2025-05-25@15:49:15 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1690

«Ammar dan Yasir»:

    Kakakin rundunar, Wasiu Abiodun, ya ce an yi garkuwa da Ilya ne daga kauyen Gatawa tare da mahaifinsa.   Iliya da mahaifinsa dukkansu daga karamar hukumar Sabon-Birni ta jihar Sokoto. An yi garkuwa da su ne a cikin watan Afrilu, yayin da ‘yan bindigar suka mamaye kauyensu, suna ta harbe-harbe, inda daga nan ne ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su.     Ilya ya bayyanawa ‘yansanda cewa, ya tsere daga sansanin ‘yan bindigar ne bayan ya yi ta gudu a dajin har na tsawon kwanaki takwas sannan ya hadu da jami’an ‘yansanda a jihar Neja. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
    Jami’an da aka kashen da suka hada da Kwamandan CWC Mallam Sanusi, rahotanni sun bayyana cewa, suna cikin wani aikin kai dauki ne yayin da wasu ‘yan bindiga kusan ashirin (20) dauke da makamai a babura suka yi musu kwanton bauna a madatsar wani rafi.   A cewar wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan, Ibrahim Kaula ya fitar, maharan wadanda suka boye jikin bishiyar mangwaro, sun kona motar jami’an tsaro kirar Hilux a yayin harin.     Gwamna Radda ya samu rakiyar kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, Dr. Nasiru Danmusa; Kwamishinan ’Yansandan Jihar, Daraktan Ma’aikata na Jihar, Shugaban Ma’aikata, Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir; da sauran manyan jami’an tsaro.   Shugaban karamar hukumar, Alhaji...
    Jaridar ;The HIL’ ta kasar Amurka wacce take bada labaran majalisa da siyasar gwamnatin Amurka ta gargadi gwamnatin shugaba Donal Trump kada ta sake irin kuskuren da shugaban kasar Iran Sadam Hussain yaki na fadawa kasar Iran da yaki, tare da tsammanin cewa a cikin yan kwanaki zai ga faduwar jaririyar gwamnatin kasar Iran a lokacin. Amma sai wankin hula ya kai masa dare, inda ya share shekaru 8 yana fafatawa da mutanen kasar Iran ba kuma tare da samun nasarar ba. Jaridar ta kara da cewa Iran ba kasace wacce tana dab da faduwa ne sai aje a karasa faduwarta ba. Kasashen wacce kan mutanen kasar a hade yake a duk lokacinda na waje yayi kokarin mamayar kasar. Labarin...
    Shugaban Wanda Alhaji Ahmed Aliyu Zarma ya wakilta ya kara da cewa, wannan cibiya ba itace ta farko ba da shugaban ya fara ginawa ba, a cewarsa ya gina irinsu a sassa daban-daban a fadin kasar nan. Yana Mai Cewa, baya ga cibiyoyin koyar da addinin musulunci ya samar da makarantu a majami’un addnin kirista da gyaran makarantu da kuma tallafawa marayu da marasa galihu a cikin al’umma. Zarma ya ce, sama da shekaru goma shugaban yana gudanar da irin wadannan Ayyukan tallafawa Rayuwar al’umma musamman marayu da marasa galihu a fadin kasar nan Baki daya. Sarki Musulmi tare da Sarkin Zazzau a wurin taron A nasa jawabin, Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubukar lll Ya jinjiwa shugaban na DSS na...
    City ta ba da sanarwa a gabanin fafatawar cewa ta shirya wani babban kyalle mai dauke da sunansa tare da sanya wa wata hanya sunan De Bruyne a makarantar horarwa ta kungiyar, Guardiola yana girmama De Bruyne sosai har ya bayyana dan kasar Belgium din a matsayin dan wasan da ya fi iya kwallo a cikin ‘yan wasan da ya taba horarwa bayan Lionel Messi. De Bruyne ya fara buga wa City wasa a watan Satumban shekarar 2015, De Bruyne ya buga wasanni 283 a matakin farko, ya ci kwallaye 72 sannan ya taimaka aka zura kwallaye 119 wanda hakan ya sa ya zama na biyu a jerin wadanda suka fi kowa taimakawa wajen zura kwallo a gasar Firimiya bayan...
    A yau Asabar ne firaministan kasar Sin Li Qiang, ya sauka a birnin Jakarta domin ziyarar aiki a kasar Indonesia bisa gayyatar da shugaban kasar Indonesia Prabowo Subianto ya yi masa. Li ya bayyana cewa, kasashen Sin da Indonesia sun bayar da misali kan yadda manyan kasashe masu tasowa suke aiki tare don kara karfi da cin moriyar juna da kuma samun nasara ga kowane bangare. CHINADA Ta Nuna Matukar Adawa Da Gasar Wasannin Da Aka Amince Da Kwayoyin Kara Kuzari Yara Miliyan 2.9 A Nijeriya Ke Fama Da Rashin Abinci Mai Gina Jiki – UNICEF Ya ce, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da Indonesia don ci gaba da samar da wadata ga al’ummomin Sin da...
    Firaministan kasar Sin Li Qiang ya jagoranci taron majalisar gudanarwar kasar Sin, wanda ya amince da shirin aiwatar da ayyukan raya amfani da makamashi mai tsafta a bangaren masana’antu na shekarar 2025 zuwa ta 2027, tare da sake duba matakan da za a dauka na inganta tsarin biyan diyya domin kiyaye lafiyar muhalli. Taron ya jaddada bukatar hanzarta yin kirkire-kirkire na fasahohin makamashi mai tsafta da kuma fadada hanyoyin samar da mafita, yayin da ake kiran gudanar da gagarumin sauyi mai zurfi a bangaren tsoffin masana’antu. Har ila yau, ya bukaci sassa masu tasowa da su ci gaba da samar da ingantaccen ci gaba wajen amfani da makamashi mara gurbata muhalli tun daga tushe, tare da mai da hankali kan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kafin wasan ƙarshe na bana da za su kara da Crystal Palace a ranar Lahadi, Salah ya riga ya ci ƙwallaye 28 a Firimiyar bana kuma ya taimaka a ci wasu 18. Kusan taimako biyu kawai suka rage masa ya kai tarihin taimako 20 da Thierry Henry da Kevin de Bruyne suka kafa. A wannan kakar, Salah ya zama ɗan wasan da ba na Ingila ba da ya fi zura ƙwallaye kwallaye a tarihin Firimiyar Ingila, inda ya zarce ƙwallaye 184 da Sergio Aguero ya ci. Haka kuma ya sabunta kwantiraginsa da Liverpool har zuwa shekarar 2027. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
    Abin da ma yake faruwa kenan yanzu wallahi matasan nan maza! namiji babu sana’a babu isasshen ilimin zamani ke wallahi na addini ma wani babu sai ya tattago aure ko da yake an ce adashi suke shiga da an dauka sai zancen kai kudi karshe dai abar iyaye da wahala shi ya sa auren ma baya cin Litinin da Laraba an watse. Abin cewa nan yaro dai ya nutsu ya nemi sana’a da zai dogara da kansa sannan ya iya daukar nauyin iyali kuma a nemi karatu bakin iyawa. Su iyaye suna gujewa yaro abin da zai je ya zo ne ka dauko ‘yar mutane babu sana’a za a ci soyayya ne ina kai ba karatu ba sai kame-kame wani...
    Idan ajiyewa za ki yi sai ki samu roba mai murfi, ki rufe sosai saboda kada ta yi kwari. Yadda za ki tuka: Sai ki dora ruwa a wuta, ya tafasa ki dauko garin doyar, ki rage wuta kina zubawa da kadan-kadan kina tukawa har ya tuku, ki tabbatar bai yi kulalai ba duk kin tuke shi, sai ki dan zuba ruwa kadan ki daddanna ki rufe ki barshi ya yi kamar minti 15, sai ki sauke ki sake tukawa, ki samu leda ki kwashe abinki, shi kenan kin kammala. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
    Na yi imanin za mu iya hakan Kuma muna fasahar da za mu iya aiwatar da hakan? Idan aka yi la’akari da albarkatun noma da Nijeriya ke da shi, musamman a cikin amfanin gona irin su rogo da rake, da kuma ta hanyar saka hannun jari kan ababen more rayuwa da fasahar kere-kere, akwai gagarumin yuwuwar bunkasa damar samar da MSG na cikin gida ta hanyar amfani da wadannan albarkatun kasa da ake samu. Muna da injiniyoyi da yawa wadanda za su iya gyara injinan. Muna da dukkan abubuwan da ake bukata a Nijeriya don samar da kayan dandano. Yawanci muna samun abubuwan da duk da muke bukata. Idan kana bukatar ruwa mai yawa, muna da madatsun ruwa a Shiroro,...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya sallami ma’aikata da dama a majalisar tsaron kasar Amuka saboda gazawarsu wajen magance wasu al-amuran tsaro da siyasa a kasar. Tashar talabijin Ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran Rauters yana cewa ma’aikatan maimakon su magance al-amuran tsaro da suka shafi tsaron kasa, sai sun zauna suna jiran abinda shugaban zai fada don su yi aiki a kansa. Labarin ya kara da cewa shugaban ya dauki wannan matakin ne don ya mika wasu ayyukansu ga Pentagon da FBI da wasu ma’aikatun tsaro don magance wasu matsaloli masu muhimmanci a cikin sauri.
    Tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka JohnKerry ya bayyana cewa HKI bata isa ta wargaza cibiyoyin makamacin nukliya na kasar Iran ba. Kamfanin dilancin labaran IP na klasar  Iran ya nakalto Kerry na fadar haka a jiya, ya kuma kara da cewa babban al-amari a cikin duk wani kokari na kauda cibiyoyin Nukliyar kasar Iran ita ce yakin da zai biyo bayan wannan kokarin, Kerry yana magana ne don maida martani ga maganar cewa HKI tana shirin kai hare-hare ko yiyuwan ta kai harehare kan cibiyoyin nukliya kasar Iran idan ta ki amincea ta dakatar da tashe makamashiun uranium a cikin gida a tattaunawan da take da Amurka kan shirin nata. Labarin ya kara da cewa wannan yana tabbatar da...
    Rayuwa ta yi wa Talatu atishawar tsaki (ba sunanta na asali ba ne) tun daga shekarar 2018, bayan ta fada harkar shaye-shayen miyagun kwayoyi a lokacin da ƙawarta ta ƙwaɗaita mata yadda lamarin yake. Ta kasance yarinya mai hazaka mai kimanin shekara 29, kuma ta yi karatu a Jami’ar Kwatano har ta yi aiki a banki na tsawon shekaru biyu kafin ta yi aiki da Kamfanin NNPC da wasu manyan wurare. Sai dai harkar shaye-shaye ta sa ta siyar da motocinta guda biya da kwamfiyuta da wasu abubuwa masu mahimmanci. Halin da wakilin Aminiya ya tsince ta a ciki ke nan a Lungun Gurguwa da ke Lagas Street, Garki Abuja. Ta shaida masa cewa, sam ba ta jin dadin wanna...
    Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Abbas Arakci  wanda ya gana da takwransa na fadar Vatican ya yi kira da a kawo karshen  laifukan  da ‘yan mamaya suke tafkawa akan Gaza da gaggawa a kuma shigar da kayan agaji zuwa yankin. Ministan harkokin wajen na Iran wanda ya je kasar Italiya domin tattaunawar bayan fage da Amurka akan Shirin kasarsa na Nukiliya, ya ziyarci fadar Vatican, inda ya gana da ministanta na harkokin wajen Cardinal paul Gallagher, ya mika sakon ta’aziyyar rasuwar Fafaroma Farancis sannan kuma da murnar zabar sabon Fafaroma Leo na 14 Abbas Arakci ya yi wa shugabannin fadar ta Vatican bayani akan matsayar Jamhuriyar musulunci ta Iran dangane da shirinta na Nukiliya na zaman lafiya, da...
    Dan majalisar Amurkan mai suna Randall Adam Fine wanda yake wakiltar jam’iyyar “Republican”  ya sake tunanowa duniya  da yadda kasarsa Amurka ta jefa wa biranen Nagasaki da Hiroshima bama-baman Nukiliya a karshen yakin duniya na biyu, ta hanayr yin kira da a jefa wa zirin Gaza irin wadannan makaman na kare dangi. Kungiyoyin Falasdinawa mabanbanta sun yi tir da wannan irin kira na ci gaba da yi wa Falasdinawa kisan kare dangi, suna masu yin kira ga ita kanta majalisar Amurka da ta fito da yi Allawadai da wannan  kira wanda yake cike da kiyayya.” Kungiyar Hamas ta bayyana abinda dan majalisar na Amurka ya yi da cewa, ya keta dokokin kasa da kasa da kuma yarjejeniyar Geneva, kamar  kuma...
    A yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna ta wayar tarho da shugaban gwamnatin kasar Jamus Friedrich Merz, bisa gayyatarsa da aka yi. Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin da Jamus suna raya dangantakar dake tsakaninsu bisa girmama juna, da amincewa da bambance-bambance, da hadin gwiwa don samun moriyar juna, kuma akwai bukatar bangarorin biyu su yi kokari tare don tabbatar da raya dangantakarsu yadda ya kamata. Ya ce, da farko dai, ya kamata a yi imani da juna a fannin siyasa tsakanin kasashen biyu. Na biyu kuma, ya kamata a kara inganta dangantakarsu, wato ci gaba da hadin gwiwa a fannonin da suka riga sun hada hannu kamar su kera motoci, da injuna, da kuma masana’antar sinadarai...
    An dai fara goyon bayan tazarcen Tinubu a wurin taron lokacin da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, ya ce babu wani gurbi a fadar shugaban kasa a 2027. Barau ya ce, “A bayyane yake a 2027, za mu sami gagarumar nasara, In Sha Allah. Don haka, mu ci gaba da hanyar da muke kai. Mu hada kai da juna, mu yi aiki tare da shugaban kasa, mu yi aiki tare da kowa, mu hada kai a tsakaninmu don samun nasarar da ake bukata.” Sanata Barau ya ci gaba da cewa sauya shekan wasu shugabannin jam’iyyun adawa zuwa APC ya kasance sakamakon aikin Shugaba Tinubu a cikin shekaru biyu kawai da ya shafe a kan karagar mulkin Nijeriya. Kazalika, Ganduje...
    Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne shugaban kasar, Mr. Xi Jinping, a kwanakin baya ya yi muhimmin bayani game da aikin raya harkoki masu nasaba da wayewar kai a kasarsa, inda ya ce, ci gaban dukkanin fannonin samar da ababen more rayuwa da kuma wayewar kai, muhimmiyar alama ce ta zamantarwa mai salon kasar Sin. Shugaba Xi ya jaddada cewa, ya kamata a karfafa hadin kan jama’a bisa tunanin tsarin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin na sabon zamani, da mai da hankali kan wayar da kan al’umma, da sa kaimin raya al’adu da kuma da’a a tsakanin al’umma, sa’an nan kuma a karfafa ayyukan ba da jagoranci, da zurfafa yin gyare-gyare...
    Kotun kolin kasar Iraki ta yanke hukuncin kisa kan wani tsohon jami’in gwamnatin kasar kan laifin aikata kisa da kuma boye gawarwakinsu Kotun kolin kasar Iraki ta yanke hukuncin kisa a jiya Alhamis kan wani tsohon jami’in gwamnatin kasar kan laifin aikata kisan gilla da kishe-kashe kan ‘yan kasar da kuma boye gawarwakinsu a manyan kaburbura. A cikin wata sanarwa da majalisar koli ta shari’ar kasar Iraki ta fitar ta bayyana cewa: Kotun kolin manyan laifuka ta kasar Iraki ta yanke hukuncin kisa kan daya daga cikin jiga-jigan tsohuwar gwamnatin kasar Khairallah Hammadi Abd Jaru bisa laifin aikata kisan gillar da aka yi wa mutane 198 daga yankin Balad a shekara ta 1981, da kuma hannu a cikin aiwatar da...
    Don haka, ya zama dole kasashen Global South su hada kansu su dauki matakan dakushe duk wani radadi da matakin harajin da Amurka ta dauka zai haifar, ciki har da bunkasawa da inganta cinikayya tsakanin wadannan kasashe,ta hanyar hada kansu domin rage dogaro da tattalin arzikin Amurka ko na kasashen yammaci, wannan yunkuri zai bunkasa tattalin arzikin kasashen yankin Global South. Kasashen na Global South suna sake zayyana tsarin tattalin arzikinsu ta hanyar bayar da fifiko ga bunkasuwar tattalin arzikinsu da bayar da dama ta bai daya ga kowace kasa wajen taka rawa a harkar kasuwanci. Domin kuwa kasashen sun hade kansu wajen nuna turjiya ga wannan tsarin haraji na Amurka.   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
    Daga Bello Wakili Dukkan ‘yan majalisun tarayya daga Jihar Katsina sun bayyana goyon bayansu ga Gwamna Umar Dikko Radda domin ya sake tsayawa takara a wa’adin mulki na biyu karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben shekarar 2027 mai zuwa. An bayyana wannan matsaya ne a lokacin wani taron hadin gwiwa da ‘yan majalisar suka gudanar, inda Honourable Sada Soli, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Jibia da Kaita, ya yi magana a madadin takwarorinsa. Ya bayyana cewa wannan shawara ta samo asali ne daga nazarin hadin gwiwa da suka yi kan nasarorin da gwamnan ya samu da kuma goyon bayan da al’ummar jihar suka nuna daga kowane bangare. ‘Yan majalisar sun yaba da irin salon shugabanci na Gwamna...
    An dai haifi Dakta Mubarak a Unguwar Hausawa Masallacin Murtala, da ke Karamar Jukumar Kumbotso ta Jihar Kano a Nijeriya. Ya yi karatun Firamare a Hausawa Model ta Jihar Kano; ya yi karatu a Kwalejin Kimiyya ta jeka ka dawo a Kano; daga nan ya tafi zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudi, inda a nan ne ya samu digiri na farko. Ya samu digiri na biyu a fannin noma da gandun daji; sannan ya samu digirin-digirgir kan Agro Paris Tech, Paris, a Kasar Faransa, ya sake yin karatun digiri na biyu a fannin sanin yanayi, Amfanin Kasa da Ayyuka na Muhalli; ya kuma samu digirin-digirgir a Jami’ar Paris a fannin Ecology. Ya yi aiki a...
