2025-10-13@22:48:23 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3569
«Ammar dan Yasir»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Babban magatakardar malajisar koli ta tsaron kasar Iran Dr. Ali Larijani ya bayyana cewa; Batun sake kakabawa Iran takunkumi yana nuni da gajiyawar kasashen turai. Dr. Ali Larijani wanda tashar talabijin din al’mayadin’ta yi hira da shi, ya kara da cewa, matakin da kasashe uku na Faransa, Birtaniya da Jamus, su ka dauka akan batun sake kakabawa Iran takunkumi, yana sake yin nuni ne da tsohuwar gabar da kasashen turai da Amurka suke da ita akan al’ummar Iran. Haka nan kuma ya ce wannan tsohuwar gaba ta yi tasiri mai girma a cikin siyasar mulkin mallaka ta kasashen turai da yadda suke son Dannen sauran kasashe. Dr. Ali Larijani ya kuma ce, wanann irin kiyayya da siyasa tana cin karo...
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima a ranar Laraba zai gabatar da jawabin Najeriya a taron Babban Zauren Majalisar Dinkin duniya (UNGA) karo na 80 da ke gudana a birnin New York na Amurka. Zai yi jawabin ne a madadin Shugaban Kasa Bola Tinubu tsakanin karfe 3:00 na yamma zuwa 9:00 na dare agogon birnin New York. Mun ci ribar Naira biliyan 601 a watanni shidan farkon 2025 – Bankin GT Dalilin da muke goyon bayan Tinubu kan karɓo bashi — Majalisar Wakilai Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa ana sa ran Najeriya za ta bayyana sabbin kudurorinta na kasa (NDCs) da aka sabunta a karkashin yarjejeniyar Paris yayin wannan jawabi. A baya, Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima,...
Rundunar sojojin ta ce waɗannan hare-hare sun nuna ƙudirin gwamnati wajen yaƙi da rashin tsaro a faɗin ƙasar nan. Ta kuma tabbatar wa ‘yan ƙasa cewa za ta ci gaba da ƙoƙari domin kare al’umma daga ‘yan ta’adda da sauran masu laifi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk da amfanin kifi ga lafiyar jikin mutum da kuma samar da kudin shiga masana sun ce ba a amfani da shi yadda ya kamata a Najeriya. Baya ga bai wa jiki lafiya, kifi ka iya samar da kudaden shiga ga daidaikun ’yan Najeriya da ma kasar gaba daya. NAJERIYA A YAU: Abin Da Doka Ya Ce Kan Kisan Jami’an ‘Yan Sanda DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa ’yan Najeriya basa samun cin kifi kamar yadda ya kamata. Domin sauke shirin, latsa nan
A yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci hada karfi da karfe wajen gina yankin Xinjiang ya zama mafi kyau a cikin tsarin zamanantar da kasar Sin. Ya bukaci hakan ne yayin da ya gana da wakilai daga dukkan kabilu da sauran fannonin rayuwar al’umma a yankin Xinjiang mai cin gashin kansa na arewa maso yammacin kasar Sin. Xi, wanda shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin koli na soja, ya isa birnin Urumqi, babban birnin yankin Xinjiang da safiyar yau, domin halartar bukukuwan cika shekaru 70 da kafuwar yankin. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya isa birnin New York na Amurka da yammacin jiya Litinin, don halartar babban taron mahawara na MDD karo na 80. Yayin da yake birnin na New York, Li zai halarci wasu jerin ayyuka da Sin ta tsara, ciki har da taron manyan jami’ai game da shawarar tsarin shugabancin duniya, kana zai gana da babban magatakardar MDD Antonio Guterres da shugabannin kasashe masu ruwa da tsaki. Yayin tarukan cudanyar mabanbantan sassa, da na bangaren Sin da daidaikun kasashen, Li zai yi karin haske dangane da mahangar kasar Sin game da yanayin da ake ciki a harkokin kasa da kasa a halin yanzu, da manyan batutuwa da ayyukan MDD. Zai kuma fayyace manufofin kasar Sin na...
Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa tuni gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ɗauki manyan matakai na gyara tattalin arziki, ciki har da cire tallafin man fetur, haɗa farashin musayar kuɗi, da kuma sabunta tsarin haraji da kwastam. Ya ƙara da cewa waɗannan sauye-sauye sun fara samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari, inda ya nuna cewa manyan kamfanonin tantance darajar kuɗi irin su Fitch da Moody’s sun ɗaga matsayin Najeriya saboda ingantattun manufofi da ƙaruwar ajiyar kuɗi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...

Kuri’ar Jin Ra’ayoyi Ta CGTN: Guguwar Amincewa Da Kasar Falasdinu Ta Nuna Yadda Amurka Da Isra’ila Suka Zama Saniyar Waren Da Ba A Taba Gani Ba
Ya zuwa ranar 23 ga watan Satumba agogon Beijing, kasashe 152 cikin 193 na Majalisar Dinkin Duniya sun amince da Falasdinu a matsayin kasa. A cikin kasashe biyar masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD, Amurka ce kadai ba ta amince da kafuwar kasar Falasdinu ba. Wannan guguwar ta amincewa da kafuwar kasar Falasdinu ta sanya Amurka da Isra’ila sun zama saniyar ware a fannin diflomasiyya game da batun rikicin Falasdinu da Isra’ila. Wata kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a da CGTN ta gudanar a duniya ta nuna cewa kashi 78.2 cikin 100 na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa, babbar hanyar warware matsalar Falasdinu ita ce aiwatar da shawarar “kafa kasashe biyu”, wadda kuma ita ce ginshikin samar da...
Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae, zai gabatar da jawabi ga mutanen kasar Iran nan gaba kadan, saboda shigowar makin tsaro mai tsarki, inda ake saran zai tabo al-amura da suka shafi tsaron kasar da kuma siyasar kasa da kasa. Makon tsaro dai shi ne makon da aka fara yakin tsaron kasar mai tsari wanda ya zama masomin yakin tsaron na shekaru 8 tare da gwamnatin Ba’ath ta kasar Iran karkashin shugabancin Saddam Hussain a lokacin An fara yakin ne a ranar daya ga watan Mehr shekara 1359 wato a shekara 1980 har zuwa shekara 1988. Har’ila yau ana saran zai yi Magana kan sabbin al-amura da suke tasowa a cikin gida. Share...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa dandalin jawabi a MDD wata dama ce ta kasashen duniya su bayyana ra’ayinsu kuma Iran zata bayyana ra’ayinta a gobe Laraba 23 ga watan Satumba na wannan shekara ta 2025. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka jim kadan fafin ya shiga jirgi zuwa birnin NewYork a safiyar yau talata. Ya ce duniya a halin yanzu tana fuskantar danniya da babakere na wasu tsirarun kasashe a duniya. Sannan gaskiya mai dacin da ke faruwa a halin yanzu shi yadda yara da jarirai da suke mutuwa a gaza, a kisan kiyashin da HKI take aiwatarwa a Gaza kimani shekaru 2 da suka gabata. Sannan yayi allawadai da...
Tom Barrack, jakadan Amurka a turkiya sannan manzonta na musamman a Siriya da Lebanon ya amince da cewa gwamnatin Trump tana son ta hada mutanen kasar Lebanon da sojojin kasar yaki. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Tom Barrack yana fadar haka a wata hirar da yayi da yan jaridu a birnin Abudhabi a yau Talata, ya kara da cewa ya takurawa gwamnatin kasar Lebanon ta kwance damarar kungiyar Hizbullah. Jakadan ya kara da cewa Hizbullah makiyarmu ce makiyar HKI kuma tana da karfi, amma ba zamu taba bamawa sojojin Lebanon makamai ba, saboda zasu yaki HKI da su. Amma zami iya basu kananan makamai don su yi mutanen kasar wanda kuma suna kungiyar Hizbullah. Share...

Xi Jinping Zai Halarci Bikin Murnar Cika Shekaru 70 Da Kafuwar Yankin Xinjiang Na Uygur Mai Cin Gashin Kansa
A ranar Alhamis 25 ga watan nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci wani babban taro a birnin Urumqi, babban birnin yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa, domin murnar cika shekaru 70 da kafuwar yankin. An shirya fara bikin da shugaba Xi zai halarta da karfe 10:30 na safiyar Alhamis, kuma babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) da dandalin shafin intanet na kamfanin dillancin labarai na kasar Sin (Xinhuanet) za su watsa shi kai-tsaye. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
Sojojin HKI sun amabci cewa sojoji biyu sun halaka a wani kwanton bauna da mayaka a Gaza su ka yi, daga ciki har da kwamandan rundunar “Folcan”. Kakakin sojan HKI ya bayyana cewa wanda aka kashe din shi ne Manjo Shahir Natna’il, sai kuma Midgal Haimik a wani fada da aka yi a arewacin Gaza. Wasu kafafen watsa labarun HKI sun ambata cewa mayakan kungiyar gwagwarmaya ta Hamas sun yi wa sojoji kwanton bauna a wasu wurare biyu mabanbanta. A bisa kididdigar sojojin HKI adadin wadanda aka kashe zuwa yanzu a yakin Gaza, sun kai 911. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website...
