Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare
Published: 1st, October 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Gombe ta sanar da fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare da kuma takaita zirga-zirgar makiyaya tsakanin kananan hukumomi daga ranar Laraba, daya ga watan Oktoban 2025.
Shugaban kwamitin sasanta rikicin manoma da makiyaya na jihar, wanda kuma shi ne kwamishinan Ma’aikatar Noma da Kiwo ta jihar, Dakta Barnabas Malle, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar.
Sanarwar ta ce matakin na cikin tsare-tsaren tabbatar da zaman lafiya a lokacin kakar bana, wanda manoma ke girbe amfanin gonarsu.
Daga cikin ƙa’idojin da aka kafa akwai hana kiwo daga ƙarfe 6 na yamma zuwa ƙarfe 6 na safe, takaita zirga-zirgar makiyaya tsakanin kananan hukumomi, da kuma hana safarar amfanin gona a waɗannan lokutan.
Gwamnatin ta kuma umarci shugabannin kananan hukumomi su tabbatar da rufe hanyoyin shiga yankunansu, tare da umartar masu rike da sarautun gargajiya da su tabbatar da aiwatar da ƙudurin domin ci gaba da samun zaman lafiya a jihar.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Dole ku ceto daliban da aka sace a Kebbi Shugaban Sojoji
Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar-Janar Waidu Shuaibu, ya umarni dakarun soji cewa ya zama tilas su nemo sannan su ceto daliban da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Makarantar ’Yan Mata ta Gwamnati (GGCSS) da ke yankin Maga a Jihar Kebbi.
Janar Waidi Shuaibu ya bayar da umarnin ne a yayin ziyarar aiki da ya kai, Jihar Kebbi, washegarin harin ’yan bindiga suka kai makarantar da ke Karamar Hukumar Danko Wasagu.