    A halin yanzu, jihohin da ke saman tebur wajen samun kyauttuka sun haɗa da Legas, Ogun da kuma Birnin Tarayya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Tsohon abin da ake zargin Sanata Natasha – duk karya ne,” in ji Obinna a fili. Har yanzu babu wata sanarwa daga ‘yansanda kan lamarin kama Obinna ya haifar da fushi a tsakanin masu fafutukar kare ‘yancin kafofin watsa labarai, waɗanda ke ganin harin ne kan ‘yancin faɗin albarkacin baki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    ’Yan Najeriya daga kowane ɓangare daban-daban sun caccaki jam’iyyar APC bisa yanke shawarar goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2027, duk da cewa shekararsa biyu kacal da hawa mulki. Wasu na ganin matakin ya nuna rashin tausayi da rashin damuwa da halin ƙuncin da al’umma ke ciki. Cutar lamoniya ta kama alhazai 99 ’yan ƙasar Indonesiya a Saudiyya NAJERIYA A YAU: Dalilin ’Yan Adawa Na Ƙulla Ƙawance A Ƙarƙashin Inuwar ADC Jagororin jam’iyyar APC, gwamnoninta da ’yan majalisa ne suka fito suka nuna goyon bayansu ga Tinubu. Amma jama’a na ganin hakan na nuna burin ci gaba da riƙe madafun iko ne kawai, ba wai taimakon talakawa ba. Ra’ayoyi daga sassa...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    El-Rufai ya yi kira ga alkalai da lauyoyi da su ji tsoron Allah su koma kan asalin aikin da ke gabansu tare da himmatuwa wajen wanzar da adalci da gaskiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa da Amurka da HKI sun san cewa zasu sami nasara a kan kasar Iran da yaki da tuni  sun fadawa kasar sun kuma mamayeta. Amma saboda wannan tsoron ne suka zabi tattaunawa da ita a kan shirinta na makamshin nukliya. Sannan Shirin makamacin nikliya ma daya ne kacal daga matsalolin da ke tsakanin Iran da HKI da kuma kasashen yamma musamman Amurka.  Ya ce akwai matsaloli da dama, tana jirin ta kamala da gudu don ta bullo da wata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya da yamma ya kuma  kara da cewa, manufar Iran ta shiga tattaunawa da Amurka ita ce,...
    Wani dan majalisar dokokin kasar Amurka daga jam’iyyar Republican daga jihar Florida Randi Fine ya bukaci gwamnatin Amurka ta yi amfani da dimbin makaman N uklkiya da ta tara don kawo karshen yaki a gaza, ta kashe dukkan Falasdinawa a lokaci guda a huta. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Fine yana fadar haka a wata hira da ta hadashi da tashar talabijin ta Foxnews a jiya Alhamis. Ya kuma  kara da cewa Amurka bata shiga tattaunawa da sojojin Nazi a yakin dunbiya na biyu ba, bata kuma yi kome bas ai da ta yi amfani da makaman nuklioya a kan Hiroshima da kuma Nagasafi sai kasar Japan ta mika kai ba tare da wasu matsala ba....
    Mataimakin limamin Jumma’a a nan Tehran Sheikh kum Hujjatul Islam Kazen Sadiki bayan yayio Magana a kan al-amuran tsaron All..da kuma yadda bayin All..da kuma shidanun mutane zasu mutu da kuma yadda sakamakon ko wannansu a gaban All…/ Ya kuma ya gamanar fatahin garin KharramShahr dake kudancin kasar Iran kuma kan iyaka da kasar Iran, wanda dakarun kare juyin juya halin musulunci tare da sauran sojoji da mayakan sa kai suka kwace wannan garin daga hannun sojojin Sdam Hussain a rana irin ta yau wato 2 ga watan Khordod. Banda haka lamamin yana Magana kan littafan da aka buga dangane da wannan gagarumin fatahin da mutanen Iran suka sami a kan wannan garin. Wanda kuma daga wannan nasarar ne ta...
    Shugaban babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Umar Iliya Damagun, ya yi Allah Ya isa ga masu zargin da yi wa jam’iyya mai mulki, APC, aiki. Wasu masu ruwa da tsaki a PDP na zargin cewa Damagun da  yi wa jam’iyyar zagon ƙasa APC, shi ya sa yake rura wutar rikicin cikin gida da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a PDP. Amma a yayin wata hira da ya yi da BBC, Damagun ya yi fatali da zargin, yana mai cewa Allah Zai saka masa tsakaninsa da masu yi masa wannan ƙazafi. “Allah Ya isa tsakanina da duk wanda ya yi min wannan ƙazafi, kuma Allah Zai yi mana shari’a,” in ji shugaban na PDP, wanda ake zargi da zama ɗan-amshin-shatan...
    Bincike ya yi nuni da cewa an bar dukkan al’ummomi ba tare da ingantattun makarantu ba a jihohi kamar Borno, Yobe, da Adamawa. Sama da makarantu 1,500 ne aka lalata tun farkon rikicin Boko Haram, inda sama da malamai 19,000 suka rasa matsugunansu, kuma da yawa ma suna fargabar komawa. ‘Yan mata suna cikin hadari, galibi ana tilasta musu auren wuri ko aikin gida ko aikin jima’i maimakon a ba su damar koyo. Wata kwararriyaa fannin ilimi da ke zaune a Jos, Jihar Filato, Misis Peace Pernam, ta ce, “Ilimi wata hanya ce ta rayuwa mai muhimmanci da ke kawar da fatara, rage matsalar tsaro, da samar da ci gaban kasa, duk da haka, ga miliyoyin yara a yankin Arewa...
    ‘Yan sama jannatin kumbon Shenzhou-20 dake cikin tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin dake cikin da’irarta, sun kammala jerin ayyukansu na farko a wajen tashar a yau Alhamis. Hukumar kula da ayyukan sama jannati ta kasar Sin (CMSA) ta ce, ‘yan sama jannatin da suka hada da Chen Dong da Chen Zhongrui da Wang Jie, sun yi aiki na tsawon sa’o’i 8, inda suka kammala da misalin karfe 4:49 na yamma agogon Beijing, bisa taimakon takwarorinsu dake duniyar dan Adam. Chen Dong da Chen Zhongrui ne suka yi aiki a wajen tashar, inda suka fita ta hanyar dake jikin kumbon Tianhe. Wannan shi ne karo na farko da ‘yan sama jannati suka fita ta hanyar tun bayan da tashar...
    MDD ta bayyana cewa; Da akwai damuwa mai zurfi akan halin da ‘yan Hijirar Sudan suke ciki a gabashin kasar Chadi saboda rashin masu bayar da kudaden taimakon kula da su. Ma’aikatan MDD a fagen ayyukan ceto sun ce ana samun kwararar ‘yan hijira daga Sudan zuwa gabashin kasar ta Chadi, da kuma ‘yan kasar ta Chadi da suke komawa gida. Tun da yaki ya barke a Sudan zuwa yanzu an yi rijistar kwararar ‘yan Sudan masu yawa. A cikin wata daya kadai ‘yan Sudan  su dubu 55, sai kuma ‘yan asalin Chadi da su ka koma gida zuwa Jahar Inidy da yankin Fira, a gabashin kasar, da su kuma sun kai dubu 39. Sanarwar ta MDD ta ci gaba...
    A karo na biyu sojojin kasar Yemen sun sanar da kai hari akan filin saukar jirgin sama na “Ben Gorion” a matsayin ci gaba da taimakawa Falasdinawa da sojojin HKI suke yi wa kisan kiyashi. Sanarwar ta sojojin na Yemen ta kuma ce; Makami mai linzamin da su ka harba, wanda ya fi sauti sauri ne, kuma ya sauka a inda aka harba shi, wato filin jiragen sama na Yafa dake karkashin mamaya, da ake kira da “Ben Gorion.” Harin ya tilastawa miliyoyin ‘yan  sahayoniya guduwa zuwa Mabuya sanadiyyar gittawar makami mai linzamin da aka harbo daga kasar Yemen. Haka nan kuma an dakatar da zirga-zirgar jirage a filin na Ben Gorion. Da safiyar yau ma dai kakakin sojan kasar...
