ASUU Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwanaki 14 Don Biyan Buƙatunta
Published: 30th, September 2025 GMT
Buƙatun da ASUU ke nema sun haɗa da: sake duba yarjejeniyar 2009 tsakaninsu da gwamnati, samar da ƙarin kuɗaɗen bunƙasa jami’o’i, biyan bashin albashin da suke bi, da samar da ingantaccen tsarin kuɗi mai ɗorewa ga jami’o’i.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku.
কীওয়ার্ড: Gargaɗi Gwamnatin Tarayya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Gombe ta bai wa alƙalai da Khadi-Khadi kyautar sabbin motoci 16
Gwamnatin Jihar Gombe ta raba sabbin motoci ƙirar SUV guda 16 ga Alƙalai na Babbar Kotu da Khadi-Khadi na Kotun Shari’a domin taimaka musu wajen gudanar da aikinsu yadda ya kamata a fadin jihar.
Motocin sun haɗa da motoci biyu ƙirar Toyota SUV samfurin 2025 da aka bai wa babban alƙal8 da Grand Khadi.
Na kusa komawa APC – Gwamnan Taraba Tsohon Minista Kabiru Turaki ya zama sabon shugaban PDP na ƙasaMotocin guda 14 ƙirar GAC SUV samfurin 2025 da aka raba wa sauran alƙalai da khadi-khadi.
Da yake miƙa motocin, Mataimakin Gwamna Mannasah Daniel Jatau, ya ce gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na ƙoƙari wajen samar da kayan aiki na zamani domin inganta ayyukan gwamnati, musamman a ɓangaren shari’a.
Ya ce gwamnati na magance matsalolin da ta gada, ciki har da biyan fansho da biyan albashi a kan lokaci.
Ya kuma yi kira ga waɗanda aka bai wa motocin da su yi amfani da su wajen gudanar da ayyukansu.
A nasa jawabin, Kwamishinan Kuɗi, Muhammad Gambo Magaji, ya bayyana cewa an kashe sama da Naira biliyan biyu wajen sayen motocin.
Ya ce tsawon sama da shekaru 10 ɓangaren shari’a bai samu sabbin motocin aiki ba.
Kwamishinan Shari’a, Barista Zubair Muhammad Umar, ya ce rabon motocin wani ɓangare ne na cika alƙawarin gwamnati na inganta ɓangaren shari’a.
Ya tunatar da cewa aikin gina sabon ginin Babbar Kotu na kimanin Naira biliyan 16 na ci gaba da gudana.
A jawabinsa na godiya, Babban Magatakardar Babbar Kotu, Barista Bello Shariff, ya yaba wa gwamnatin jihar bisa goyon bayan da ta ke bai wa bangaren shari’a.
Ya bayyana cewa za su yi amfani da motocin ta hanya mai kyau domin inganta ayyukansu.