar October 15, 2025 Labarai Gwamnan Kaduna Ya Taya Al’Amin Murnar Nasarar Lashe Gasar Ƙirƙirar Fasaha Ta Duniya A Ƙasar...
Shugaban Zaunannen Kwamitin Majalisar Wakilan Jama’ar Sin Ya Gana Da Mukaddashin Shugaban Majalisar Dattawan Kasar Liberia
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Bude Bikin Baje Kolin Kasuwanci Na Kasa Da Kasa Na 138 A Guangzhou October 15, 2025 Daga Birnin Sin Mujallar “Qiushi” Za Ta Wallafa Muhimmiyar Kasidar Shugaba Xi Jinping Kan Muhimman Shawarwari Hudu Da Ya Gabatar October 15, 2025 Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Taya Patrick Herminie Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Seychelles October 15, 2025
Gwamnan Kaduna Ya Taya Al’Amin Murnar Nasarar Lashe Gasar Ƙirƙirar Fasaha Ta Duniya A Ƙasar Birtaniya
An tallafawa ‘yan Kasuwa ƙanana, kuma an rage fitar da hayakin da ke gurɓata muhalli a faɗin nahiyar Afirka. Gwamna Uba Sani ya bayyana wannan nasara a matsayin babbar gagarumar bajinta da kuma abin alfahari ga Jihar Kaduna da NIjeriya baki ɗaya, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da zuba jari a fannin kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire domin bunƙasa tattalin arziki da bai wa matasa dama. “Wannan nasara ta sake tabbatar da ƙwarewar ƙirƙira da ƙarfin tunanin matasan Jihar Kaduna. Muna gina tattalin arzikin da ke dogaro da kirkira wanda ke daraja ra’ayi tare da haɓaka baiwa” in ji Gwamna Uba Sani. “Daga ajujuwa zuwa manyan matakan duniya, matasan Kaduna suna jagorantar makomar...
Rahotanni sun bayyana cewa rikici na kara Kamari tsakanin kasashen Pakistan da kuma Afghanistan inda dakarun sojin kasar Pakistan suka sanar da cewa sun tarwatsa tankokin yakin kasar Afghanistan guda 6 kuma an samu mummunar asara a cikin dakarunta a arangama da aka yi a yankin Kurram. Bayan tsagaita wuta na dan wani lokaci fadan ya sake rikicewa tsakanin dakarun sojin Pakistan da na mayakan Taliban, inda Islam abad ta zargi Kabul da bada mafaka ga kungiyoyin yan ta’adda dake kawo rashin zaman lafiya a yanki, arangamar da akayi a baya bayan nan ta nun irin tashin hankali da ake ciki a iyakokin kasashen biyu Kakakin sojin kasar Pakistan ya bayyana cewa dakarun kungiyar Taliban sun kaddamar da hari kan...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abass Araqchi ya bayyana yadda wasu kasashen turai 3 suka yi amfani da yarjejeniyar JCPOA da kuma kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya wajen mayar da kudurin kwamitin da aka soke shi a baya kan kasar iran, wanda ya fuskanci adawa daga kasashe da dama ciki har da mambobin biyu na dindindin a kwamitin sulhu a matsayin dokar da ta sabama doka kuma ba za ta yi tasiri a shari’a ba. Kasashen turai saboda matsin lambar Amurka ta fice daga yarjejeniyar JCPOA don haka wadannan kasashe basu da hurumin da za su ce wani abu kan jarjejeniyar, tun da saboda su ne da Amurka dukkan yarjejeniyar ta wargaje Minista Araqchi ya bayyana cewa batun yankin...
Kwamandan rundunar ta 6, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya yabawa sojojin bisa nuna kwarewa da juriya, inda ya bukace su da su ci gaba da sharar daji har sai an kakkaɓe duk wasu masu aikata laifuka gaba daya a jihar Taraba. Ya bayyana ci gaba da jajircewar rundunar sojin Nijeriya wajen tabbatar da tsaro da tsaron duk ‘yan kasa masu bin doka da oda, yana mai ba da tabbacin cewa, sojojin za su ci gaba da hada kai da sauran hukumomin tsaro da al’ummomin yankin domin samun dawwamammen zaman lafiya a jihar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Yajin Aikin: Ɗalibai Sun Bai Wa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana 7 Su Warware Rikicinsu October 15, 2025 Manyan...
Bugu da kari, shugaba Xi ya ce a shirye yake ya hada hannu da Patrick Herminie wajen aiwatar da sakamakon taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika na FOCAC a matsayin wata dama ta ci gaba da daukaka dangantakar kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare zuwa manyan matakai da kara kyautatawa jama’arsu. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya October 14, 2025 Daga Birnin Sin Uwar Gidan Shugaban Sin Ta Ziyarci Wajen Nune-nunen Karfafawa Mata Gwiwa A Bangaren Fasahohin Zamani October 14, 2025 Daga Birnin Sin Sin Tana Adawa Da Matakan Kuntatawa Na Amurka Kan Bangarorin Kasar Da Suka...
Ministan Yada Labarai Mohammed Idris, ya bayyana Jihar Borno a matsayin jiha mafi juriya a Najeriya, yana jaddada gagarumar nasararta wajen shawo kan ƙalubale da dama tsawon shekaru. Yayin wata ziyarar ban-girma da ya kai wa Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Alhaji Umar Isa Kadafur, a Maiduguri, Ministan ya yaba wa mutanen jihar bisa jajircewarsu da himmarsu wajen fuskantar matsaloli. Wannan ziyara na daga cikin shirye-shiryen taron Kwamitin Kwamishinonin Yada Labarai na jam’iyyar APC. Ya bayyana cewa abubuwan da suka faru a Borno cikin shekaru goma da suka wuce sun nuna jarumtaka da haƙurin mutanen jihar, waɗanda ke ci gaba da ginawa da tafiya gaba duk da matsalolin da suka fuskanta. Ministan ya jaddada cewa ƙarfin gwiwar mutanen Borno abin alfahari...
’Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya tare da sace dabbobi da dama a wasu ƙauyuka da ke Ƙaramar Hukumar Kankia a Jihar Katsina. Lamarin ya faru ne a daren ranar Litinin, inda aka kashe wani mazaunin ƙauyen Kwadawa da ke yankin Gachi, yayin da wani kuma ya jikkata. Gwamnan Bayelsa ya fice daga jam’iyyar PDP Kotu ta umarci a tono gawarwakin wadanda gobara ta kashe a Legas don yin bincike Shaidu sun ce kimanin ’yan bindiga 100 ne suka kai harin, inda suka kuma mamaye ƙauyen Bogga; ƙauyen Fulani da ke kan hanyar Kankia zuwa Ingawa. Sakamakon haka, mazauna ƙauyukan Bogga, Taiba Badole, Arahiya Kwandawa, Rumawa, Gangara da Rugar Bindo duk da ke yankunan Gachi da Fakuwa/Kafindangi, sun tsere daga...
Kwamatin harkokin lafiya na majalisar dokokin jihar Jigawa ya ce gyaran fuskar da aka yiwa dokar da ta kafa asusun adashen gata na kiwon lafiya na jihar ya sahalewa asusun damar samo kudade daga wasu bangarori da ba na gwamnati ba. Shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Guri, Alhaji Usman Abdullahi Tura Musari, ya yi wannan tsokaci lokacin da ya jagoranci ‘yan kwamatin domin ziyarar aiki a ofishin asusun da ke Dutse. Ya bayyana bukatar ganin asusun JICHIMA ya nemo kudade daga hannun masu taimakon al’umma da cibiyoyi da ‘yan siyasa da kwamitocin zakka da na waqafi domin bunkasa asusun, ta yadda zai biya bukatun kiwon lafiyar al’ummar jihar. Alhaji Usman Musari ya lura cewar fadada hanyoyin samun kudade ga...
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fadawa kungiyar Hamas su mika makamansu da radin kansu ko kuma zai kwance damararsu da karfi. Jaridar Daily Mails ta kasar Burtaniya ta nakalto shugaban yana fadarwa kafafen yada labarai a washinton a jiya Talata. Amma kungiyar Jihadul Islami daya daga cikin kungiyoyin da ke dauke da makamai a zirin gaza ta bakin mataimakin babban sakataren kungiyar Mohammad Al-Hindi a hirar da yayi da tashar talabijan ta Aljazeerah cewa kungiyoyi masu gwagwarmaya a gaza basu amince su mika makamansu a yarjeniyar sulhu na Trump ba kuma basu damu da barazanar shugaba Trump na kwance damarasu da karfi ba. Alhindi ya kara da cewa banda haka babu wata kalma ko guda a cikin yarjeniyar da...
Wani babban jami’in kungiyar Hamas a gaza ya bayyana cewa HKI tana dakile kokarinda kungiyar take na nemo da kuma mayar da gawakin yahudawan Sahyoniya da suka halaka saboda barin wutan da sojojin ta suka yi kan gaza, wanda ya kai ga mutuwar jami’ansu da suka bawa aikin kula da yahudawan. Don haka wannan ya sa suka rasa samun wadan nan jami’insu saboda sun mutu, sun kuma mutu tare da yahudawan da suke hannunsu. Kungiyar Hamas bata san a dai dai inda suke ba a lokacinda aka kashe su, don haka akwai bukatar lokaci kafin su gano wadannan mutane. Wasunsu sun karkashin burmudhin gine-gine a gaza wanda yake bukatar kwacesu kafin a kai ga gawakinsu. Don haka lai gwamnatin yahudawanne...
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya kungiyar kwallon kafa ta kasaSuper Eagles murnar nasarar da suka samu ta ci 4 da nema a kan Cheetahs ta Jamhuriyar Benin, tare da yabawa ƙungiyar bisa ƙoƙarin da take yi na ci gaba da kokarin cika al’umma, yayin da suke neman cancantar zuwa gasar cin Kofin Duniya ta FIFA a shekarar 2026. Shugaban ƙasar ya jinjina wa Super Eagles bisa ƙwazo, da jajircewar da suka nuna a filin wasa na Uyo, yana mai cewa wannan gagarumar nasarar ta sake karfafa ‘yan Najeriya kan harkar ƙwallon ƙafa. “Yanayin farin ciki da ake ciki a fadin ƙasar nan na nuni da yakinin da muke da shi cewa Najeriya ta cancanci samun gurbi a gasar...
Yansanda a kasar Italia sun kara da masu zanga zanga masu kuma goyon bayan Falasdinawa, don hana a gudanar da wasan kwallon kafa tsakanin kungiyar kwallon kafa ta HKI da kuma ta kasar Italia a filin wasa na Udine a jiya Talata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa gwamnatin kasar Italia ta aika yansanda fiye da 1000 guda, tare da jiragen sama masu saukar ungulu don hana masu zanga –zangar isa filin wasan. Labarin ya kara da cewa zanga-zangar wacce kwamitin masu goyon Falasdinawa ya shirya. Zanga-zangar don hana wasan ta ilimunation wato fidda goni na masuhalattar gasar duniya ta FIF 2026. Daga karshe dai an yi gasar kuma kasar Italiya ta lallasa HKI da 3-0....
Ya kuma roƙi shugabannin ƙasashen Yammacin Afirka su haɗe kai wajen yaƙi da ƙungiyoyi masu amfani da ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, inda ya bayyana cewa irin waɗannan ayyuka suna ƙara haifar da tashin hankali da talauci. Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, shi ma ya yi kira ga ƙasashen yankin su amince da yarjejeniyar ECOWAS kan cin hanci, domin hana masu rashawa samun wajen ɓuya. “Mu tabbatar babu inda ɓarayi za su ɓuya. Duk wanda yake tayar da hankali a ƙasashenmu bai kamata ya samu natsuwa ba,” in ji Fagbemi. Ƙungiyar NACIWA ƙungiya ce ta hukumomin yaƙi da cin hanci daga ƙasashen ECOWAS, wadda ke aiki tare wajen yaƙi da rashawa. Shugaban ƙungiyar na yanzu shi ne Ola Olukoyede, wanda kuma...
Kasar Iran ta yi Allah wadai da kalaman kin jinin Iran da Trump ya yi a majalisar dokokin Isra’ila ta Knesset Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fitar da sanarwa inda ta yi Allah wadai da zarge-zarge marasa tushe da kuma da’awar rashin gaskiya da rashin kunya da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi kan Iran, wanda ya yi a ranar Litinin a zauren majalisar dokokin yahudawan sahayoniya a gaban masu aikata laifukan kisan kare dangi. A cewar wani rahoto da ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar a jiya Talata, sanarwar ta ce: Amurka a matsayinta na kasar da ta fi kowacce kasa samar da ayyukan ta’addanci a duniya, kuma mai goyon bayan gwamnatin sahayoniyya ‘yan...
A Lokacin Yaki, Iran Ta Tarwatsa Wata Cibiyar Leken Asirin Yahudawan Sahayoniyya Da Ke Yankin Farar Hula
Iran ta kai hari a wani sansanin sojan Isra’ila na sirri da ke karkashin wata hasumiya a Tel Aviv Yankin Gray, wani dandali ne na bincike, ya bayyana samuwar wani maboyar sirri na sojan Isra’ila da ke karkashin wani hasumiya a Tel Aviv, wanda ake kyautata zaton yana cikin wadanda aka kaiwa hari da makami mai linzami na Iran yayin harin da aka kai ranar 13 ga watan Yuni. Bisa binciken da aka gudanar, dandalin ya gano wurin da wani wurin karkashin kasa da aka fi sani da “Site 81”, wani rukunin jami’an leken asiri na hadin gwiwar sojojin Amurka da Isra’ila da ke karkashin rukunin gidaje na Da Vinci a wata unguwa mai yawan jama’a a tsakiyar birnin Tel...
Shugaban Kasar Columbia Ya Soki Donald Trump Akan Bai Wa Isra’ila Makamai Shugaban na kasar Columbia Gustavo Petro ya ce, Bugun kirjin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na bai wa “Isra’ila” makamai tare da cewa ta yi amfani da su da kyau, ba wani abu ne da ya cancanci a yi masa tafi, sunan shi tarayya a aikata laifi. Shugaba Gustavo Petro yana mayar da martani ne akan zancen da shugaban kasar Amurka ya yi a Majalisar “Knesset’ ta Haramtacciyar Kasar Isra’ila ya ce; Isra’ilan ta yi amfani da makaman da ya ba ta da kyau. Shugaba Gustavo ya kara da cewa; wadannan makaman na Amurka sun kashe mutane 70,000 sannan kuma sun jikkata wasu 200,000....
Kungiyar Jihadul-Islami Ta Falasdinu Ta Ce; ‘Yantar Da Fursunonin Falasdinawa Abu Ne Mai Muhaimmanci
Babban sakataren kungiyar Jihadul-Islami ta Falasdinu ya jaddada cewa: ‘Yantar da sauran fursunonin manufa ce da ba za ta fice daga muhimman abubuwan da suka aka sa a gaba ba Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Jihadul- Islami ta Falasdinu, Ziyad al-Nakhalah, ya tabbatar da cewa: Ba za a taba mantawa da manufar ‘yantar da sauran jajirtattun fursunonin Falasdinu daga gidajen yarin ‘yan mamayar yahudawan sahayoniyya ba saboda yana daga cikin muhimman abubuwan da ‘yan gwagwarmaya suka sa a gaba. Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Palestine Today cewa: Kwamandan al-Nakhalah ya jaddada a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar litinin cewa: Tutocin gwagwarmaya suna ci gaba da wanzuwa a kasa...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yadda ‘ya’yan jamiyyar PDP ke ficewa suna komawa jam’iyya mai mulki na cigaba da nuna yadda take kara samun koma baya a siyasar Najeriya. Banda haka, rikicin cikin gida da yaki ci yaki cinyewa na cigaba da yi mata dabaibayi. Shin ko hakan na nufin jam’iyyar ta fara gushewa ne a siyasar Najeriya? NAJERIYA A YAU: Shin Babu Wata Hanyar Magance Matsalolin ASUU Ne Sai Yajin Aiki? DAGA LARABA: Yadda Aka Yi Almajiri Ya Zama Mabaraci Wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
Sojoji sun kama wata mata da mijinta da suka yi kaurin suna wajen safarar makamai a yankin Saminaka da ke Karamar Hukumar Lere ta Jihar Kaduna. Dubun ma’auratan ta cika ne a wani shingen binciken inda sojojin Rundunar Operation Fansan Yamma suka gano harsasai 1,207 hannunsu. Kakakin rundunar, Manjo Samson Zhakom ya ce an kama su ne a hanyars ta kai wa ’yan ta’addan da ke addabar yankin Arewa maso Yamma makaman. Ya ce matar mai shekaru 18 mijin masi shekaru 40 suna tsare suna amsa tambayoyi, yana mai jinjina wa sojoji da ’yan banga bisa kwarewar da suka nuna wajen kama miyagun. Kofin Duniya: Da sauran rina a kaba duk da Najeriya ta ci Jamhuriyar Benin 4-0 Na yafe...