    A jawabinsa yayin Kaddamar rabon kayan Sanata Muhammadu Adamu Aliero ya bayyana cewa “Komawar mu jam’iyyar APC ya nufin kawar da adawa don samar da ci gaba a jihar Kebbi, kuma zamu yi hadin gwiwa da gwamnatin, Gwamna Nasir Idris don amfanin mutanenmu ga irin ayyukan da ya gudanar a dukkan kananan hukumomin 21 na jihar, Wanda shi ne muke kira a ko da yaushe cewa a samar da cigaba ga jama’ar da muke shugabanta,” Inji Sanata Muhammadu Adamu Aliero. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
    An kashe ma’aikatan ofishin jakadancin haramtacciyar kasar Isra’ila biyu a birnin Washington na Amurka Kafofin yada labaran Amurka sun rawaito cewa: An kashe ma’aikatan ofishin jakadancin haramtacciyar kasar Isra’ila biyu bayan da aka harbe su a wajen dakin adana kayan tarihi na Yahudawa da ke birnin Washington D.C. na Amurka. Kafofin yada labaran Amurka sun rawaito sakataren tsaron cikin gida na Amurka na cewa: An kashe ma’aikatan ofishin jakadancin haramtacciyar kasar Isra’ila biyu a kusa da gidan adana kayan tarihi na Yahudawa da ke birnin Washington, inda ake gudanar da taron kwamitin Yahudawa na Amurka (AJC). Jim kadan bayan harbin, ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da cewa an kama wanda ake zargin. Kamfanin dillancin labarai na NBC ya bayar...
    Shuwagabannin Amurka da Afirka ta Kudu sun yi arangama kan zargin kisan kare dangi a Afirka ta Kudu Fadar White House ta shaida wata zazzafar musayar wuta tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, wanda ya musanta zargin da ake masa na cewa Pretoria na cin zarafin ‘yan kasar fararen fata. An yi ganawar ne mako guda bayan da Trump ya yi zargin cewa gwamnatin Afirka ta Kudu na yin kisan kiyashi ga ‘yan kasarta ‘yan asalin Turai. A yayin tattaunawar da ta samu halartar jami’ai daga bangarorin biyu, shugaban na Amurka ya bukaci ma’aikatansa da su nuna masa faifan bidiyo da ke da alaka da zargin kisan kiyashin, sannan Ramaphosa ya kuma mika...
    Ya kuma ce suna sane da cewa yajin aikin zai iya shafar jama’a musamman a Katsina. “Ba ma’aikata kaɗai muke ba – iyaye ne mu kuma masu ciyar da iyali. Abin da muke nema kawai haƙƙinmu ne,” in ji shi. Yajin aikin zai iya haifar da tsaiko wajen samun wutar lantarki a yankin, musamman a Katsina inda yajin aikin ke da zafi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sanata mai wakiltar Kebbi ta tsakiya, Sanata Muhammad Adamu Aleiro, ya raba wa al’ummar mazabar sa kayan tallafi da nufin ba su damar dogaro da kai.   Kayayyakin sun hada da babura 150 (Keke NAPEP), babura 114, firiza mai zafin rana guda 302, injin nika 750, famfunan ruwa mai amfani da hasken rana 500, injin dinki 800 da kuma buhunan taki 3,400.   Da yake jawabi a wajen bikin raba kayayyakin a karamar hukumar Aleiro ta jihar Kebbi, Sanata Adamu Aleiro, ya ce hakan na daga cikin romon dimokuradiyya ga al’ummar mazabarsa kadai, har ma da jihar.   Sanata Aleiro, ya lissafo wasu ayyukan da ya aiwatar a matsayin aikin mazabu a kananan hukumomi takwas na mazabarsa da suka hada...
    Bayan sabon farmakin da Isra’ila ta kai a zirin Gaza, kasashen Yamma na kokarin kara matsin lamba kan Isra’ila, wacce ta kauda kai kan kiraye kirayen da duniya ke yi na ta dakatar da yakin a Gaza. Kungiyar ta EU, ta kara mastin lamba ta hanyar sake nazari kan yarjejeniyarta da Isra’ila ta tsawon shekaru 25 dake a tsakaninsu. Tunda farko dama kasashen kasashen Canada-Faransa da Ingila  sun sanar da yin Allah wadai da farmakin kasa na soja na sojojin Isra’ila a Gaza. Baya ga hakan kuma Birtaniyya a ranar Talata ta sanar da kawo karshen yarjejeniyar ciniki cikin ‘yanci da Isra’ila. Ita ma kiasar Sweden, ta yi kira da a kakaba takunkumi ga membobin gwamnatin Isra’ila. Bayanai sun ce...
    Masana sun yi kira ga hukumomi da su yi bincike mai zurfi don gano waɗanda ke taimaka wa Boko Haram sannan a hukunta su domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin Arewa maso Gabas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rukunin ƙarshe na mahajjatan Jigawa 368 ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Nuhu Muhammadu Sunusi zuwa Saudiyya don aikin hajjin shekarar 2025. A wata hira da aka yi da shi a Radio Nigeria kafin tashinsu a daren Laraba, Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya bayyana cewa rukunin ƙarshe na mahajjatan 368 sun fito ne daga ƙananan hukumomin Birnin Kudu, Buji, da Taura na jihar. A cewarsa, wannan rukunin ƙarshe ya haɗa da Amirul Hajj na jihar, malamai  masu wa’azi, wasu jami’an shiyyoyi da cibiyoyi, da kuma wasu jami’an hukumar. Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana cewa, jihar ta kammala aikin tantance mahajjata cikin nasara ba tare da wata tangarda ba. Ya yabawa Gwamnan jihar, Malam Umar...
    Sahun ƙarshe na mahajjata 140 daga jihar Kwara, ciki har da jami’an NAHCON, da ya tashi daga filin jirgin sama na Babatunde Idiagbon da ke Ilori ya isa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2025. Yayin jawabi ga mahajjatan kafin tashin su da misalin ƙarfe 6:42 na yammacin Laraba, Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai na Jihar Kwara, Farfesa Mashood Mahmud-Jimba, ya shawarci mahajjatan da su kasance masu ɗabi’a a lokacin da suke kasa mai tsarki. Farfesa Mahmud-Jimba ya bayyana cewa an shirya duk abin da ya dace domin tabbatar da cewa mahajjatan sun gudanar da aikin hajji ba tare da wata matsala ba. Ya kuma shawarce su da kada su yi ayyuka masu wahala domin samun damar shiryawa...
    Duk da cewar bai buga wasa ko daya a gasar AFCON da ta gabata ba, wannan karon ana saran Musa zai kasance daga cikin wadanda zasu haska a gasar ta Unity Cup da kasashe zasu buga a Landan.   Za a gudanar da gasar cin kofin Unity Cup wanda ya kunshi Nijeriya, Jamaica, Ghana da kuma Trinidad and Tobago a filin wasa na Gtech Community mai daukar yan kallo 17,250 da ke Brentford a yammacin Landan, za a fara gasar ne da wasan kusa da na karshe a ranar Talata 27 ga watan Mayu, yayin da Trinidad & Tobago za ta kara da Jamaica, Washegari Nijeriya mai rike da kofin Afirka sau uku za ta fafata da Ghana mai rike...
    Ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai a yau Laraba, inda jami’in ma’aikatar kasuwancin kasar da ke da ruwa da tsaki ya bayyana cewa, aiwatar da matakan da suka dace bisa “Ayyuka guda goma” na hadin gwiwa da Afirka, ya haifar da sakamako mai kyau, wanda ya zuba babban kuzari ga hadin gwiwar Sin da Afirka. Mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin Tang Wenhong ya bayyana cewa, an riga an tattauna tare da kasashen Afirka sau da dama, an kuma amince da tsarin “Kasa daya, manufa daya” wajen tsarawa da aiwatar da matakai. Rashin Tsaro: Matasa Sun Yi Zanga-zangar Toshe Babbar Hanya Saboda Satar Mutane A Edo Za A Gudanar Da Baje Kolin...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi tattalin arziki zamantakewa ysaro da sauransu, sannan mu yi masu karin bayani daga karshe kuma mu ji ra’ayin masana dangane da su. Dafatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ///…Masu sauraro shirimmu na yau zai yi magana dangane da tattaunawa    tsakanin JMI da kuma Amurka dangane da shirin nukliyar kasar Iran na zaman lafiya. Wanda ya zuwa yanzu an gudanar zagaye na 4 na tattaunawar. Har zuwa wannan lokacin dai dukkan bangarorin suna fadar cewa ana samun ci gaba a tattaunawar. Amma bayan kwanaki da        ...
    Kwamiti mai kula da al-amuran harkokin waje a kasar Burtaniya tana matsawa sakataren harkokin wajen kasar David Lammy kan cewa ya amince da kasar Falasdinu mai zaman Kanata. Jaridar Telegram ta kasar Burtaniya ta nakalto wannan rahoton a yau Laraba, ta kuma kara da cewa Dan majalisa Emily Thomberrry ya kara da cewa wannan mataki na farko ne, idan Lammy ya bada wannan sanarwan a cikin wata mai zuwa a lokacin haduwarsa da Saudiya da Faransa a wani babban taro wanda zai bada damar daukar matakai nag aba. Jaridar tace, wannan maganar tana zuwa ne bayan da sakataren ya dakatar da tattaunawa ta harkokin kasuwanci da HKI, da kuma kiran jakadan HKI a London don gabatar da korafinsa kan sake...
