Kotu Ta Dakatar Da PENGASSAN, NNPCL Kan Katse Wa Matatar Ɗangote Ɗanyen Mai Da Iskar Gas
Published: 29th, September 2025 GMT
A taƙaitaccen hukuncin da ya yanke kan ƙarar, Mai shari’a Subilim ya bayyana cewa, ci gaba da yajin aikin zai lalata kasuwancin matatar da gurgunta mafi mahimmancin ayyukan ci gaban tattalin arzikin al’ummar Nijeriya.
Alƙalin kotun ya ce, dokar hana ci gaba da yajin aikin za ta ci gaba da aiki har tsawon kwanaki bakwai ne kacal.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su
Babban lauya kuma mai kare haƙƙin ɗan Adam, Femi Falana (SAN), ya bai wa ƴan Nijeriya shawara da su kai Gwamnatin Tarayya ƙara don neman a mayar musu da kuɗin fansar da suka biya yayin da aka yi garkuwa da ƴan uwansu. Ya ce gwamnatin ta kasa sauke babban nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mata na kare rayuka da dukiyoyin ƴan ƙasa.
Falana ya yi wannan jawabi ne a lokacin buɗe sabuwar shekarar Shari’a ta Tsangayar Shari’a ta Jami’ar Yakubu Gowon da ke Abuja. Ya ce yawaitar garkuwa da mutane a sassan ƙasar nan ya nuna gazawar gwamnati wajen tabbatar da kariya kamar yadda kundin tsarin mulki da Yarjejeniyar Afrika kan Haƙƙin Dan Adam suka tanada. Ya kuma soki bambancin yadda hukumomi ke tunkarar lamarin, yana mai cewa ana hanzari ne idan manyan mutane aka sace, amma an bar talakawa cikin tsoro da halin ƙaƙa-niki-ka-yi.
Falana Ya Kai Karar Gwamnatin Tarayya Da Jihohi Kan Yara Da Ba Su Zuwa Makaranta Tsauraran Manufofin Tattalin Arziƙin Tinubu Ya Ƙara Yawan Matalauta – FalanaFalana ya jaddada cewa kai gwamnati kotu zai taimaka wajen kare haƙƙin waɗanda suka biya kuɗin fansa, tare da matsa wa gwamnati ta inganta tsaro cikin gaggawa. Sabon rahoton Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ya nuna cewa ƴan Nijeriya sun biya Naira Tiriliyan 2.23 a matsayin kuɗin fansa tsakanin Mayu 2023 zuwa Afrilu 2024. Rahoton Crime Experience and Security Perception Survey (CESPS) na 2024 ma ya nuna cewa fiye da mutum miliyan 2.2 an yi garkuwa da su a wannan lokaci, tare da matsakaicin kuɗin fansa na kusan ₦2.7m ga kowane mutum.
ADVERTISEMENTA cewar masana tsaro, garkuwa da mutane ya koma kasuwancin da ke samar da riba ga miyagu, lamarin da ke buƙatar tsauraran matakai daga gwamnati tare da ingantaccen tsari da haɗin gwuiwar jami’an tsaro.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA