Sin Da Benin Da Thailand Za Su Aiwatar Da Matakan Saukaka Tantance Kaya Na Kwastam
Published: 30th, July 2025 GMT
Babbar hukumar kwastam ta Sin ta fitar da sanarwar a yau Talata cewa, shirin amincewa da juna na tsarin “Masu gudanar da kamfanoni da aka ba su izni” wato AEO a takaice tsakanin Sin da Benin da Thailand zai fara aiki a hukumance daga ranar 1 ga watan Agustan shekarar 2025.
Bayan aiwatar da wannan tsarin amincewa da juna, za a ba da dama tsakanin kwastam na Sin da na Benin, da kuma kwastam na Sin da na Thailand, don su amince da juna a karkashin AEO.
Bugu da kari, yayin da ake tantance kayayyakin da ake shigowa da su daga waje a wurin kwastam, za a saukaka wa kamfanonin dake karkashin tsarin AEO wasu abubuwa, kamar rage yawan matakan dubawa, da ba su fifiko kan ayyukan kwastam, da kuma kebe musu jami’an hulda na kwastam da sauran matakai na samun sauki.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Guterres: Jerin Shawarwarin Da Sin Ta Gabatar Sun Cika Ka’idar Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya
Babban sakataren MDD António Guterres, ya bayyana a jiya Talata cewa, jerin shawarwarin da Sin ta gabatar wato shawarar raya duniya, shawarar tabbatar da tsaron duniya, shawarar raya wayewar kan al’ummun duniya, da kuma jagorantar harkokin duniya, sun dace da ka’idar kundin tsarin MDD.
Guterres ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida a wani taron manema labarai da aka yi a ranar. Ya ce shawarwarin da Sin ta gabatar sun mutunta manufar kasancewar bangarori da dama, kuma sun goyi bayan MDD a matsayin cibiyar hadin gwiwar kasa da kasa, tare da dukufa kan inganta hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban da warware rikice-rikice cikin lumana.
Guterres ya kara da cewa, yanzu ana fuskantar rarrabuwar kawuna a fagen siyasa ta duniya da kuma karuwar yaduwar rikice-rikice, da ma rashin hukunta masu laifi. Bugu da kari, sabbin fasahohi suna ci gaba da bullowa “ba tare da bin wani tsari ba”, yayin da rashin daidaito ke kara tsananta. A wannan yanayi, babban taro karo na 80 na MDD mai tsawon mako guda da za a fara a mako mai zuwa, zai ba da duk wata dama ga tattaunawa da shiga tsakani.(Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp