Kwamitin Aikin Hajjin 2025 Na Jihar Kano Ya Kammala Rahoton Aikinsa Na Wucin Gadi
Published: 30th, July 2025 GMT
Kwamitin Aikin Hajjin 2025 Na Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Sarkin Karaye, Mai Martaba Alhaji Muhammad Mahraz Karaye, ya kammala rahoton aikinsa na wucin gadi.
Darakta Janar na Hukumar, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ne ya bayyana hakan a fadar Sarkin da ke Karaye.
Ya ce rahoton ya ƙunshi dukkan abubuwan da suka shafi aikin Hajji tun daga lokacin da aka ƙaddamar da kwamitin a birnin Makkah, ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Kano, Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf.
“Rahoton ya kunshi cikakken bayani kan ayyukan da kwamitin ya gudanar zuwa yanzu, kuma zai kasance muhimmin ɓangare na rahoton ƙarshe da za a miƙa ga Gwamna,” In ji shi.
Alhaji Lamin Rabi’u ya bayyana cewa Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta rigaya ta tattara nata cikakken rahoton, wanda za a mika wa Gwamnan nan ba da daɗewa ba.
A nasa jawabin, Sarkin Karaye ya nuna godiya ƙwarai ga Gwamnan Jihar bisa amincewa da baiwa kwamitin damar gudanar da wannan aiki mai muhimmanci.
Shugaban Hukumar gudanarwa na hukumar Alhaji Yusif Lawan, ya bayyana godiya ga Sarkin Karaye bisa sadaukarwa da haɗin kai da ya bayar, wanda ya taimaka wajen samun nasarar aikin kwamitin.
Abdullahi Jalaluddeen
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Karamar Hukumar Gwarzo Ta Karfafa Yaƙi Da Miyagun Kwayoyi Da Shan Magani Ba Bisa Ka’ida Ba
Shugaban karamar hukumar Gwarzo, Dr. Mani Tsoho, ya yi gargaɗi ga mazauna yankin kan mummunan ɗabi’ar shan magani ba tare da shawarar likita ba, yana mai bayyana hakan a matsayin babban haɗari ga lafiya da ka iya janyo matsalolin da ke barazana ga rai.
Dr. Tsoho ya yi wannan gargaɗi ne yayin da yake ziyarar duba asibitin Gwarzo General Hospital, inda ya gana da marasa lafiya, ya duba yadda ake gudanar da ayyuka, tare da yabawa ma’aikatan lafiya bisa jajircewarsu wajen kula da jama’a.
Ya nuna damuwa cewa, yawancin matsalolin lafiya da ake fuskanta a cikin al’umma na faruwa ne sakamakon amfani ko wuce gona da iri wajen shan magunguna ba tare da shawarwarin ƙwararru ba.
Ya shawarci jama’a da su nemi shawarar likitoci da masu magunguna kafin su sha kowanne irin magani.
Shugaban karamar hukumar ya yi kira ga mazauna yankin da su rika ziyarar asibiti mafi kusa da zarar sun ji wata alamar rashin lafiya don samun kulawa cikin lokaci.
Ya tabbatar da cewa akwai likitoci da nas-nas ƙwararru a cibiyoyin lafiya na yankin da za su samar da ingantacciya kulawa.
Yayin da yake jaddada kudirin gwamnatinsa na inganta harkokin lafiya a dukkan yankuna, Dr. Tsoho ya ce hukumar tana aiki don samar da isassun magunguna, kayan aiki na zamani da kuma horaswa ga ma’aikatan lafiya.
Baya ga batun lafiya, shugaban ya kuma yi kira ga jama’a da su kasance masu lura da tsaro, tare da yin gaggawar kai rahoton duk wani motsi ko mutum da ba su yarda da shi ba ga jami’an tsaro domin daukar mataki cikin lokaci.
Daga Khadijah Aliyu