    Amma kuma kariyar ciniki ba za ta taimaka ga raya sana’o’i da masana’antu a duniya ba. Idan mun lura, a cikin shekaru 10 da suka wuce, yadda kasar Amurka ta dauki matakai na kare sana’o’in samar da karafa, a maimakon ya hana raguwar guraben ayyukan samar da karafa, sai ya haifar da karuwar kudaden da sana’o’i masu alaka suka kashe. Haka al’amarin yake ma ta fannin samar da sassan na’urorin laturoni na Chips da fasahohin kirkirarriyar basira, domin rashin yin takara da hadin gwiwa da sauran kasashe ba zai haifar da da mai ido ba, illa koma baya da illoli ga sana’o’i masu alaka. A bangaren kasar Sin kuma, yadda kasar Amurka ke yi mata kafar ungulu don dakile ci...
    Mai ba da shawara ga jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Kalamai masu karo da juna na Trump da mataimakansa sun zubar da kwarin gwiwa ga gwamnatin Amurka Mai bai wa Jagoran juyin juya halin Musulunci shawara ya bayyana cewa: Sabani da ake ci gaba da yi a cikin maganganu da ayyukan Trump da takwarorinsa na haifar da rashin amincewa da gaskiyar gwamnatin Amurka. Ali Akbar Velayati mashawarcin Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya yi tsokaci a cikin wani sako da ya wallafa a dandalin X kan kalamai masu cin karo da juna da jami’an Amurka suka yi. Mai bai wa Jagoran juyin juya halin Musulunci shawara ya ce ci gaba da cin karo da juna...
    Sakataren harkokin wajen Amurka ya bayyana cewa: Gwamnatin rikon kwaryar Siriya na iya rugujewa cikin ‘yan makonni Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa: Gwamnatin rikon kwarya a Siriya na iya rugujewa cikin ‘yan makwanni, lamarin da zai sa kasar ta fada cikin yakin basasa matukar Amurka ba ta ba ta hadin kai ba. A yayin zaman Majalisar Dattijan Amurka, Sakataren harkokin wajen kasar Rubio ya yi furuci da cewa: Idan Amurka ta yi aiki da gwamnatin Siriya, yana iya yiwuwa, gwamnatin ta samu nasara, ko kuma gwamnatin ta kasa samun nasara idan Amureka ba yi aiki da ita ba, kuma tabbas ba zata taba samu nasara ba. Ya kara da cewa: “A hasashen Amurka, idan aka yi...
    Babban Mufti na kasar Oman ya bayyana cewa: Matakin taron kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ya fi kankara sanyi da rashin muhimmanci Babban Mufti na masarautar Oman, Sheikh Ahmed bin Hamad Al-Khalili, ya jaddada yabonsa ga fitaccen matsayi na kasar Yemen da kuma matsin lamba da dakarun kasar Yemen suke yi na kai kayan agaji a zirin Gaza. A gefe guda kuma, ya nuna rashin jin dadinsa da raunin kudirin taron kasashen Larabawa kan daukan matakan matsin lamba kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da take aiwatar da kashe-kashen gilla kan al’ummar Falasdinu. A wani rubutu da ya yi a dandalin X, Al-Khalili ya bayyana godiyarsa ga jaruman kasar Yemen da kuma kasashen da suka bayar da gudumawa wajen matsin lamba...
    Sojojin Sudan sun karbe iko da sansanin dakarun kai daukin gaggawa na karshe a birnin Khartoum fadar mulkin kasar Sojojin Sudan sun ci gaba da dama a jihohin Kordofan da Darfur, inda suka bar birnin Nahud da ke yammacin Kordofan, wanda sojojin suka killace birnin ta kowane bangare. Sojojin Sudan sun samu nasarar karbe ikon yankin Atrun mai mahimmanci a Arewacin Darfur, tare da bude hanyar shiga sauran garuruwan Darfur gaba daya. Bayan kazamin fada tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces a yankin Al-Saliha da ke kudancin Omdurman, wanda ya dauki tsawon sama da wata guda ana gwabzawa, sojojin sun samu nasarar mamaye yankin gaba daya, sai dai wasu kananan yankuna da sojojin ke...
    Kwamishinan ‘yansandan Jihar Kebbi, CP Bello M. Sani, ya yaba da ƙoƙarin jami’ansa kuma ya umarci a miƙa lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuka (SCID) domin zurfafa bincike. Bayan binciken, za a gurfanar da su a kotu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sanatocin jihar Kebbi guda uku da suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC, tare da Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Sanata Atiku Bagudu, sun bukaci hadin kai tsakanin mambobin jam’iyyar domin samun nasara a zaben 2027. Sanata Adamu Aliero, wanda ya yi jawabi a madadin sauran sanatocin, ya bayyana haka a wani taron jiga-jigan jam’iyyar APC da reshen jihar ya shirya a Birnin Kebbi. Sanata Aliero ya ce sauya shekar su daga jam’iyyar adawa PDP zuwa jam’iyya mai mulki APC, domin cigaban jihar ne gaba ɗaya. A cewarsa, akwai ayyuka da dama da za a aiwatar a jihar Kebbi, amma saboda wakilan jihar a majalisa suna jam’iyyar adawa, aka hana jihar damar cin gajiyar wadannan ayyukan. Game...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A bana ake cika shekaru 80 da kawo karshen yakin duniya na II da ma dawowar yankin Taiwan karkashin ikon babban yankin kasar Sin, wadda nasara ce da babu wanda zai goyi bayan lalata ta, sai masu neman cimma wani buri na kansu. La’akari da shekarun da aka shafe, da tsayawar kasar Sin tsayin daka kan tabbatar da iko kan yankunanta, ya kamata yankin Taiwan da masu tunzura shi su fahimci cewa, suna bata lokacinsu domin manufar kasar Sin daya tak, manufa ce da ta samu amincewar kasa da kasa kuma babu wanda zai iya sauyata. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
    Mahaifinta, Everistus Nnadozie, ya ce an sanar da shi cewa surukinsa Esosa Imasuen ne ya yi wa ‘yarsa duka har ta samu raunika sosai. Ya ƙara da cewa an kai ta asibiti inda likita ya tabbatar da cewa tana fama da zubar jini a cikin jikinta. Ya ce kafin ya isa asibitin, ‘yarsa ta rasu. Bayan haka kuma, Esosa ya ɗauki gawarta ya kai wani waje ba tare da ya sanar da iyayenta ba. “Na je gidansa, sai aka ce ya tsere,” in ji mahaifin. Ya ce yana ta kiran Esosa domin ya nuna masa inda aka kai gawar ‘yarsa, amma ya ƙi amsa waya. Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Edo, ya ce sun duba wurare da dama...
    Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana cewa ya zama wajibi ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da yaki da rashin tsaro a kafatanin kananan hukumomi ashirin da biyar na jihar   Kwamishinan Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida na Jihar Neja, Birgediya Janar Mohammad Bello Abdullahi, ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga manema labarai a taron shirye-shiryen babban taron tsaro da za a gudanar a Minna.   Janar Mohammad Bello Abdullahi ya kara da cewa Gwamnati jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da rashin tsaro, inda ya bukaci hadin gwiwa daga kowane bangare domin cimma burin da aka sanya a gaba.   A cewarsa, babban taron zaman lafiya da tsaro na farko da za...
    A ziyarar da ya kai jerin kogon Longmen, mai shekaru sama da 1,500 wanda UNESCO ta sanya cikin jerin wuraren tarihi da aka gada na duniya, wanda kuma shi ne ke wakiltar matsayin koli na fasahar sassaka kan dutse ta kasar Sin, shugaban ya bayyana muhimmancin karewa da gado da ma yayata al’adun gargajiya na kasar Sin masu daraja. (Fa’iza Mustapha)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
        Cikakkue bayanai daga baya… Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama wasu mutum shida da ake zargi da aikata fashi da makami tare da ƙwato motocin sata guda huɗu, bayan wani samame da suka kai. Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce sun samu nasarar ne a ranar 10 ga watan Mayu, 2025, inda tawaga ta musamman ƙarƙashin jagorancin CSP Rabiu Gidado ta kama wani da ake zargi, Saidu Abubakar, a Jihar Filato. Malamai sun gindaya sharaɗi kafin janye yajin aiki a Abuja  An kama ɗan bindiga a hanyar zuwa aikin Hajji a Sakkwato An same shi da wata mota ƙirar Toyota Corolla samfurin 2016 da aka sace wa wani mazaunin unguwar Naibawa a Kano. Yayin gudanar da bincike, Abubakar ya amsa cewa...
    A yau Talata shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasikar bude dandalin hadin gwiwa na Shanghai ko SCO na 2025, game da rage talauci da wanzar da ci gaba, wanda ke gudana a birnin Xi’an, na lardin Shaanxi dake arewa maso yammacin kasar Sin. Cikin sakon na sa shugaba Xi ya bayyana cewa, rage talauci wanda batu ne da ya shafi duniya baki daya, buri ne na daukacin kasashen duniya. Ya ce duk da cewa aiki ne mai matukar wahala, amma duk da haka kasar Sin ta cimma nasarar rage shi daidai da ajandar samar da ci gaba mai dorewa ta MDD ta nan zuwa shekarar 2030, shekaru 10 gabanin wa’adin karshe na ajandar. Hakan ya shaida ingancin...