‘Yan bindiga sun sace ɗan majalisar dokokin Jihar Filato, mai wakiltar Pankshin Kudu, Laven Denty, a gidansa da ke unguwar Dong na ƙaramar hukumar Jos ta Arewa. A makon da ya gabata ma, Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito yadda ‘yan bindiga suka kutsa cikin unguwar Dong, inda suka yi garkuwa da wani mai yi wa ƙasa hidima (NYSC), da kuma ɗalibin Jami’ar Jos. Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Ɓullar Cutar Mpox A Jihar Yadda Aka Bai Wa Ousmane Dembélé Kyautar Ballon d’Or Ta 2025 Masu garkuwar da mutanen sun shiga gidan iyalan Solomon Dansura, da misalin ƙarfe 10 na dare inda suka tafi da baƙinsa guda biyu a lokacin. Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto babu wani martani daga hukumomin jihar ko kuma...
An bayyana dan wasan a matsayin wanda ya lashe kyautar ne a bikin da aka gudanar ranar Litinin 22 ga watan Satumban 2025 a dakin taro na Theatre du Chatelet da ke birnin Paris a kasar Faransa. Ballon d’Or kyauta ce da akan bai wa dan wasan da ya nuna gwaninta a kowace shekara, inda akan yi la’akari da gudunmawar da dan wasan ya bayar ga kungiya da kuma kasarsa. Tun farko an fitar da jerin ‘ƴan wasa 30 cikin wadanda ake sa ran za su lashe kyautar. Dembele ya taka rawar gani wajen taimakon kungiyar PSG ta lashe gasar Ligue 1 da da kuma samun nasarar lashe gasar Champions Leage na farko a tarihinta, sannan ta kai wasan karshe...
Mohammad Hindi mataimakin sakatare janar din kungiyar gwagwarmaya ta jihadil Islami ya bayyana cewa an karbi bukatar dakatar da bude wuta a gaza, amma kasar Amurka da kasashen turai basa son a dakatar da bude wuta har sai an kawar da dukkan kungiyoyin gwagwarmaya baki daya ba wai a yankin falasdinu ba kawai. Haka zali ya kara da cewa HKI ta kai hari kan wajen da wakilan kungiyar hamas suke a birnin doha na kasar Qatar don tattaunawa kan batun dakatar da bude wuta. Isra’ila ta sanar a hukumance cewa prime minister Natanyaho ya sanar da shugaban Amurka Donald trump jim kadan kafin kai harin cewa isra’ila za ta kai wa Qatar hari, Harin ya jawo nuna damuwa sosai kan...
An ba shi kyautar ne a daren ranar Litinin a Theatre du Chatelet da ke birnin Paris, inda ya doke matashin Barcelona, Lamine Yamal, wanda ya lashe kyautar matashin ɗan wasa mafi ƙwazo. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Ƙididdiga a Najeriya, NBS ta ce arzikin cikin gida da kasar ke samu ya karu da kashi 4.23 cikin 100 a rubu’i na biyu na shekarar 2025 da muke ciki. Sabbin alkaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa an samu karin kashi 3.48 idan aka kwatanta da irin wannan lokacin a 2024, lamarin da hukumar ta ce alamu ne na ingantar tattalin arzikin kasar. Hukumar ta NBS ta ce fannin aikin gona ne kan gaba wajen samar da karuwar arzikin kasar, wannan ya karu zuwa kashi 2.82 sabanin kashi 2.60 a 2024. Sauran fannonin da hukumar ta ce an samu ci gaba sun hada da fannin masana’antu da, da fan fetur da kuma fannin ma’adinai. NBS ta ce...

He Lifeng: Ya Kamata Sin Da Amurka Su Karfafa Dangantakar Tattalin Arziki Da Cinikayya Mai Dorewa Cikin Lumana
Mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng ya gana da tawagar ‘yan majalisar wakilan Amurka karkashin jagorancin Adam Smith a yinin yau Litinin 22 ga wata a birnin Beijing. He Lifeng ya ce, a ranar 19 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaba Donald Trump sun yi wata tattaunawa ta wayar tarho, kuma sun cimma muhimmiyar matsaya, tare da samar da jagoranci bisa manyan tsare-tsare don tabbatar da daidaiton dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka a mataki na gaba. Kasashen Sin da Amurka na da sararin yin hadin gwiwa da kuma samun moriyar juna. Ana sa ran Amurka za ta sa kaimi wajen yin magana da kasar Sin bisa ka’idojin mutunta juna, da zaman lafiya da samun nasara...
29. Florian Wirtz (Liverpool) 28. Virgil van Dijk (Liverpool) 27. Declan Rice (Arsenal) 26. Erling Haaland (Man City) 25. Denzel Dumfries (Inter Milan) 24. Fabian Ruiz (PSG) 23. Jude Bellingham (Real Madrid) 22. Alexis Mac Allister (Liverpool) 21. Serhou Guirassy (Borussia Dortmund) 20. Lautaro Martinez (Inter Milan) 19. Joao Neves (PSG) 18. Scott McTominay (Napoli) 17. Robert Lewandowski (Fc Barcelona) 16. Vinicius Jr (Real Madrid) 15. Viktor Gyokeres (Arsenal) 14. Desire Doue (PSG) 13. Harry Kane (Bayern Munchen) 12. Kvicha Kvaratskhelia (PSG) 11. Pedri Gonzalez (Fc Barcelona) 10. Nuno Mendes (PSG) 9. Gigio Donnarumma (Man City) 8. Cole...
A halin yanzu, shugaba Bola Tinubu yana ganawa da gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara a fadar shugaban kasa dake Abuja a yammacin yau Litinin. Ganawar na zuwa ne kwanaki kadan bayan Fubara ya koma ofis a ranar 19 ga watan Satumba bayan da Shugaba Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da aka kafa a jihar Ribas tun farko. Tinubu ya bayyana matakin ne domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali bayan shafe watanni ana rikicin siyasa da ke barazana ga harkokin mulki da tsaro a jihar mai arzikin man fetur. Cikakken bayanai na nan tafe… Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
Yayin da “bikin girbi na manoman kasar Sin” na takwas ke karatowa, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, shugaban kasar, kuma shugaban kwamitin kolin soja Xi Jinping, a madadin kwamitin kolin JKS, ya mika gaisuwar bikin, da fatan alheri ga manoma da ma’aikatan dake gudanar da ayyukan da suka shafi harkokin noma, da kauyuka da kuma manoma a fadin kasar. Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a bana, mun shawo kan illar bala’o’i kamar fari, da ambaliyar ruwa, da samun daidaiton noman hatsin rani, da karuwar noman shinkafa mai nuna da wuri, ana kuma sa ran samun karin girbin hatsi. Xi Jinping, ya jaddada cewa, zamanantarwa irin ta kasar Sin ba za a iya...
Na hudu, an yi ta samu ci gaban sayayya sakamakon masu yawon bude ido daga ketare. Bisa ga manufar rage haraji lokacin barin kasa da kasar Sin ke gudanarwa, an shirya shirin “Sayayya a Sin” yadda ya kamata, wanda hakan ya canza fa’idar yawan baki daga ketare da suke yawon shakatawa a kasar zuwa habaka kudin da ake kashewa. (Bilkisu Xin) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ana ci gaba da takaddama a duniyar kwallon kafa kan wa ya fi cancanta da lashe kyautar Ballon d’Or a matsayin gwarzon dan wasan duniya na bana. A ranar Litinin din na za a bayar da Kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2025 a birnin Paris na kasar Fasansa, ga wanda alakalai suka zaba a matsayin Gwarzon Dan Wasan Kwallon Kafa na Duniya. Ballon d’Or ce kyauta mafi girma ta shekara-shekara ga ’yan wasan kwalllon kafa saboda bajintar da ya nuna ga ƙungiyarsa da ƙasarsa. Gasar ta bana ta kasance mafi zafi duba da yadda alkaluma ke nuna irin zakakurancin kowanne daga manyan ’yan wasan da ake hasashen za su iya lashe kambin. An rufe sansanin NYSC da kasuwanni saboda rashin...
A jiya Lahadi ne dai jirgin ruwan agaji da aka bai wa sunan; ” Umar Mukhtar” ya bar ruwan kasar Libya domin nufar Gaza da zummar karya killace yankin da aka yi na tsawon shekaru 18. Masu kula da jirgin ruwan na “Umar Mukhtar” sun bayyana cewa; Sun yi tanadin kayan aikin liktanci da aka bai wa sunan; Likitan Falasdinawa Husam Abu Saafiyyah. Har ila yau, hukumar agajin kasar Libya ta tanadi jirgin sama mai saukar angulu domin kai daukin gaggawa idan bukatar hakan ta taso. Da akwai mutane 20 a cikin wannan jirgin ruwan da su ka likitoci, masu fafutuka da kuma lauyoyi daga Libya da wasu kasashen turai. Jirgin ruwan na Agaji yana da cikakken goyon bayan al’ummar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jam’iyyar APC reshen jihar Taraba ta yi yi kakkausar suka ga mulkin Gwamna Agbu Kefas, inda ta ce bayan shekaru biyu a ofis ya gaza cika alkawuran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe. Jam’iyyar ta ce rashin tasirin gwamnatin PDP zai sauƙaƙa wa APC kwace mulki a shekarar 2027 a jihar. Da yake magana a Jalingo, Sakataren APC na jihar, Fidelis Francis, ya zargi Gwamna Kefas da rashin ƙaddamar da muhimman ayyukan raya ƙasa, ciki har da barin hanyar zuwa ƙaramar hukumar gwamnan a lalace bayan gadoji sun karye. Ya bayyana mulkin nasa a matsayin “wanda bai shirya ba kuma ba shi da wani tsari.” Francis ya ƙara da cewa PDP tun daga 1999 ba ta da abin...