Dandazon ’yan bindiga sun kai hari a yankin Kankia da ke Jihar Katsina inda suka halaka mutum daya tare da jikkata wasu da dama. Shaidu sun ce ’yan bindiga kimanin 100 a kan babura ne suka kai harin a yankin Kwadawa da ke Gundumar Gashi da ke Karamar Hukumar Kankia, inda ake Ana zargin maharan sun kai harin daukar fansa ne, Maharan da suka kai farmaki a yankin da ke Gabahsin karamar hukumar, sun sace dabbobi da ba a san adadinsu ba, suna masu barazanar halaka duk mutanen yankin. Wakilinmu ya ruwaito cewa a halin yanzu mazauna yankunan Bogga, Taiba Badole, Arahiya, Kwandawa, Rumawa, Gangara da Rugar Bindo da ke gundumar Gachi da kuma Fakuwa/Kafindangi suna yin kaura domin tsira...
Al’ummun Kasashe Daban-Daban Sun Yabawa Shawarwarin Sin Dake Taimakawa Wajen Dunkulewa Don Hanzarta Ci Gaban Mata
Ta ce shawarwari hudu da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar, duk suna kira ne da a yi hadin gwiwa don tabbatar da daidaiton jinsi, ya zama bai daya cikin manyan batutuwa da ya dace a tattauna a duniya. Ana bukatar karin ayyuka, kuma ba shakka wannan taro yana da matukar muhimmanci. A nata bangare kuwa, wakiliyar kasar Tanzaniya Juliana Kibonde, cewa ta yi, an saurari jawabin shugaba Xi Jinping, wanda ke da matukar muhimmanci ga kasashen Afirka. An kuma lura da yadda za a ba mata ikon ci gaba a fannoni kamar na fasaha, da siyasa da sauyin yanayi. Kazalika, shugaba Xi ya ambaci batun gibin dijital, kuma ana iya fahimtar cewa, wasu kasashe suna...
’Yan Majalisar Tarayya uku daga Jihar Kaduna sun sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC. Shugaban Majalisar Wakilai Abbas Tajuddeen ya sanar a ranar Talata cewa masu sauya shekar sun hada da Honorabul Abdulkarim Hussain Mohammed, Aliyu Mustapha Abdullahi da kuma Sadiq Ango Abdullahi. Tajuddeen, wanda shi ma dan asalin Jihar Kaduna ne, ya sanar da cewa, Gwamnan jihar, Uba Sani ya halarci zaman majalisar domin shaida dawowar ’yan majalisar zuwa APC daga PDP. Masu sauya shekar sun bayyana cewa rikin cikin gida da rabuwar kai da suka dabaibaye tsohuwar jam’iyyarsu ta PDP ce ta sa suka yanke shawarar sauya sheka. Shugaban Hukumar Zaɓen Yobe Jihar Yobe ya rasu Faɗa ya ɓarke tsakanin Palasɗinawa da Hamas bayan sulhu da Isra’ila...