    Ya misalta rashin basaraken da cewa, ba rashin ne kawai ga iyalai ko al’ummar masarautarsa ba, a’a rashi ne ga illahirin masarautar Bauchi da ma jihar Bauchi baki ɗaya.   Gwamna Muhammad ya misalta Alhaji Garba a matsayin babban basaraken gargajiya wanda aka sani da hikima, tawali’u, da sadaukar da kai ga hidimta wa al’ummarsa.   “Ya kasance mutum mai dattako wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen kyautata zaman lafiya da cigaba,” in ji gwamna Bala.   Gwamnan sai ya yi addu’ar Allah ya jiƙan mamacin ya gafarta masa kura-kuransa tare da sanya shi cikin aljanna maɗaukakiya. Ya kuma jajanta wa masarautar Bauchi, iyalai da al’ummar jihar da fatan Allah ba su haƙurin juriya na wannan babban rashin.. ...
    Mahajjata da jami’ai sun yaba da wannan gaskiya da rikon amana. Wasu sun ce hakan ya ƙara musu ƙwarin gwiwa ga tsaron mahajjata da amincin tsarin aikin hajji. “Alhamdulillah, Hajiya ta samu kuɗinta gaba ɗaya,” in ji wani jami’in sansanin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta da wani yanki na siyasa mai zaman kansa Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Yahudawan sahayoniya ba su da wata kafa ta siyasa mai cin gashin kanta, a maimakon haka dole ne a fahimci matsayinsu geopolitical bisa tsarin mulkin Amurka. A jawabin da ya gabatar a wajen rufe taron tattaunawa na Tehran a jiya litinin, Qalibaf ya kara da cewa: A fagen siyasar kasa, siyasa ba ita ce kullin nauyi ba, a maimakon haka, labarin kasa shi ne ginshikin da siyasa ta ginu a kansa a matsayin wani mataki mai girma. Ya bayyana cewa: Idan ana magana game da ababen...
    Wani harin kwanton bauna da rundunar sojin al-Qassam suka kai kan sojojin mamayar Isra’ila a Beit Lahiya ya yi sanadiyar halaka tare da jikkatan sojojin mamaya masu yawa Rundunar Izzuddeen al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, ta sanar da cewa: Mayakanta sun kai wani kazamin harin kwantan bauna a yankin al-Atatra da ke yammacin Beit Lahiya a arewacin zirin Gaza, inda suka yi nasarar ritsawa da sojojin mamaya masu yawa da suka yi sanadaiyyar halakar wasu daga cikinsu bayan jikkata wasu da dama. Rundunar ta Al-Qassam ta ce: Mayakanta sun kai hari kan motocin sojin mamayar Isra’ila uku da bama-baman Shawaz guda biyu da kuma makami mai linzami, sannan kuma suka yi arangama da wata rundunar mamayar Isra’ila....
    Akalla Falasdinawa 38 ne suka rasa rayukansu a wani jerin hare-haren jiragen yaƙin Isra’ila da aka kai a sassa daban-daban na Gaza cikin rabin sa’a da dare, in ji likitocin Falasɗinawa. Rahotanni daga hukumar agajin gaggawa da ke ƙarkashin Hamas sun ce jiragen yaƙin Isra’ila sun kai hari a wurare da dama, ciki har da wata makaranta a gabashin birnin Gaza, da kuma wani tsohon gidan mai a sansanin ’yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza, inda iyalai da dama ke neman mafaka. Hukumar ta ƙara da cewa tawagar ceto na fuskantar matsaloli wajen kai ɗauki ga waɗanda suka jikkata saboda ƙarancin kayan aiki da kuma tsananin harin. Wannan hari ya biyo bayan umarnin kwashe jama’a gaba ɗaya...
    Gwamnatin kasar Masar na shirin yin arangama ta soji da haramtacciyar kasar Isra’ila Kafofin yada labaran Isra’ila, musamman tashar talabijin ta 14, sun watsa wani rahoto cewa: Gwamnatin kasar Masar na kokarin karfafa karfinta na soji a tsibirin Sinai, tana mai gargadin abin da ta bayyana a matsayin “yiwuwar rugujewar yarjejeniyar zaman lafiya” da aka rattaba hannu tsakanin kasashen biyu a shekara ta 1979. Tashar talabijin ta NAN ta nakalto Eliyahu Dekel, tsohon shugaban hukumar leken asirin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila kuma masani kan al’amuran Masar na cewa: Masar na cikin gaggawar shirin tunkarar rikicin soji, yana mai cewa “yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla tsakanin kasashen biyu a shekarar 1979 ta kasance cikin yanayi na rugujewa tun lokacin da...
    Mutane sun koma kwana a cikin jejin a sakamakon hare-haren ’yan bindiga a yankin Ƙaramar Hukumar Ƙaura Namoda da ke Jihar Zamfara. Mazauna yankunan sukan dawo cikin gari su yini, idan dare ya yi kuma su shiga daji su kwana, sakamakon ƙaruwar hare-haren ’yan ta’adda, inda suka kashe mutum huɗu suka yi garkuwa da wasu 26. Wani mazaunin Ƙauran Namoda da ya buƙaci a ɓoye sunansa ya ce adadin mutanen zai iya cin haka, inda ya tabbatar cewa maharan sun kashe wata mata tare da sace wasu 26. Ya bayyana cewa daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su har da wani magidanci da matansa biyu da ’ya’yansa uku. An kama matar ɗan ta’adda Ado Aliero da mahaifiyarsa a cikin...
    Da yammacin jiya Litinin, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya ziyarci birnin Luoyang na lardin Henan. A yayin ziyarar, Xi ya ziyarci kamfanin Bearing Group na Luoyang, da gidan ibada na “Farin Doki”, da kuma ramin dutse na Longmen. Ya fahimci yadda aka inganta ci gaban masana’antun samar da kayayyaki a wurin, da karfafa kiyayewa, da amfani da abubuwan tarihi da al’adu, da habaka ingantattun masana’antun al’adu da yawon shakatawa da sauransu. (Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
    Wani jami’in hukumar, Ibrahim Muhammad, ya bayyana cewa tsare-tsaren da hukumar ta ɗauka sun taimaka sosai, inda komai ke tafiya cikin kwanciyar hankali a Saudiyya. An fara jigilar maniyyatan ne a ranar 9 ga watan Mayu 2025 a filin jirgin sama na Owerri da ke Jihar Imo. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kula da lafiya na nufin yin abubuwa da ke kare mutum daga kamuwa da cututtuka da kuma tabbatar da cewa jiki na aiki yadda ya kamata. Wannan ya haɗa da cin abinci mai gina jiki, motsa jiki akai-akai, da dai sauran su. Sai dai a wannan zamani ’yan Najeriya ba kasafai suke kula da lafiyar jikinsu ba, a mafi yawan lokuta ma sai ciwo ya kwantar da mutum sannan yake tunawa da likita. Ko waɗanne matakai ya kamata al’umma su ringa dauka wajen kare kansu da kuma lafiyar jikinsu? NAJERIYA A YAU: Mece ce Makomar Dimokuraɗiyya Idan Aka Wajabta Kada Kuri’a? DAGA LARABA: Tasirin Mulkin Karɓa-Karɓa A Najeriya Shirin Najeriya A YAU na...
    Bayan da mahukuntan kasar Sin suka kaddamar da yadda harkokin tattalin arzikin kasar suka gudana a watan Afrilun bana a ranar 19 ga wata, mataimakin shugaban zartaswa na kamfanin Novonesis na kasar Denmark, Morten Enggaard Rasmussen ya tattauna da wakilin CMG, inda a cewarsa, alkaluma sun nuna karfin tattalin arzikin kasar Sin. Ya ce Kamfaninsa zai ci gaba da fadada harkokinsa a sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko a kasar ta Sin. Haka kuma, kafofin yada labaru na kasa da kasa sun ce, yadda tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa ya wuce zaton mutane, suna cewa tattalin arzikin kasar Sin na da juriya da tabbaci. A watanni 4 na farkon bana, saurin karuwar muhimman alkaluma masu alaka...
    Jami’an Sashen Binciken Laifuka na Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Nasarawa (SCID) sun kama wani mai garkuwa da mutane a Kasuwar Shinge da ke Lafia, bisa rahotonnin sirri da suka samu. An samu nasarar cafke wanda ake zargin bayan shafe dogon lokaci  rundunar na nemasa ruwa a jallo saboda laifuka da dama da suka hada da garkuwa da mutane da kuma satar shanu. A yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa laifinsa, sannan ya jagoranci jami’an tsaro zuwa maboyarsa da ke kauyen Ruwan Baka a karamar hukumar Doma, inda aka samu bindiga kirar AK-49 mai lamba 453144 tare da alburusai. Wannan nasarar ta biyo bayan kama wata Fatima Salisu a ‘yan kwanakin baya, wadda aka tare tana jigilar makamai daga...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, yankin Taiwan na kasar Sin ba shi dalili ko iko ko kuma hujjar halartar babban taron hukumar lafiya ta duniya (WHA), har sai sai gwamnatin tsakiya ta kasar ta amince masa. Kakakin ma’aikatar ne ya bayyana haka yau Litinin, lokacin da yake tsokaci kan matakin da WHA ta dauka na kin sanya bukatar Taiwan ta halartar taron a matsayin ‘yar kallo, cikin ajandarta. A cewar kakakin, an shafe wani lokaci yanzu, hukumomin jam’iyyar DPP da wasu kasashe suna kokarin mayar da hannu agogo baya, inda suke kalubalanta da kokarin hargitsa kudurin MDD mai lamba 2758, domin kalubalantar manufar Sin daya tak a duniya. Ya ce, wannan ba kalubale ne ga cikkaken ‘yancin kasar...