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Jinjinawa Tawagar Kokawar Greco-Roma Ta Iran Murnar Lashe Gasar Cin Kofin Duniya
Jagoran juyin juya halin Musulunci yana taya tawagar kokawa ta Greco-Roma ta Iran murnar lashe gasar cin kofin duniya Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya taya tawagar kokawa ta Greco-Roman ta kasar Iran murnar nasarar da ta samu a gasar cin kofin duniya, yana mai godiya ga ‘yan wasa da masu horar da ‘yan wasa da masu gudanarwa da suka sanya farin ciki a zukatan al’ummar Iran da kuma abin alfahari ga kasar Iran. A cikin sakon nasa, Jagoran ya ce: Ina taya matasan kokawa murna. Ƙudurin ku da himma a cikin kokawa na Greco-Roman sun kawo farin ciki ga zukatan mutane da kuma alfahari ga ƙasar. Ina rokon Allah Ya ba ku daukaka da nasara,...

Kungiyar Ansarullahi Ta Yemen: ‘Yan Koren Amurka Da Isra’ila Suke Neman Wargaza Hadin Kan Larabawa Da Na Musulmi
Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada cewa: ‘Yan koren Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila na da nufin wargaza hadin kan Larabawa da na Musulmi Jagoran kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen Sayyed Abdulmalik al-Houthi ya jaddada cewa: ‘Yan koren Amurka da na haramtacciyar kasar Isra’ila suna neman tada fitina da sanya kiyayya a tsakanin al’ummomin Larabawa da na Musulmi. Ya yi nuni da cewa wadannan ‘yan kore ba su da wani aiki na gaske da zai yi hidima ga kasashensu na asali, sai dai mayar da hankali kan kokarinsu wajen wargaza zamantakewar al’umma, karkashin kulawar Amurka da tallafin Larabawa da kuma jagorancin yahudawan sahayoniyya. A cikin jawabin da ya gabatar a jiya Lahadi, a daidai lokacin da ake gudanar...
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya isa birnin New York, Amurka, domin halartar taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 wanda zai gudana daga ranar Litinin 22 ga Satumba zuwa Lahadi 28, 2025. Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu, zai gabatar da jawabin Nijeriya a gaban zauren, tare da shiga wasu tattaunawa da tarukan a gefe da dama. Ministan Harkokin Ƙasashen Waje, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa Nijeriya za ta ci gaba da mara baya ga tsarin haɗin gwuiwa tsakanin ƙasashe, ciki har da yunƙurin samun kujerar dindindin a Majalisar Tsaron MDD bisa matsayar haɗin kan Afrika, wato Ezulwini Consensus. Ya ce Shettima zai kuma bayyana sabbin manufofin Nijeriya na rage hayaƙin da ke gurbata muhalli bisa...
A yau Lahadi 21 ga wannan wata da yamma, firaministan kasar Sin Li Qiang ya gana da tawagar membobin majalisar wakilai ta kasar Amurka da Adam Smith ya jagoranta a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing. A yayin ganawar, Li Qiang ya bayyana cewa, Sin da Amurka manyan kasashe ne dake da muhimmanci sosai a duniya, kiyaye dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka mai dorewa yadda ya kamata ya dace da moriyar kasashen biyu da begen kasa da kasa. Sin tana son yin kokari tare da kasar Amurka wajen girmama juna, da zama tare cikin lumana, da yin hadin gwiwar samun moriyar juna. Kana kasar Sin tana son kasar Amurka ta yi hadin gwiwa tare da ita don sa...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya gargadi cewa, tarihi ba zai gafarta wa shugabannin Arewa ba idan suka kasa daukar matakin gaggawa wajen dakile kashe-kashe, garkuwa da mutane da rikice-rikicen da ke addabar yankin. Ya ce shiru da fifita wasu akan wasu daga cikin shugabanni suna kara ta’azzara matsalar tsaro a jihohin Zamfara, Kaduna, Katsina, Filato da Benuwe. Ya bayyana cewa akwai damuwa matuka yayin da ‘yan bindiga ke ci gaba da addabar al’umma, wasu daga cikin manyan mutane na fifita shirya shagulgula masu tsada maimakon kiraye-kirayen tarurrukan neman mafita na gaske don kawo karshen wannan rikici. “Lokacin yin shiru ya wuce, yanzu ne lokacin daukar mataki. Tarihi ba zai gafarta wa halin ko-in-kula ba a lokacin da ake bukatar mataki fiye da...
A daren ranar 19 ga wannan wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump sun tattauna ta wayar tarho, inda shugaba Xi ya jaddada cewa, alakar Sin da Amurka na da matukar muhimmanci, Sin da Amurka na iya cimma nasarar bai daya da wadata tare, ta yadda za su amfani kawunansu, da ma sauran sassan duniya baki daya. A nasa bangare kuwa, shugaba Trump cewa ya yi, alakar Amurka da Sin ita ce mafi muhimmancin dangantaka a duniya, yana mai cewa, aiki tare tsakanin kasashen biyu ka iya haifar da manyan abubuwa da za su ingiza zaman lafiya da daidaito a duniya. Ya yi fatan wanzar da babbar dangantaka mai armashi ta dogon lokaci tsakanin...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bukaci kasar Agfanistan ta mayarwa kasar Amurka san sanin sojojin sama na kasar wanda ke Bagram ko kuma zata ga ba dadi. Kafanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka da farko a shafinsa na zumunta na ‘ Truth Social’. Shugaban ya gargadi Taliban kan vewa idan sun ki mayarwa Amurka sansanin sojojin Bagram to wani abu ba dadi zai faru da sun. Trump ya dade yana zargin gwamnatin shugaba Biden da ya gada da yin ba dai-dai ba, daga ciki har da ficewa daga kasar Afganistan bayan mamaya na tsawon shekaru 20 ba tare da shiri ba. Amurka ta mamaye kasar Afganistan tun shekara 2001 har zuwa 2022...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa tattalin arzikin kasar Iran nan gaba zai ginu ne bisa shirin bayan karewar man fetur ne, inda fasahohi da ilmi da kirkire-kirkire da kuma darussan da za’a dauko daga kasashe kawayen kasar a kungiyoyin BRICS da kuma SCO ne zasu zama abin dogaru. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto shugaban yana fadar haka ne a daren jiya Asabar a wani taro wanda yake magana a kan hanyoyin da Iran zata bi don bunkasa fasaha da ilmin kere-keren kasar da samar da ci gaba masu dorewa a kasar. Pezeshkiya yace sauye-suyen da sauri da ake samu a duniya musamman a yankin tekun fariya sun sanya dabarbarun ci gaba na sauyawa...
Abdulahi, wanda ke jigilar kaya daga Agbara a Jihar Ogun zuwa Ibadan, ya ce yana kashe har Naira 25,000 a kowace tafiya da yake yi, inda mafi yawan kuɗin ke shiga hannun ƴ an Agbero a Legas, waɗanda ke gudanar da ayyukansu sa’o’i 24 a rana, kwana 7 a mako. Ya ce daga Berger, gefen Legas, zuwa Agbara, manyan motoci kan gamu da aƙalla tashoshi 15 na ta’annati, inda ake karɓar kuɗi tsakanin Naira 1,000 zuwa Naira 3,000 a kowane wuri. Manajan Daraktan wani kamfani da ke aiki a cibiyar masana’antu ta Agbara a Jihar Ogun, wanda ya nemi a sakaya sunansa ba, ya shaida wa wannan jarida cewa jigilar kwantena na kayayyakin masarufi daga tashar jiragen ruwa ta Apapa...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta SERAP tare da Amnesty International sun nemi Shugaba Bola Tinubu ya janye ƙarar da aka shigar a kotu kan ɗan gwagwarmaya Omoyele Sowore, da kuma kamfanonin sada zumunta X da Facebook. Ƙungiyoyin sun bayyana damuwa cewa hukumomin tsaro na ƙara amfani da kotu wajen tsoratar da ƴan Nijeriya da hana su faɗar albarkacin baki. A cikin wata wasiƙar da suka aike wa shugaban ƙasa ranar 20 ga Satumba, 2025, SERAP da Amnesty sun bayyana cewa ƙarar da DSS ta shigar bisa zargin saƙonnin da ake cewa sun na adawa da Tinubu ya zama wani SLAPP (ƙarar da ake amfani da ita don toshe bakin masu suka). Sun ce irin waɗannan suna haifar da tsoro...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta kama mutum biyar da ake zargi da satar fakiti 7,871 na abincin yara, wanda aka fi sani da Tamuwa, wanda aka tanada don yara masu fama da cutar yunwa. Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 19 ga Satumba, 2025 . Ya bayyana cewa an gano kayan ne a samame guda biyu da aka kai a Maiduguri. Shettima ya bar Abuja don halartar taron majalisar ɗinkin duniya a New York An sanya tukwicin N10m domin kama makasan limamin coci a Enugu Samamen farko ya auku ne a ranar 12 ga Afrilu, lokacin da aka tsayar da wata mota a Njimtilo, kusa da Maiduguri, inda...
