Sanarwar ta ƙara da cewa, taken taron shi ne “Buɗe Dabarun Damarmaki”, kuma ya tattaro duk masu ruwa da tsaki a sassan Arewacin Nijeriya.

 

A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya yaba wa Ƙungiyar Dattawan Arewa bisa jajircewar da take yi wajen ci gaban yankin Arewa.

 

“Ta hanyar kiran wannan taro a ƙarƙashin taken ‘Buɗe Dabarun Damarmaki,’ kun sake nuna kyakkyawar manufar ku kan makomarmu baki ɗaya.

 

“Bangarori kamar – Ma’adinai, Noma, da Makamashi — ba bisa haɗari aka same su ba, ginshiƙai ne waɗanda dole ne a gina su don ci gaban Arewacin Nijeriya. A Zamfara muna sane da halin da muke ciki: ƙasa mai albarkar ma’adanai masu tarin yawa da ƙasar noma, amma duk da haka mutanenmu ba su ci cikakken ribar waɗannan abubuwan ba.

 

“Muhimmin tambaya a gare mu a matsayinmu na shugabanni ba shi ne yin abin da ya kamata ba, amma ta yaya za mu iya juya akalar abin da ake muke da shi zuwa ci gaban al’umma. Don jawo jarin da ake buƙata da kuma samar da masana’antu a yankinmu don amfanin al’umma, dole ne mu tsaya haiƙan, mu rungumi sabuwar hanyar haɗin gwiwa.”

 

Gwamna Lawal ya ci gaba da jaddada cewa, Arewa mai zaman lafiya, Arewa ce mai ƙarfin tattalin arziki, yanki ne da ya kamata shugabannin jihohinta 19 su zurfafa haɗin gwiwa fiye da siyasa.

 

“Dole ne mu haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen kare mutane da saka hannun jari. Tsaro shi ne babban abin da ake buƙata na duk wani ci gaba mai ma’ana. Masu zuba jari, na cikin gida da na lasa da ƙasa, ba masu hannu da shuni ba ne; su masu gaskiya ne. Ba za su saka jari a inda babu tsaro ba. Dole ne mu haɗa ƙarfin tsaron mu, mu raba hankali a cikin haƙiƙanin lokaci, da kuma samar da manyan jami’an tsaro na al’umma don samar da ingantaccen tsaro.

 

“A Zamfara, ƙoƙarinmu a fili yake, mun ƙaura daga halin da ake ciki a da na rashin gaskiya da rashin bin doka da oda a fannin ma’adinai zuwa yanayin na gaskiya da amana. Mun farfaɗo da harkar noma ta hanyar inganta noman zamani, sarrafa kayan noma, da samun rance. Kuma muna samar da yanayi mai tsaro da kwanciyar hankali wanda shi ne ƙashin bayan komai.

 

“Kirana a yau shi ne Yarjejeniyar Tattalin Arziki na Arewacin Nijeriya — alaƙar mai ƙarfi tsakanin jihohi 19 da su yi magana da murya ɗaya kan harkokin tsaro da tattalin arziki. Samar da hanya guda ɗaya ga manyan masu zuba jari da ke neman yin kasuwanci a faɗin yankin. A hafa hannu a muhimman ababen more rayuwa kamar wutar lantarki da jirgin ƙasa, igiya mai ƙarfi da zara haɗe jihohin mu.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Farashin Kayan Abinci Na Cigaba Da Sauka A Jihohin Arewa Maso Gabas

A Damaturu, farashin mudun shinkafa ya ragu daga N5,000 zuwa N2,500, yayin da wake, masara da gero suma suka sauka fiye da rabin tsohon farashinsu. Masana tattalin arziki sun ce yawaitar shigo da hatsi kamar shinkafa da alkama ya taimaka wajen rage tsadar abinci da ake fama da ita a watannin baya.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ta Ragu Zuwa Kashi 16.065% November 17, 2025 Labarai ‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga  November 17, 2025 Labarai Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi November 17, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ministan tsaron Iran na Ziyara a UAE don karfafa dangantakar tsaro tsakanin kasashen yankin
  • Farashin Kayan Abinci Na Cigaba Da Sauka A Jihohin Arewa Maso Gabas
  • Gobara ta laƙume rayukan yara biyu ’yan gida ɗaya a Ribas
  • Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi
  • Sarki Sanusi Ya Shawarci Unguwannin Da Suka Fuskanci Matsalar Tsaro Su Sa Idon
  • Tsaro: Na kan yi kuka duk lokacin da na ji an kashe wani — Akpabio
  • ’Yan Bindiga A Kano: Sanusi II ya ziyarci Faruruwa, ya buƙaci a tsaurara tsaro
  • Na kusa komawa APC – Gwamnan Taraba
  • Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Gina Sabbin Ginshikan Samar Da Ci Gaban Kasa Masu Inganci
  • An Gabatar Da Sabuwar Hanyar Raya Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Tsakanin Sin Da Afirka