    Shugaban kasar Lebanon Josept Aoun ya bayyana cewa gwamnatinsa tana son ta maida makamai a kasar Lebanon karkashin ikon hukuma kadai. Aoun ya ce kungiyar Hizbullah tana iya shiga harkokin siyasa na kasar Lebanon amma makamai na gwamnatin ne kadai. Jaridar ‘The National Ta Kasar Amurka’ ta n akalto shugaban yana fadar haka a kasar Masar a ganawarsa da tokwaransa na lasar Abdulfattah Assisi a yau Litinin. Aoun ya kara da cewa yana bukatar taimakon kasar Masar don gano ramukan da ake boye makamai a kasa. Sannan zai yi magana da shugaba Mahmood Abbas na Falasdinawa kan yadda za’a karbe makaman da suke hannun falasdinawa a sansanoninsu na yan gudun hijira da ke Ainul Helwa kusa da garin Saida na...
    Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Na’im Kasim a wani jawabinda da ya gabatar don tunawa da cika shekara guda da shahadar shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi da abokan tafiyarsa, ya bayyana cewa shugaban ya kasance mai  kaunar falasdinawa ne har cikin zuciyarsa. Sheikh Qasim ya kara da cewa, shugaba Ra’isi ya rike makamai da dama a rayuwarsa a JMI amma wannan bai canza  shi ba, ya kasance yana tambaya ta dangane da gwagwarmaya da HKI a yankin Hizbullah da kuma sauran mujahidai a yankin. A lokacin shugabancinsa ya taimakawa kungiyar Hizbullah, sosai kamar yanda wadanda suka gabaceshi suka yi. A ranar 20 ga watan Mayun shekarar da ta gabata ce. Sayyid Ibrahim Ra’isi shugaban kasar Iran yayi...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ba da umurni kan babban shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin karo na 15, inda ya nanata wajibcin tsai da shiri bisa halin da ake ciki, matakin da ya kasance muhimmiyar dabarar jam’iyyar kwaminis ta Sin wato JKS a fannin gudanar da harkokin kasa, kuma fifiko a siyasance na tsarin mulkin gurguzu mai salon musamman na Sin. Xi ya ce tsai da babban shiri na 15 na da babbar ma’ana ga tabbatar da manyan tsare-tsare da aka tanada a yayin babban taro karo na 20 na JKS, da gaggauta zamanantar da al’ummar Sinawa. Don haka dole ne a samar da shiri bisa halin da ake ciki, bisa tushen demokuradiyya...
    Aƙalla mutum uku aka kashe, yayin da aka sace 26 a wani sabon harin da ’yan bindiga suka kai yankin Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda, a Jihar Zamfara. Harin ya faru ne daga ranar Alhamis zuwa Asabar a ƙauyukan da suka haɗa da Sabon Gari da Kungurki. Mataimakiyar shugaban majalisar dokokin Edo ta yi murabus Hajji: Gwamnan Gombe ya yi bankwana da maniyyata 966, ya bai wa kowa kyautar Riyal 200 Wani mazaunin yankin ya ce: “Mutane sun fara barin gidajensu da daddare, suna dawowa ne da safe. Hare-haren da ake kai wa Sabon Gari da maƙwabtan ƙauyuka na ƙara tsananta.” Ana zargin yaran wani ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Bello Kaura wanda aka fi sani da Dan Sade ne da...
    Akalla mutane uku ne aka ce an kashe tare da yin garkuwa da wasu 26 a wani sabon harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a karamar hukumar Kauran Namoda da ke jihar Zamfara. Daily trust ta bankado cewa, hare-haren na tun ranakun Alhamis zuwa Asabar, sun shafi al’ummomi da dama a yankin. Tattalin Arzikin Sin Ya Bunkasa Bisa Daidaito A Afirilu Yanzu-Yanzu: Ana Zargin Makiyaya Sun Kashe Mutane 15 A Benuwe Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, lamarin ya fi kamari akauyen Sabon Gari, inda aka kashe mace guda tare da yin garkuwa da mazauna yankin kusan 20. Wani mazaunin Kauran Namoda, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya yi ikirarin cewa, adadin ya zarta haka, inda ya...
    Hukumar kididdiga ta kasar Sin NBS, ta ce duk da matsi sakamakon dalilai na ciki da na waje, tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa bisa daidaito a watan Afirilun da ya gabata. Alkaluman da NBS din ta fitar a Litinin din nan sun nuna karuwar hajojin da manyan masana’antun kasar ke samarwa da kaso 6.1 bisa dari a shekara, yayin da alkaluman samar da hidimomi suka karu da kaso 6.0 bisa dari a shekara. Sai kuma darajar jimillar hajojin sayayyar daidai, ta kayayyakin bukatun yau da kullum da ta kai kudin kasar yuan tiriliyan 3.7, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 515.6 a shekara, adadin da shi ma ya yi karuwar kaso 5.1 bisa dari. Kazalika, alkaluman sun nuna daga watan Janairu...
    Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya rantsar da tsohon Sojan sama (Air Vice Marshal) Ibrahim Umaru a matsayin sabon Kwamishinan tsaro na cikin gida a yayin taron majalisar zartarwa na 28 a fadar gwamnati. Tsohon hafsan Sojan saman, wanda ya yi ritaya, ya kasance Daraktan-Janar na sashin aiyuka na musamman a fadar gwamnatin jihar Kano kafin naɗin nasa. Kasar Sin Za Ta Inganta Cikakken Tsarin Fitar Da Ma’adanai Zuwa Ketare Don Kiyaye Tsaron Kasa Rashin Tsaro Da Raba Wa Manoma Kayan Aiki Kan Lokaci Na Baraza Ga Wadata Kasa Da Abinci Gwamnan Yusuf ya buƙaci sabon kwamishinan ya yi aiki da gaskiya, mutunci da himma wajen kare rayuka da dukiya a jihar, yana mai jaddada mahimmancin haɗin gwuiwa tsakanin hukumomin...
    Seyi Tinubu, ɗan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, na cikin tawagar mahaifinsa da ta ziyarci fadar Vatican a ranar Lahadi domin halartar bikin rantsar da sabon Fafaroma, Leo XIV. A yayin ziyarar, Shugaba Tinubu ya gana da Fafaroma har suka gaisa. Yadda Boko Haram ta kashe manoma 90 a Borno cikin wata 5 NAJERIYA A YAU: Mece ce Makomar Dimokuraɗiyya Idan Aka Wajabta Kada Kuri’a? Amma abin da ya ja hankalin mutane shi ne lokacin da Seyi ya yi ƙoƙarin zuwa wajen mahaifinsa yayin da yake gaisawa da Fafaroma. A wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, an ga wani jami’in tsaro ya dakatar da Seyi cikin ladabi, yana nuna masa cewa bai kamata ya matsa kusa da wajen...
    Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya aika ta’aziyya ga iyalan mutane 37 da hatsarin kwale-kwalen Gbajibo ya rutsa da su daga jihar Neja a karshen mako.   A cikin sanarwar gwamna AbdulRazaq ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Neja kan wannan lamari mai ban tausayi.   Gwamnan ya bukaci ma’aikatan jirgin da fasinjoji da su bi ka’idojin tsaro domin amfanin kowa.   Ya bayyana a matsayin al’ada mai raɗaɗi kuma ba za a yarda da ita ta rashin amfani da na’urorin kariya da gwamnati ta bayar akai-akai.   Yana rokon Allah ya jikan wadanda aka kashe. REL/ALI MUHAMMAD RABIU
    Sarkin Saudiyya, Salman Bin Abdulaziz, ya bayar da umarnin ɗaukar nauyin Hajjin iyalan Falasɗinawa 1,000 da suka rasa ‘yan uwansu sakamakon yaƙin da ke ci gaba da gudana a Zirin Gaza da Isra’ila. Wannan taimako na cikin littafin kujerun Hajji da masarautar ke rabawa a kowace shekara ga al’umma ko kuma ɗaukar nauyin waɗanda suka cancanta, ciki har da waɗanda suka riga suka biya kuɗin Hajjin. Amurka Da Saudiyya Sun Ƙulla Yarjejeniyar Dala Biliyan 600 Kan Tsaro, Makamashi Da Fasaha Isra’ila Ta Yi Barazanar Kai Hare-Hare Kan Iran Kamar Hamas Da Hezbollah Sarkin ya bayyana wannan mataki ne a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin nuna goyon baya da jin ƙai ga al’ummar Falsɗinawa a wannan lokaci mai wahala da suke...
    Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara ta yi kakkausar suka ga gwamna Dauda Lawal kan kalaman da ta bayyana a matsayin bata gari dangane da kokarin gwamnatinsa na magance ‘yan fashi da makami da kuma bayar da tallafi ga wadanda ‘yan fashin suka kashe.   Hakan ya biyo bayan wani faifan bidiyo ne da aka ga gwamnan yana magana da manema labarai kan yadda gwamnatinsa ke tafiyar da harkokin tsaro da kuma jin dadin wadanda matsalar tsaro ta shafa.   A wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar APC, Yusuf Idris Gusau ya fitar, ya bayyana kalaman gwamnan a matsayin rashin gaskiya da yaudara.   Malam Idris Yusuf Gusau ya yi zargin cewa, gwamnatin ta gaza cika wasu...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Yana fatan tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka za ta kai ga cimma yarjejeniya ta gaskiya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshgan ya bayyana cewa: Iran tana fatan tattaunawarta da Amurka za ta kai ga cimma yarjejeniya ta gaskiya da za ta tabbatar da dorewar zaman lafiya a yankin. A yammacin jiya Lahadi, a gefen taron dandalin tattaunawa na Tehran na shekara ta 2025, a wata ganawa da ministan harkokin wajen masarautar Oman Badar bin Abdullah al-Busaidi, Shugaba Pezeshkian ya yaba da irin kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, da kuma irin rawar da gwamnatin Oman take takawa wajen daukar nauyin shawarwarin da ba na kai tsaye ba tsakanin Amurka da Jamhuriyar...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Iran ta jajirce kan harkokin diflomasiyya kuma tana neman yarjejeniya ta gaskiya Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada kudurin kasar Iran kan harkokin diflomasiyya da kuma cimma daidaito bisa tsarin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya, tare da cikakken mutunta hakkin nukiliyar kasar Iran, da kuma tabbatar da manufar dage takunkuman da aka sanya mata. Wannan dai ya zo ne a cikin jawabin da Araqchi ya gabatar a ranar Lahadin da ta gabata a wajen taron tattaunawa na birnin Tehran, wanda cibiyar nazarin harkokin siyasa da kasa da kasa ta ma’aikatar harkokin wajen kasar ta dauki nauyin shiryawa, tare da halartar tawagogi 200 na manyan jami’ai daga kasashe 53 da...
    Gwamnatin jihar Kebbi ta jajanta wa al’ummar Waje da ke karamar hukumar Danko Wasagu sakamakon harin ‘yan bindiga da ya yi sanadin mutuwar manoma 15 tare da jikkata wasu 3.   Mataimakin gwamnan jihar, Sanata Umar Abubakar Tafida, ya mika sakon ta’aziyyar gwamnati tare da bayar da tallafin Naira miliyan 24 ga iyalan wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata.   Ya bayyana hakan a matsayin kokarin da gwamnatin jihar ke yi na tallafawa iyalan wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata a wannan lokaci mai cike da kalubale.   Sanata Abubakar, ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta dauki matakan da suka dace don magance matsalar rashin tsaro, tare da baiwa manoma damar gudanar da ayyukansu cikin...
    A lokacin da kasashen Yamma suka yi biris da kisan gillar da ake yi a Gaza, kuma suna kuka kan cutar da tsohon shugaban Amurka Biden ke fama ita Marubuciya kuma ‘yar jarida kasar Autraliya Caitlin Jahnstone a cikin wani makala da ta rubuta ta siffanta abin da ta kira matsayin munafuncin ƙasashen yamma wajen mu’amala da kimar ɗan adamtaka da gwada alhini kan batun ciwon tsohon shugaban Amurka Joe Biden game da cutar sankara da ke fama da ita a matsayin mafarin fallasa sabanin da ke cikin maganganun siyasa da kyawawan ɗabi’u na Amurka dangane da laifukan yaƙi musamman abin da ke faruwa a Gaza. Tana cewa: Ciwon daji na Prostate yana da ‘yancin wanzuwa. Yayin da ciwon daji...
    Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta ce ta samu gagarumar nasara wajen shiga sahun kasashen duniya a ranar cutar hawan jini ta duniya. Kwamishinan lafiya Dr Abubakar Labaran ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a taron tunawa da ranar hawan jini ta duniya, wanda aka gudanar a Kano.     A taron tunawa da ranar, ma’aikatar ta shirya wani tattaki da taron manema labarai da nufin wayar da kan jama’a game da cutar hawan jini da inganta rigakafinta, ganowa da sarrafa shi.     An fara tattakin ne a ma’aikatar lafiya ta hanyar gidan waya da karfe 8:30 na safe kuma aka kammala a cibiyar bayar da agajin gaggawa (EOC) da ke cikin asibitin...
    Fira ministan gwamnatin rikon kwaryar Libiya ya bayyana cewa: Babu wata cibiyar tsaro a Libya sai dai cibiyoyi na yau da kullum da suka hada da sojoji da ‘yan sanda Abdul Hamid Dbeibah, shugaban gwamnatin rikon kwaryar gwamnatin hadin kan kasa, ya ce: “Babu wani wuri a kasar Libya, sai dai cibiyoyi na yau da kullum, ciki har da sojoji da ‘yan sanda,” Dbeibah, ya fadi haka ne biyo bayan al’amuran tsaro da suka faru a babban birnin kasar, Tripoli, a ranar litinin bayan kisan Abdul Ghani al-Kikli, wanda aka fi sani da “Ghaniwa,” kwamandan kungiyar da ake kira “Stability Support Apparatus”. Bayanin na Dbeibah ya zo ne a yayin wani taron tsaro da aka gudanar a makon da ya...
    Sarkin Saudiyya, Salman Bin Abdulaziz, ya bayar da umarnin ɗaukar nauyin Hajjin iyalan Falasɗinawa 1,000 da suka rasa ‘yan uwansu sakamakon yaƙin da ke ci gaba da gudana a Zirin Gaza da Isra’ila. Wannan taimako na cikin littafin kujerun Hajji da masarautar ke rabawa a kowace shekara ga al’umma ko kuma ɗaukar nauyin waɗanda suka cancanta, ciki har da waɗanda suka riga suka biya kuɗin Hajjin. Amurka Da Saudiyya Sun Ƙulla Yarjejeniyar Dala Biliyan 600 Kan Tsaro, Makamashi Da Fasaha Isra’ila Ta Yi Barazanar Kai Hare-Hare Kan Iran Kamar Hamas Da Hezbollah Sarkin ya bayyana wannan mataki ne a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin nuna goyon baya da jin ƙai ga al’ummar Falsɗinawa a wannan lokaci mai wahala da suke...
    Allah ya yiwa fitaccen ɗan jarida kuma wakilin Gidan Rediyon Muryar Amurika (VOA) a jihohin Borno da Yobe, Haruna Dauda Biu rasuwa a ranar Lahadi a Maiduguri. Marigayin, wanda ya kuma kasance tsohon shugaban ƙungiyar ‘yan jarida (Correspondents Chapel) na jihar Borno, ya rasu ne bayan doguwar jinya. Na Dauki Karramawar Jaridar LEADERSHIP Da Matukar Muhimmanci – Gwamna Abba Babu Wani Dan Jarida Da Aka Hana Shiga Taron Gwamnonin Arewa – CPS Ibrahim Musa An shirya gudanar da sallar jana’izarsa yau Litinin a ƙofar gidansa da ke unguwar State Low-Cost, Maiduguri. Abokan aiki da ‘yan uwa sun bayyana baƙin ciki game da rasuwar, suna yaba masa da halayensa na kirki da ƙwarewarsa a fannin jarida. Daga kanmu, magana ta...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ɗaya daga cikin ginshiƙan tsarin dimokuradiyya shi ne zaɓi – bai wa jama’a dama su zaɓi abin da suke so, ko kuma wanda suke so ya shugabance su. Wannan ne ya sa ɗaya daga cikin muhimman matakai a kafuwar tsarin shi ne zaɓe. Sai dai kuma abin tambaya shi ne, zaɓin ya haɗa har da na yin zaɓe ko ƙaurace masa? Mene ne matsayin tsarin dimokuraɗiyya idan aka wajabta wa al’umma kaɗa ƙuri’a? NAJERIYA A YAU: Shin Jam’iyyar NNPP Za Ta Kai Labari A 2027? DAGA LARABA: Tasirin Mulkin Karɓa-Karɓa A Najeriya Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai duba. Domin sauke shirin latsa nan
    Bayanai daga falasdinu na cewa an kashe ‘yan jarida 5 na Falasdinawa a wasu hare-hare daban-daban da Isra’ila ta kai a zirin Gaza, lamarin da ya kai adadin ma’aikatan yada labaran da aka kashe tun farkon yakin Isra’ila a zirin Gaza zuwa 222. Daga cikin wadanda harin ya rutsa da su har da dan jarida mai daukar hoto Aziz al-Hajjar, da matarsa, da ‘ya’yansu, wadanda aka kashe a ranar Lahadi, lokacin da jiragen yakin Isra’ila suka kai hari a gidansu da ke unguwar Saftawi a arewacin Gaza. A gefe guda kuma, an kashe dan jarida Ahmad al-Zinati tare da matarsa, Nour al-Madhoun, da ‘ya’yansu, Mohammad da Khaled, a lokacin da aka kai wa tantin su hari a Khan Younis a...