A yayin da ake gudanar da shagulgulan ranar zaman lafiya ta Duniya ta Bana, Kungiyar rajin tabbatar da zaman lafiya da hadin Kai da kuma cigaban Arewacin Nigeria ta yi Kira ga Gwamnati a dukkan matakai da kuma Hukumomin tsaro su karfafa amfani da bayanan tsaro na sirri wajen kare rayukan al’ummar Kasa. Shugaban Kungiyar ta ACI Dakta Abdullahi Idris ya yi wannan Kira a wani taron manema labarai da Kungiyar ta Kira a Kaduna. Ya yi bayanin, Kungiyar ta lura da matakan da Gwamnati da Hukumomin tsaro suka dauka domin maido da zaman lafiya a wasu sassan Arewcin Kasar nan. Dakta Abdullahi Idris ya ce, matakan da aka dauka abin a yaba ne, Amma kuma sun yi kadan matuka...
Wanda zan iya tunawa za su kai goma haka. Ko akwai wani fim wanda bayan fitar sa ka samu ƙalubale daga dangi ko wajen masu kallo? Gaskiya a fim dai har yanzu ban samu wani ƙalubale ba, saboda duk abin da nake fitowa a rol na malunta ne. Kawai dai akwai wata waƙa da na yi bidiyonta a kanta ne gaskiya na fuskanci ƙalubale sosai, dan akwai wanda ya taɓa kira na yana hawaye ya ce min me ya ja min wannan harka haka har na fito ina rawa da jaruma?. To, sai na ji ban ji daɗi ba a lokacin, dan akwai gidajen TƁ da suka karɓa suke haskawa, nayi sauri na hana a haska ɗin. Sai kuma wani...
Ministan harkokin wajen Iran ya kore abinda wasu kafafen watsa labaru su ka watsa na zantawa a tsakaninsa da manzon Amurka a gabas ta tsakiya Steven Witkoff. Ministan harkokin wajen na Iran, Abbas Arakci ya fada wa kamfanin dillancin labarun “Tasnim” na Iran cewa; Babu gaskiya a cikin labarun da wasu kafafen watsa labaru su ka watsa.” Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma ce; Da akwai tuntubar juna a tsakanin Tehran da Washington kodai ta kai tsaye ta hanyar wasiku, ko kuma ta hanyar masu shiga Tsakani idan bukatar hakan ta taso.” Wasu kafafen watsa labarun kasashen turai ne dai su ka watsa labarin dake cewa; Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya gana da manzon musamman na Amurka...
Sanarwar ta ƙara da cewa, an bayar da ƙarin kayayyakin da za a raba a matsayin tallafin ne daga Hukumar Kula da Ilimi ta Duniya (UBEC) da UNICEF. A jawabinsa a wajen taron, Gwamna Lawal ya sake nanata cewa gwamnatinsa ta zo ne da aikin ceto da sake gina jihar. Ya ce: “Tun da farko mun gane cewa hanya mafi inganci wajen dawo da Zamfara kan turba ita ce saka hannun jari a zukatan al’ummarmu. “A yau, a cikin wannan alƙawari, na yi farin cikin sanar da raba kayayyakin koyo da koyarwa 408,137 da gwamnatin jihar Zamfara ta sayo kai-tsaye. “Wannan shi ne ɗaya daga cikin mafi girma na zuba jari a cikin albarkatun koyarwa da...
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin sahyuniya ta gaddamar da shirin mamaye wasu sabbin yankuna a kusa da birnin Qudus inda ta mamaye yankuna guda 3 kuma ta bukaci falasdinawa neman izini kafin su shiga gidajensu. Wannan mataki ya canza ka’idar mallakar kasa, bayan da Isra’ila ke kokarin kwace iko da muhimman wurare a gabar yammacin kogin jodan, wanda zai yi illa sosai ga yiyuwar samun kasar falasdinu mai cin gashin kai . Ana su bangaren hukumomin falasdinawa sun yi tir da wannan mataki, kuma sun bayyana shi a matsayin mataki mai muhimmacin wajen hade birnin Qudus da sauran yankunan falasdinawa ,kuma take hakokin falasdinawa ne. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies...

Kin Amincewar Japan Game Da Muggan Laifukan Yakin Da Ta Aikata Ya Dakatar Da Bukatar Sin Ga Hukumar UNESCO
A ranar Alhamis 18 ga watan nan, aka kaddamar da fara nuna fim din nan mai taken “Evil Unbound” a dukkanin sassan duniya, fim din da ya ba da labarin yadda a yayin yakin kin mamayar dakarun Japan, wata rundunar dakarun sojin kasar Japan ta aiwatar da wani shirin sirri, na gwaje-gwajen kimiyya ta makamai dake iya illata lafiyar bil’adama, a wani boyayyen wuri dake lardin Heilongjiang na arewa maso gabashin kasar Sin. Duk da cewa akwai shaidu na hakika, da suka tabbatar da aukuwar muggan laifukan da rundunar ta 731 ta tafka, bukatar kasar Sin ta shigar da wannan lamari cikin kundin killace abubuwan tarihi na UNESCO ya gamu da tsaiko, har na tsawon sama da shekaru shida. Kazalika,...

‘Yan Ta’addan Lakurawa Sun Sake Zama Sanadin Mutuwar Mutane Da Dama A Turmutsitsin Shiga Kwale-kwale
Al’ummar Jihar Sakkwato na cike da fargaba da alhini bayan da wasu mazauna kauyuka da dama suka rasu a hatsarin kwale-kwale a Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato. Lamarin ya faru ne lokacin da jama’a ke tserewa daga wani sabon harin da ‘yan ta’addan Lakurawa suka kai, inda kwale-kwalen da ke dauke da mutane fiye da kima ya kife. Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na Rundunar ‘Yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Abubakar Rufa’i, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga wakilin Rediyon Najeriya a jihar. ASP Abubakar ya ce har yanzu ba a tantance adadin mutanen da suka shiga kwale-kwalen ba, yana mai jaddada cewa ana ci bincike da aikin ceto. Wani shaidan gani da ido, wanda bai...
Kamfanin dillancin labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, lamarin wanda ya faru ne a lokacin da ake gudanar da aikin a ƙarshen mako a masana’antar, ya yi sanadin mutuwar ma’aikata biyu ciki har da wani jami’in soji da ke aiki tare da jikkata wasu huɗu. “Na ji wani babban ƙara har sai da ya girgiza gine-ginen da ke kewayen DICON. Mutane na ta gudu daga wurin, amma muna tunanin fashewar bam ne, amma daga baya mun gano cewa daga masana’anta ne,” inji wani mazaunin da ya nemi a sakaya sunansa. Shaidun gani da ido sun ce fashewar na da nasaba da samar da hoda mai matukar muhimmanci wajen ƙera hodar harsashi ga sojojin Nijeriya. Daga...
A kwanan nan ne aka rufe taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO a takaice, a birnin Tianjin dake arewacin kasar Sin, inda shugaban kasar, Xi Jinping ya gabatar da shawarar tsarin inganta jagorancin duniya. Wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, ta zanta da shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, wanda ya halarci taron, inda ya ce, ana amfani da ma’aunai biyu a halin yanzu a duk duniya. A cikin shawarar tsarin inganta jagorancin duniya da shugaba Xi Jinping ya gabatar, akwai wani muhimmin bangare na gudanar da harkokin duniya bisa dokokin kasa da kasa, wato ya kamata a mutunta ka’idoji. Masoud Pezeshkian, ya ce bai kamata a aiwatar da ma’aunai biyu a...
A shekarar 2025 a gundumar Qiemo dake jihar Xinjiang ta kasar Sin, wasu sabbin sassan dausayi da ake iya nomawa sun bayyana a cikin makeken yankin hamada. A ’yan shekarun nan, an gyara yankin rairayi zuwa gonaki, wadanda fadinsu ya zarce murabba’in kilomita 40 a gundumar Qiemo. A cikin sama da shekaru 10, an yi kokarin raya wasu sassan dausayi da ake iya nomawa a cikin yankin hamada dake jihar Xinjiang, inda fadin gonakin da ake noman hatsi ya karu zuwa murabba’in kilomita dubu 8 ko fiye, al’amarin da ya sa Xinjiang ta zama jihar da ta fi samun karuwar hatsi da ake nomawa a duk fadin kasar Sin. Wani babban manomi dake wurin, mai suna Liu Yong, ya ce...
