An shawarci ‘yan siyasa a jihar Neja da su kiyaye mutuncin da aka san jihar da su domin tabbatar da nasarar zaben kananan hukumomin jihar da ke tafe.

 

Zaben da aka shirya gudanarwa a ranar farko ga watan Nuwamba na wannan shekara, ya yi alkawarin za a yi shi cikin gaskiya ba tare da wata tangarda ba, tare da shirye-shiryen da tuni aka yi nisa.

 

Mai ba Gwamnan Jihar Neja shawara ta musamman kan harkokin siyasa Alh Mohammed Nma Kolo ne ya bayar da wannan shawarar a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Minna.

 

Alh Nma Kolo ya kuma tunatar da su cewa a kowace gasa dole ne a samu wanda ya yi nasara da wanda bai yi nasara ba.

 

Mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa da dabaru ya jaddada muhimmancin hadin kai da fahimtar manufa a tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki. “Bari mu kalli neman mukaman siyasa ba a matsayin neman mulki ba, a’a a matsayin kira ga hidima, ta yadda idan muka fifita hidima fiye da kishin kashin kai, mu inganta ci gaba da karfafa dimokaradiyyarmu,” inji shi.

 

Sai dai ya yabawa hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Neja bisa matakin da ta dauka na kiyaye bangaranci, sannan ya bukaci masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa a jihar da su bi ka’idojin gudanar da zabe, bisa la’akari da jajircewar da gwamnatin ta yi wajen tabbatar da tsarin dimokuradiyya a karkashin Gwamna Mohammed Umar Bago, yana da kwarin gwiwar cewa za a gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

 

“Gwamnan mu hazikin dan siyasa ne wanda ya fahimci mahimmancin bin ka’ida, don haka ya kamata mu mayar da wannan karimci da jajircewa wajen tabbatar da an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.” Inji shi.

 

Alh Mohammed Nma Kolo ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su marawa Gwamna Umar Bago goyon baya don ganin an samu sabuwar Neja.

 

PR ALIYU LAWAL.

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Siyasa Neja tabbatar da

এছাড়াও পড়ুন:

Masu ibadar Umara 42 sun mutu a hatsarin mota a hanyar zuwa Makka

Wasu masu ibadar Umara 42 sun mutu bayan da motarsu ta yi taho-mu-gama da wata tankar mai a kusa da birnin Madina da ke kasar Saudiyya.

Dukkan masu ibadar ’yan kasar Indiya ne, kuma hatsarin ya ritsa da su ne a kan hanyarsu ta zuwa Makka bayan kammala ziyara a birnin Madina.

Ministan harkokin wajen Indiya Dakta S. Jaishankar ya bayyana cewa mutum daya daga cikin fasinjojin ya tsallake rijiya da baya a hatsarin da ya auku da tsakar daren Litinin.

Hatsarin ya auku ne a bayan da motar safa mai daukar mutum 43 da masu ibadar suke ciki ta yi karo gaba-da-gaba da wata tankar mai.

’Yan ta’adda sun sace dalibai 25 a dakunan kwanansu a Kebbi NELFUND ya raba wa ɗalibai tallafin karatu na Naira Biliyan 116 

A sakon ta’azaiyyarsa ga iyalan mamatan, Ministan harkokin wajen Indiya, ya bayyaan cewa ofisoshin jakadancin kasar ke Saudiyya, na bayar da cikakken tallafi ga masu Umarar da hatsarin ya rusta da su.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sace Ɗalibai: Gwamnatin Tinubu ba ta shirya kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga ba — Amnesty
  • MACBAN Ta Nemi Amurka Ta Cire Sunanta Daga Jerin Waɗanda Ta Ƙaƙabawa Takunkumi
  • Masu ibadar Umara 42 sun mutu a hatsarin mota a hanyar zuwa Makka
  • Da amincewar hukumomi nake tattaunawa da ’yan bindiga — Sheikh Gumi
  • Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku
  • ’Yan Bindiga A Kano: Sanusi II ya ziyarci Faruruwa, ya buƙaci a tsaurara tsaro
  • Makiya Sun Kulla Makirci kan Kasar Labanon Irin Wanda Suka Kulla Kan Siriya
  • Meke Kawo Yanke Hukunce-hukunce Masu Karo Da Juna Daga Kotuna?
  • Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca
  • Illolin Neman Kudi Ido Rufe Ba Tare Da Kula Da Halal Ko Haram Ba