Ya ce Morocco, ta sha alwashin zurfafa hadin gwiwa tare da Sin, karkashin shawarar ziri daya da hanya daya, da fadada musaya a fannoni irinsu yawon bude ido, da ilimi, da al’adu, da ci gaba da yayata kawance bisa matsayin koli tsakanin kasashen biyu. A daya bangaren kuma, Morocco na maraba, da kuma goyon bayan shawarar inganta tsarin shugabancin duniya da Sin ta gabatar. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Peng Liyuan Ta Halarci Bikin Mika Lambobin Yabo A Fannin Raya Ilimin Yara Mata Da Mata Na Hukumar UNESCO
Ta ce tun bayan da Sin da UNESCO suka kafa wannan dandali na gabatar da lambobin yabo a fannin raya ilimin yara mata da mata a shekarar 2015, kawo yanzu, a mika jimillar irin wadannan lambobi 20 ga ayyuka daban daban da suka cancanta daga kasashe 19. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wasu ’yan bindiga da ake zargin Lakurawa ne, sun kai hari ƙauyen Sayinna, da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza a Jihar Sakkwato. Sun kashe Hakimin ƙauyen, Malam Murtala Sa’adu, tare da wani mutum mai suna Ibrahim Mai-Kuɗi. Yadda za ka dawo da kuɗinka da ka yi kuskuren turawa wa wani An tsinci gawar kwamandan hukumar NDLEA a otel a Kalaba Mai bai wa shugaban Ƙaramar Hukumar Tangaza shawara, Alhaji Gazali Raka ne, ya tabbatar da harin. Ya ce maharan sun kashe hakimin ne saboda yana taimaka wa ’yan sa-kai wajen tsaro a yankin. An ce maharan sun shiga ƙauyen ne da misalin ƙarfe 1:30 na daren ranar Alhamis, inda suka dinga harbi a ko ina. Bayan sun kashe mutanen biyu, sai...
Daga nan ya wuce gidan tsohon shugaban ƙasa Marigayi Muhammadu Buhari domin yi wa matar sa Aisha da sauran ‘yan uwa ta’aziyya. Tinubu a gidan marigayi tsohon shugaban kasa, Buhari Ya bayyana Buhari a matsayin “shugaba mai kishin ƙasa da sadaukarwa, wanda gudunmawarsa ga haɗin kan Najeriya da ci gabanta ba za a manta da su ba,” inda ya tabbatar da ci gaba da goyon bayansa ga iyalan. Cikin manyan baki da suka halarci taron har da Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi; Gwamna Umar Bago na Jihar Neja; Gwamna Dikko Radda na Katsina; Gwamna AbdulRahman AbdulRazak na Kwara da Ministan Tsaro, Bello Matawalle. Sauran sun haɗa da tsoffin gwamnoni Sule Lamido na Jigawa; Aliyu Wamakko na Sakkwato;...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sheikh Na’im Kassima wanda ya gabatar da jawabi a jiya juma’a ya kuma kara da cewa; A halin yanzu kungiyar gwagwarmaya tana fuskantar matsanancin yanayi mai hatsari,tare da jaddada cewa; Wanzuwar HKI, manufarsa ita ce a samar da wani yanki na turai da Amurka a cikin wannan yankin domin hana al’ummar yankin ci gaba da bunkasa ta fuskokin ttatalin arzki, siyasa da al’adu da ci gaba. Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya kira yi kasar Saudiyya da ta bude sabon shafin alakarta da kungiyoyin gwagwarmaya. Har ila yau Sheikh Na’im Kassim ya ce, HKI wani makami ne na kasashen turai da aikinsa shi ne yin kisan kare dangi akan duk wanda ya ki yin biyayya a gare su....

Miyetti Allah ta roki Gwamntin Kwara da ta sa baki kan rufe Kasuwar Kara da Shugaban Karamar Hukuma Ya Yi
An bukaci gwamnatin jihar Kwara da ta gaggauta shiga tsakani kan rufe kasuwar Kara da ke yankin Kwara ta Kudu da shugaban karamar hukumar ya yi domin ceto harkokin kasuwanci daga durkushewa. Shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Kwara, Alhaji Shehu Garba ne ya yi wannan roko a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Ilorin. Sanarwar ta ce shirin rufe kasuwannin Kara da ke yankin Kwara ta Kudu da shugaban karamar hukumar ya yi ba tare da sanin sarakunan gargajiya da shugabanni da masu gudanar da aiki ba, bai dace ba. Ya bayyana cewa kafin daukar irin wadannan shawarwarin da shugaban karamar hukumar ya yi ya kamata a yi shawarwari da yawa don tafiyar da...

Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Ya Ce: Kwamitin Sulhu Ya Rasa Damar Tattaunawa Da Fahimtar Juna
Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Kwamitin sulhun Majalisar ya rasa damar tattaunawa da fahimtar juna a yau Jakadan kasar Iran kuma wakilin din-din-din a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani, ya yi tsokaci kan rashin amincewa da daftarin kudiri na ci gaba da dage takunkumin da aka kakabawa Iran a taron kolin na yau, sakamakon matsin lamba daga kasashen Amurka da Turai. Irawani ya bayyana a yayin taron kwamitin sulhun a jiya Juma’a cewa: Kwamitin sulhun ya yi watsi da damar tattaunawa da fahimtar juna, yayin da Rasha da China bisa gaskiya suka gabatar da wani madaidaicin kudiri na tsawaita kudurin Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2231 da kiyaye tsarin diflomasiyya. Ya ce: “Maimakon amincewa da...
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta jaddada cewa: Iran tana da ‘yancin mayar da martani ga duk wani mataki da ya sabawa doka Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar da wata sanarwa a jiya Juma’a dangane da haramtaccen matakin da kungiyar Tarayyar Turai Troika ta dauka na mayar da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya kan Iran a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ta hanyar yin amfani da tsarin warware takaddama kan shirin hadin gwiwa na hadin gwiwa (JCPOA) (yarjejeniyar nukiliya ta 2015) da kuma kuduri mai lamba 2231. Bayanin ya ci gaba da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah-wadai da matakin da kasashen Turai uku wato Faransa da Jamus da kuma Birtaniya suka dauka na yin amfani da...
Mataimakin ministan harkokin wajen Iran mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa ya mayar da martani kan zargin shugaban Faransa Emmanuel Macron Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa, Kazem Gharibabadi, ya musanta zargin da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi a baya-bayan nan, yana mai jaddada cewa, a yayin da ministan harkokin wajen Iran ke magana, ko tattaunawa, ko ya aika da sako, ko gabatar da wata shawara, wannan mataki ya nuna ra’ayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma yana samun matsaya na cikin gida, kamar yadda aka gani a tattaunawar fahimtar juna tare da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya a birnin Alkahira. A cikin...
Daga baya an ƙara nata wani nauyin kula da Tashoshin Warri, Koko, Burutu da kuma ta Sapele, waɗanda kamfanonin ƴ an kasuwa masu zaman kansu ne, ke tafiyar da su, amma har zuwa yau, mahukunta a NPA ne, ke tafiyar da duk wata ragamar hukumar baki ɗaya. A shekaru da dama da suka gabata, matsaloli da dama, sun dabaibaye NPA da suka haɗa da, cin hanci da rashawa da rashin ingantattun kayan aiki, musamman na zamani da sauransu, inda waɗannan matsalolin suka haifar wa da NPA koma baya matuƙa, musamman na wajen zama a kan gaba wajen gudanar da harkar hada-hadar kasuwanci a nahiyar Afirka. Amma, za mu iya cewa, Allah san barka da naɗa Dakota Abubakar Ɗantsoho, a matsayin...

Kamfanin Kasar Sin Ya Bayar Da Gudunmuwar Kayayyaki Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Sudan Ta Kudu
Kamfanin man fetur na kasar Sin (CNPC), ya mika wasu kayayyakin agaji ga dubban mutanen da ambaliya ta raba da matsugunansu a jihar Unity mai arzikin man fetur dake arewacin kasar Sudan ta Kudu. Daraktan sashen hulda da jama’a na reshen kamfanin CNPC a Afrika Ren Yongsheng, ya ce gudunmuwar ta kunshi tantuna, da barguna, da tabarmi, da gidajen sauro, da magungunan zazzabin cizon sauro. A cewar ofishin MDD mai kula da harkokin jin kai, kimanin mutane 273,000 ne ambaliyar ta shafa a gundumomi 12 na jihohin Jonglei da Unity da Upper Nile da Central Equatoria, inda jihohin Jonglei da Unity suka dauki sama da kaso 91 na jimilar mutanen da ambaliyar ta shafa. Martha Remijo Rial, daraktan kula da...
1- Musayar yawu ta hanyar sumbatar juna- Ma’ana, ta hanyar sumbatar juna a tsakanin ma’aurata, idan guda daga cikinsu na ɗauke da cutar, nan da nan ɗayan shi ma zai kamu da cutar. 2- Gaurayewar jini ko haɗuwar jini- Haɗuwar jini, misali; idan wani ya yi amfani da reza ya yanke, ɗayan ya yi amfani da ita, zai iya kamuwa da cutar, ko kuma wani abu maikama da haka. 3- Ɓangaren saduwa a tsakanin ma’aurata- A wajen saduwa tsakanin mata da miji, ta hanyar haɗuwa maniyyi ko maziyyi da sauran makamantansu, wannan cuta za ta samu hanyar shigewa nan take da ɗaya daga cikinsu na ɗauke da ita. Don haka, waɗannan hanyoyi da aka ambata dukkanninsu na iya faruwa a...
Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe, ta ƙaryata rahotannin da ke nuna cewar an kai hari sakatariyar ƙungiyar ’yan jarida ta Najeriya (NUJ) da ke Damaturu. Wannan na cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Juma’a. An cafke mutum 6 kan tono gawa a kabari don yin asiri a Gombe Wata mata ta ƙona al’aurar ’yarta da wuta kan zargin maita a Bauchi Kakakin rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ya ce abin da ya faru shi ne wani jami’in tsaro da ke gadin wajen ne ya samu rauni a ƙafarsa ta hagu. A cewarsa, raunin ba shi da alaƙa da harbin bindiga, kamar yadda wasu shafukan Internet suka wallafa. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:45 na daren ranar...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ziyarci iyalan tsohon Shugaban Ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari a Jihar Kaduna bayan halartar ɗaurin auren ɗan tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari. Da zuwansa, Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, da ɗan marigayin, Yusuf Buhari, tare da wasu suka tarbe shi. Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Game Da Bunkasa Ci Gaban Mata An Dakatar Da Shugabannin Makarantun Sakandire 6 A Sakkwato Kan Rashin Bin Dokokin Aiki Shugaba Tinubu ya gana da uwargidan marigayin, Aisha Buhari, da sauran ‘ya’yansa, inda ya sake yi musu ta’aziyya. Ya kuma tabbatar wa Aisha Buhari cewa zai ci gaba da kula da ayyukan alheri Buhari ya bari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
Albarkacin bikin murnar cika shekaru 100 na kafuwar Jam’iyyar Zhigong ta Sin, shugaban kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta Sin, JKS, kana shugaban kasar Xi Jinping ya aika wasikar taya murna, kuma a madadin kwamitin tsakiyar JKS, ya taya dukkan ’yan Jam’iyyar Zhigong murna tare da nuna musu gaisuwa. Xi Jinping ya jaddada cewa, a kan sabon tafarki, ana fatan Jam’iyyar Zhigong ta ci gaba da zaune bisa jagorancin JKS, ta kuma kara zurfafa fahimta da aiwatar da tsarin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin, ta hada kai da ’yan uwa Sinawa dake ketare, da wadanda suka dawo gida, da kuma daliban dake karatu a kasashen waje, don ba da gudunmawa ga babban aikin dunkulewar kasar, da kuma taka rawar...
Wata mata mazauniyar garin Magama Gumau a Ƙaramar Hukumar Toro, Jihar Bauchi, ta shiga hannun ’yan sanda biyo bayan ƙona al’aurar ’yarta mai shekaru 10 kacal a duniya, kan zargin maita. Rahotanni sun nuna cewa matar ta yi amfani da cokali ta hanyar sanya shi a wuta ya yi zafi sannan ta umarci ’ya’yanta biyu suka riƙe yarinyar sannan ta ƙona ta. Janye Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya koma Ribas ’Yan bindiga sun kai hari sakatariyar ’yan jarida ta jihar Yobe Wannan ya jefa yarinyar cikin mawuyacin hali, inda ta ke fama wahalar yin fitsari da bayan gida. Bayan lamarin ya faru, maƙwabta sun kai ƙarar matar wajen ’yan sanda. An garzaya da yarinyar zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa...
Wata mata mazauniyar garin Magama Gumau a Ƙaramar Hukumar Toro, Jihar Bauchi, ta shiga hannun ’yan sanda biyo bayan ƙona farjin ’yarta mai shekaru 10 kacal a duniya, kan zargin maita. Rahotanni sun nuna cewa matar ta yi amfani da cokali ta hanyar sanya shi a wuta ya yi zafi sannan ta umarci ’ya’yanta biyu suka riƙe yarinyar sannan ta ƙona ta. Janye Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya koma Ribas ’Yan bindiga sun kai hari sakatariyar ’yan jarida ta jihar Yobe Wannan ya jefa yarinyar cikin mawuyacin hali, inda ta ke fama wahalar yin fitsari da bayan gida. Bayan lamarin ya faru, maƙwabta sun kai ƙarar matar wajen ’yan sanda. An garzaya da yarinyar zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa...
Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari a sakatariyar Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) da ke Damaturu, babban birnin jihar Yobe, da sanyin safiyar Juma’a. Rahotanni sun ce yayin harin, maharan sun harbi wani jami’in ɗan sanda da ke gadin sakatariyar suka ji masa rauni ƙafa. An dakatar da shugabannin sakandare 6 a Sakkwato kan zargin cin amanar aiki Amurka ta hau kujerar-na-ƙi kan buƙatar MDD ta tsagaita wuta a Gaza Lamarin dai ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na dare, inda maharan suka buɗe wuta. Shugaban ƙungiyar NUJ reshen jihar, Rajab Ismail Mohammed, ya bayyana harin a matsayin abin tayar da hankali da kuma babbar barazana ga lafiyar ’yan jarida...
Bola Ahmad Tinubu shugaban najeriya yayi alkawarin karbar bakuncin gasar wasannin kasasen renon ingila commom wealth a karon farko a shekara ta 2030 idan da rai da lafiya. Shugaba tinubu ya bayyana hakan ne ta bakin shugaban hukumar wasanni ta kasa shehu dikko a lokacin da yake tarbar mambobin kungiyar ta common wealth a birnin tarayya Abuja a wani bangaren na kokarin da najeriya ke yi kan batun. Malam Shehu Dikko ya bayyana cewa shugaban kasa bola Ahamd tunubu ya dauki alwashin dawo da wasanni a Afrika a karon farko,inda ya bayyana shi a matsayin wani babban matakin kara kusanto da mambobin kungiyar kusa, A ci gaba da kokarin da gwamnati ke yi na ganin ta karbi bakunci shirya gasar,...
Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta ce akalla mutane 1,666 mazauna jihar Legas sun rasa ransu ta hanyoyin da ba su dace ba, ciki har da kashe kansu, tsakanin farkon 2020 zuwa karshen 2024. Wannan bayani ya fito ne daga bakin likitan binciken gawarwaki na rundunar, ACP Samuel Keshinro, yayin gabatar da rahoton bincike kan kisan mata a wani taron da aka gudanar a jihar ranar Alhamis. Cutar Kwalara ta kashe mutum 58 a Bauchi Amurka ta hau kujerar-na-ƙi kan buƙatar MDD ta tsagaita wuta a Gaza A cewar Keshinro, rahoton ya mayar da hankali ne kan abubuwan da suka shafi kisan kai, kashe kai, hatsarurruka da sauran hanyoyin mutuwa da ba su da alaka da cuta, domin wayar da kan...
Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar Yamen sun kaddamar da hare-hare guda 3 da gagarumar nasara a wasu mihimman wurare a HKI, da zimmar mayar da martani kan hare haren da Isra’ilan take kai mata, saboda ci gaba da nuna goyon bayan alummar falasdinu da take yi da ta kwashe shekaru biyu ta na yi musu kissan gilla, Acikin wani bayani da kakakin sojin kasar Yamen Yahya Saree ya fitar ya sanar cewa kasarsa ta kaddamar da hare hare a muhimman wuraren guda 3 a Yaffa da HKI ta mamaye , kuma ta yi amfani da makami na haypersoni balisstic missile da ta basu suna da falasdinu na 2. Haka zakila ta kai hari a yankin umm Rashrash wato...
Rahotanni sun bayyana cewa tankunan yakin HKI na ci gaba da kutsa kai a tsakiyar gaza a yau juma’a, lamarin da ya jawo tsananta kai hare-hare ta kasa da tilastawa dubban mutane barin muhallinsu sakamakon yankewar hanyoyin sadarwa, A gefe daya kuma Amurka a karo na 6 ta hau kujerar naki kan kudurin kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya na bukatar dakatar da bude wuta da kuma sakin fursunoni da aka kama. Yankin gaza yana dauke da mutane miliyan daya kafin yaki, sai dai rahutanni sun bayyana cewa ya zuwa yanzu sama da 350,000 ne suka bace. Hare hare Isra’ila tun daga 7 ga watan oktoban shekara ta 2023 ta kashe falasdinawa 65141 kuma ta jikkkata 165925 kamar yadda majiyar...
A cewar ma’aikatar, dakatarwar ta na nufin samar da damar ci gaba da tattaunawa da duk masu ruwa da tsaki da kuma yin cikakkiyar bitar tsarin harajin da tasirinsa na dogon lokaci ga tattalin arziki. A watan Afrilu 2025, Kwaturola Janar na Kwastom, Adeniyi, ya bayyana shirin sake gabatar da harajin kashi 4 bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki, cewa wannan cajin, wanda ake lissafawa bisa Free on Board (FOB) na kayan da ake shigowa da su, an riga an sokƙ shi a baya daga al’umma masu kasuwanci saboda nauyinsa ga masu shigo da kaya. Nan da nan sanarwar ta jawo cece-kuce daga ƴ an kasuwa, kamfanonin jigilar kaya, da ƙungiyoyin masana’antu, waɗanda suka bayyana cewa matakin zai rage...
A ranar 18 ga watan Satumban shekarar 1931, sojojin Japan suka tarwatsa wani sashi na layin dogo dake karkashin ikonsu, a kusa da birnin Shenyang, tare da zargin sojojin kasar Sin da aikata barna, domin su fake da hakan wajen kai hari barikin sojojin Sin dake kusa da birnin na Shenyang a daren ranar, da kuma hakan ne suka kaddamar da mamayar da suka kitsa cikin kasar Sin. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Likitocin Sin Dake Aikin Agajin Kiwon Lafiya A Nijar Sun Gudanar Da Tiyatar ALT A Karon Farko A Yammacin Afirka
A baya bayan nan, tawagar likitocin kasar Sin ta 24 dake aikin agajin kiwon lafiya a janhuriyar Nijar, ta gudanar da tiyatar ALT irinta ta farko da aka yi nasarar gudanarwa a yankin yammacin Afirka. An gudanar da tiyatar ne a babban asibitin gwaji na kasar ta Nijar. Kuma ana gudanar da tiyatar ALT ne ta hanyar yankar wasu sassan fata da tsokar cinyar mara lafiya, domin dasawa a wasu sassan jikinsa da suka lalace sakamakon wata matsala. Ana kallon nasarar da aka samu ta aiwatar da wannan tiyata a Nijar, a matsayin nasarar da za ta cike gibin da ke akwai a fannin, a yankin yammacin Afirka. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni...
Kotun ta kuma samu Musa da mallakar harsashi na musamman har guda 34 mai nauyin (7.62mm) ba bisa ƙa’ida ba. Ga laifin kisan kai, sashe na 220 na kundin laifuffuka da kuma hukuncin da ke karkashin sashe na 221, Musa an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya. A laifi na biyu na mallakar harsasai ba bisa ka’ida ba, sashe na 8 (1) na dokar bindigogi, an yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari. Bugu da ƙari, an kore shi daga aikin sojan Nijeriya acikin ƙasƙanci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...

Sashen Raya Kimiyya Da Fasaha Na Sin Ya Kai Babban Matsayi Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Karo Na 14
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A cewarsa, jihar ta ba da fifiko wajen samar da kudade, kayayyakin more rayuwa, da kuma samun damar koyo tun bayan hawansa kujerar mulki. Gwamnan ya kara da cewa, yadda gwamnatinsa ta mayar da hankali kan ilimin ’ya’ya mata, bayar da tallafin karatu, da rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, ya taimaka wajen kawo sabon matsayi a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rahotannin cibiyoyin kididdiga a HKI sun ambaci cewa, ana ci gaba da samun yin hijirar yahudwa zuwa waje wanda shi ne mafi girma a cikin shekaru da dama. Jaridar “Ma’ariv” ta amabto wani makwararre a fagen kididdiga yana cewa; Shekarar 2024 ta fuskanci ficewar mutane masu yawan gaske daga “Isra’ila” saboda yakin da ake yi a Gaza. Haka nan kuma ya ce, wannan shi ne karo na hudu a cikin shekaru masu yawa da ake yin hijira daga Isra’ila. Bugu da kari ya ce, baya ga yahudawa da akwai ‘yan hijira da dama da suke ficewa da hakan yake da jan hankali sosai. Haka nan kuma ya ambaci wasu daga cikin dalilan da su ka Sanya ake yin hijira da...
Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa 4 daga cikin sojojinsu na mamaya sun halaka a sanadiyyar fashewar wata nakiya da aka dasa wacce ta tashi da daya daga cikin motocinsu a Gaza. Majiyar ‘yan sahayoniyar ta ce,baya ga sojojin 4 da su ka halaka a yau Alhamis, an kuma samu wasu 8 da su ka jikkata lokacin da motar Hommer ta daukar sojoji da aka dasawa nakiya ta fashe da su. Kafafen watsa labarun na ‘yan sahayoniya sun bayyana abinda ya faru da cewa: Yana da tsananin ciwo”, sannan kuma su ka kara da cewa, labarin ya faru ne a yankin da ake dauka cewa yana da aminci. A wani gefen, kungiyar ” Kata’ibul-Mujahidin” ta sanar a yau Alhamis...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar ’yan sandan Jihar Neja ta kama wasu mutane tara da ake zargi da shirin yin garkuwa da kansu tare da neman kuɗin fansa Naira miliyan 7. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, inda ya ce waɗanda ake zargin na da hannu a cikin shirin zamba na Ponzi, kuma ɗaya daga cikin tawagarsu ya shirya da wanda ake zargin ya samu kuɗin fansa daga abokan aikinsu. An kama sojan bogi da ɓarayin mota 2 a Jigawa Kasar Albania ta nada mutum-mutumi a matsayin minista An kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin mai suna Suleiman Dauda a Minna babban birnin jihar, inda daga bisani ya ambaci wasu...
Tun a ranar 7 ga watan Satumba, 2025, wani mutum mai suna Hussaini Manager ya kai rahoto ofishin ’yansanda na Kafin Hausa cewa an sace masa mota ƙirar Golf mai launin shuɗi mai lambar MGA 108 JG a Agura Motor Park, Kafin Hausa. Bincike ya gano cewa ɗaya daga cikin mutanen na yin sojan gona ne, yana kiran kansa Lance Corporal Kabiru Musa, alhali kuma ɗan asalin unguwar Rimin Kebe ne a Jihar Kano. Lokacin da aka cafke su, an samu mota, katin ATM guda bakwai, lasisin tuƙi guda biyu, da wasu abubuwa da ake zargin na damfara ne a hannunsu. Bayan kammala bincike, an gurfanar da su a gaban kotu. Kwamishinan ’yansandan Jihar Jigawa, Dahiru Muhammad, ya yaba wa...
Wani jariri ya rasu a bayan mahaifiyarsa lokacin da take kokarin tserewa daga harin ’yan bindiga a ƙauyen Allawa da ke ƙaramar hukumar Shiroro ta Jihar Neja. Hakkin ya fito ne daga bakin Hakimin Bassa, Bagudu Amos, yayin wani taron tattaunawa da mata kan rikici da zaman lafiya mai taken: “Ƙarfafa Matakan Kare Fyade da Cin Zarafin Mata a Jihar Neja”. Gwamnatin Gombe ta gyara hanyoyin kiwo domin daƙile rikicin manoma da makiyaya HOTUNA: Yadda dubban magoya baya suka yi dafifi don tarbar Fubara Taron dai wata kungiya mai zaman kanta mai suna Tunani Initiative ce ta shira shi, tare da hadin gwiwar gidauniyar Dorothy Njemanze Foundation da kuma gidauniyar Foundation, domin ƙarfafa gwiwar mata wajen magance cin zarafin jinsi...
A lokacin dokar ta-ɓaci, Tinubu ya naɗa tsohon Hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), a matsayin wanda zai yi mulki na rikon ƙwarya. A jawabin bankwana da ya yi da safiyar ranar Alhamis, Ibas ya roƙi ’yan siyasa a jihar su ci gaba da kiyaye zaman lafiya da haɗin kai da gwamnatinsa ta samar a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Zamanin kebe kai ya ƙare, Haɗin gwiwar Iran da Rasha ya cimma abin koyi mai nasara A yayin ganawarsa da ministan makamashin kasar Rasha Sergei Tyswell da tawagarsa, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Nasarar da aka samu na hadin gwiwa tsakanin kasashe masu cin gashin kai kamar Iran da Rasha, ya tabbatar da cewa zamanin kebe kai a duniya ya kare. Ya kuma jaddada cewa, wadannan kasashe suna iya samun ci gaba da bunkasa ba tare da bukatar ko dogaro da karfi mai amfani da bangare guda. Shugaban na Iran ya bayyana jin dadinsa da ci gaban hadin gwiwar kasashen biyu, musamman a fannin sufuri, makamashi, da ayyukan samar da wutar...
Magoya bayan Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, sun yi dafifi a Gidan Gwamnati da ke Fatakwal domin tarbar shi da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, bayan dawowarsu ofis. Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Fubara na tsawon watanni shida a lokacin da rikicin siyasa ya yi ƙamari a jihar. Gwamnatin Tarayya ta raba wa talakawa N330bn — Ministan Kuɗi ’Yan bindiga sun sako ma’auratan da suka sace a Katsina bayan biyan N50m Sai dai a ranar Laraba, Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci tare da umartar gwamnan, mataimakiyarsa da ’yan majalisar dokokin jihar da su koma bakin aiki daga ranar Alhamis, 18 ga watan Satumba. A halin yanzu, tsohon shugaban riƙon ƙwarya na jihar, Rear Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya miƙa mulki...
Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Iran ta cika hakkinta, yanzu kuma turai ne ake jiran ta cika nata hakkokin Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa, a wani mataki da Iran ta dauka na nauyin shiga tattaunawa da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, domin tsara wani sabon daftarin aiki mai ma’ana kan yadda za a aiwatar da alkawuran da ta dauka na kare hakkokin da suka hau kanta, yanzu kuma ana jiran Turai ta cika nata alkawuran. A wata tattaunawa ta wayar tarho tare da ministocin harkokin wajen Faransa, Jamus, da Birtaniya, da kuma jami’in kula da harkokin waje na EU, Araqchi ya ce: “Dole ne sauran bangarorin su yi amfani da...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila na aikata kisan kiyashi a Gaza, kuma magoya bayanta suna da hannu a ciki Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya jaddada cewa: Rahoton kwamitin binciken gaskiya na Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar da cewa, laifukan da haramtacciyar kasar Isra’ila ta aikata a Gaza sun kai na “kisan kare dangi”, inda ya yi kira ga masu kare gwamnatin ta Isra’ila da su daina shiga da hada baki wajen aikata wadannan laifuka kan al’ummar Falastinu. Baqa’i ya bayyana cewa: Kwamitin bincike mai zaman kansa na kwamitin kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya kan laifukan da ake aikatawa a Falasdinu da aka mamaye karkashin jagorancin fitacciyar marubuciya Navi Pillay,...
Wani makami mai linzami na Yemen ya tilastawa jirgin saman fira ministan gwamnatin Isra’ila saukar gaggawa Kafofin yada labaran yahudawan swahayoniyya sun watsa rahoton cewa, an tilastawa jirgin saman Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu yin saukar gaggawa a lokacin da ake atisayen soja bayan harba makami mai linzami daga kasar Yemen zuwa yankunan Falasdinawa da aka mamaye. Kafofin yada labarai sun ruwaito cewa, makamin da aka harba a yankunan da aka mamaye a shekarar 1948, jiya, Talata, ya tilastawa miliyoyin yahudawan sahayoniyya tserewa maboyan karkashin kasa. An yi ta jin karar harbe-harbe ta sama a yankuna da dama na yankunan Falasdinawa da aka mamaye, tare da jin karar fashewar abubuwa masu karfin gaske. Share 0 0 votes Article...
A lokacin dokar ta-ɓaci, Tinubu ya naɗa tsohon Hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), a matsayin wanda zai yi mulki na rikon ƙwarya. A jawabin bankwana da ya yi da safiyar ranar Alhamis, Ibas ya roƙi ’yan siyasa a jihar su ci gaba da kiyaye zaman lafiya da haɗin kai da gwamnatinsa ta samar a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya jaddada cewa dakarun tsaron Nijeriya suna da ƙarfin da za su iya fatattakar ’yan ta’adda, amma abin da ya rage shi ne samun ingantaccen shugabanci da ƙwarin gwiwa daga fadar shugaban ƙasa. Atiku ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su haɗa kai domin ceto ƙasar nan, inda ya bayyana cewa dawo da zaman lafiya da bunƙasa tattalin arziƙi ya kamata su zama fifiko. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Jihar Zamfara ta roki Hukumar Raya Kasashen Waje ta Kasa (FCDO), Premier Urgence Internationale (PUI), da sauran masu ruwa da tsaki da su kara tallafa wa ‘yan gudun hijirar da ke jihar. Kwamishinan Bada Agaji na Jiha Alhaji Salisu Musa Tsafe ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake jawabi ga mahalarta taron na kwana guda kan shirin ceton rayuka da karfafawa da kuma juriya (LEARP) wanda kungiyar FCDO ta dauki nauyin shiryawa a Abuja. A wata sanarwa dauke da sa hannun Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar, Bashir Kabiru Ahmad, Kwamishinan ya bayyana cewa a halin yanzu jihar na karbar dubban ‘yan gudun hijira daga al’ummomi sama da 1,008 a fadin kananan hukumomin 14, kamar yadda...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Imo, ta ce jami’an tsaro da suka haɗa da ’yan sanda, sojoji da DSS sun kashe ’yan ta’addan ƙungiyar IPOB da yawa. Kakakin rundunar, DSP Henry Okoye, ya ce tawagar ta lalata sansanonin IPOB a yankin Ezioha da ke Ƙaramar Hukumar Mbaitoli, da kuma a Umuele, Ubuakpu, da Amakor a Ƙaramar Hukumar Njaba. ’Yan bindiga sun sako ma’auratan da suka sace a Katsina bayan biyan N50m NAJERIYA A YAU: Wadanne Kalubale Gwamna Fubara Zai Fuskanta Bayan Dawowa Mulkin Ribas? Ya ce da yawa daga cikin mambobin ƙungiyar sun mutu yayin samamen, wasu kuma an kama su, yayin da wasu suka tsere da raunuka. Okoye, ya ƙara da cewa an gano bindigogi da harsasai da dama a...
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar wa kungiyar mafarauta/Yanbulala reshen jihar Jigawa na rundunar a shirye ta ke ta shirya wani horo na kara musu karfin gwiwa ga mambobinsu. Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Dahiru Muhammad ya bayar da wannan tabbacin ne a yayin wani taro da aka yi da mafarauta/Yanbulala na yankin wanda Lamido Wada ya jagoranta a Dutse babban birnin jihar. Ya bayyana cewa, Rundunar za ta hada gwiwa da wadanda abin ya shafa domin fuskanatar kalubalen zirga-zirga don daukar matakin da ya dace. A cewarsa, rundunar ta ci gaba da shirye-shiryen ‘yan sanda da al’umma ke tafiyar da su ta hanyar samar da hadin gwiwa mai karfi da masu ruwa da tsaki da suka himmatu...
Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mani Malam Mumini ya jajanta wa al’ummar karamar hukumar Gumi kan mumunan al’amuran da suka salwantar da rayukan mazauna kauyen Fas su 19 a makonnin da suka gabata. Malam Mumini ya bayyana haka ne a lokacin da ya jagoranci wasu jami’an gwamnati da suka kai ziyarar jaje ga al’umma, inda ya jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa, da Majalisar Masarautar, da daukacin al’ummar Gumi. Ya bayyana bala’in a matsayin mai raɗaɗi, yana mai jaddada cewa, gwamnatin jihar ta himmatu wajen magance matsalolin. Mataimakin Gwamnan ya tuna cewa lamarin na farko ya faru ne a lokacin da mazauna kauyen cikin firgici kan harin da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne suka kai, suka shiga...
A lokacin gudanar da bincike, an samu layin waya guda 21 da takardun rijistar layi guda 29 a wajen Suleiman, wanda ya ce yana harkar rijistar layin ne. Ya amsa cewa shi ne ya bai wa waɗanda “aka sace” waya da lambar da aka yi amfani da ita wajen neman kuɗin fansa. Binciken ya nuna cewa waɗannan mutanen suna cikin wani tsari na zamba wanda ake kira da Ponzi. An kuma gano cewa ɗaya daga cikinsu ya haɗa baki da wanda aka ce an yi garkuwa da shi don su karɓi kuɗi daga sauran abokan harkarsu. SP Abiodun ya ce bincike ana ci gaba da bincike domin kama sauran waɗanda ke da hannu a lamarin, yayin da aka riga aka...
Wani ɗan kasuwa a Jihar Katsina mai suna Anas Ahmadu da matarsa, Halimatu wadda ke ɗauke da juna biyu, da kuma ’yarsu mai shekaru biyu, sun kuɓuta daga hannun ’yan bindiga, bayan sun shafe kwanaki 21 a hannunsu. An sako su ne a daren ranar Laraba bayan biyan kuɗin fansa Naira miliyan 50, kamar yadda wani ɗan uwansu ya bayyana wa Aminiya. Gobara ta kashe manyan jami’an hukumar FIRS 4 a Legas NAJERIYA A YAU: Wadanne Kalubale Gwamna Fubara Zai Fuskanta Bayan Dawowa Mulkin Ribas? “Alhamdulillah! Anas, Halimatu da ’yarsu sun kuɓuta. Yanzu haka suna kan hanyarsu ta zuwa gida, amma sai da aka biya ’yan bindigar kuɗin fansa Naira miliyan 50,” in ji shi. An sace su ne a...
A wani yunkuri na inganta kula da mata masu juna biyu da sauran ayyukan kiwon lafiya a jihar Jigawa, Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF tare da hadin gwiwar Karamar Hukumar Kirikasamma sun mika kayayyakin aiki da wasu muhimman kayayyaki ga cibiyar kiwon lafiya ta farko a Kirikasamma. Mai kula da cibiyar kiwon lafiya ta farko, Kabiru Musa, ya bayyana cewa kayayyakin sun haɗa da gadajen haihuwa, zannuwan gado, kayan aikin jinya, matashin kai da sauransu, kuma za a rarraba su zuwa wuraren kiwon lafiya a fadin karamar hukumar. A cewarsa, kayan da UNICEF da karamar hukumar suka samar za su inganta yadda ake gudanar da ayyukan kiwon lafiya a yankin. Yayin mika kayayyakin ga mai...