APC ta ƙaryata jita-jitar sauya Shettima kafin zaɓen 2027
Published: 4th, April 2025 GMT
Jam’iyyar APC, ta musanta jita-jitar cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, na shirin sauya Mataimakinsa, Kashim Shettima, kafin zaɓen 2027.
Jam’iyyar ta ce babu wata matsala tsakaninsu kuma maganar sauya Shettima ba ta da tushe.
Hakeem Baba-Ahmed ya yi murabus daga gwamnatin Tinubu Fitaccen malami Dokta Idris Dutsen Tanshi ya rasuDaraktan Yaɗa Labarai na Jam’iyyar APC na Ƙasa, Alhaji Bala Ibrahim, ya shaida wa Aminiya cewa wasu ne ke yaɗa wannan jita-jitar don tayar da ƙura.
“Wannan jita-jita ce kawai marar tushe. Maganganu ne da bai kamata a ɗauke su da muhimmanci ba,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, “Ko da a ce akwai wani dalili da zai sa shugaban ƙasa ya sauya mataimakinsa, ba zai iya yin hakan shi kaɗai ba. Dole sai da shawarwari tare da masu ruwa da tsaki.”
Ko da yake APC ba ta bayyana aniyar Tinubu na sake yin takara a karo na biyu ba, magoya bayansa da wasu shugabannin jam’iyya sun fara neman goyon baya don ya sake tsayawa takara a 2027.
Wasu na ganin ya cancanci ya nemi wa’adi na biyu domin kammala ayyukan da ya fara.
A halin yanzu, wasu ’yan siyasa daga yankin Arewa ta Tsakiya suna kira da a ba su tikitin shugaban ƙasa ko mataimaki a zaɓe mai zuwa.
Sun ce tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a 1999, yankin bai taɓa samun shugaba ko mataimakin shugaban ƙasa ba.
Farfesa Nghargbu K’tso, wanda ya wakilci tawagar, ya ce: “Daga cikin yankuna shida na ƙasar nan, Arewa ta Tsakiya da Kudu Maso Gabas ne kaɗai ba su taɓa samar da shugaban ƙasa ko mataimaki ba cikin shekaru 26 da suka gabata. Lokaci ya yi da za a yi adalci da haɗin kai.”
Sai dai Bala Ibrahim, ya mayar da martani cewa buƙatar Arewa ta Tsakiya ba ta da tushe kuma “ta mutu tun kafin ta fara.”
Ya ce yankin bai taka gagarumar rawa a zaɓen da ya gabata ba bare ya nemi irin wannan buƙata, kuma ba yanzu ne lokacin tattauna rabon muƙamai ba, tunda Tinubu bai kammala wa’adinsa na farko ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Sauya Mataimaki Zaɓen 2027
এছাড়াও পড়ুন:
Ana zargin mace da kashe ’yar uwarta a kan N800 din barkono
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Ondo ta tabbatar da kama wata mata mai suna Iluyemi Bosede bisa zargin kashe yayarta, Tewogboye Omowumi, a Akure, babban birnin jihar.
A cewar sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, Olayinka Ayanlade, ya fitar a ranar Talata, ya ce lamarin ya faru ne a ranar shida ga Satumba, 2025, bayan wata sa’insa da ta kaure tsakanin matar da marigayiyar kan Naira 800.
Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin NajeriyaJami’in ya bayyana cewa Bosede ta ture ’yar uwarta har ta faɗi ƙasa, lamarin da ya haifar da mutuwarta.
Ya ce, “Binciken farko ya nuna cewa Iluyemi Bosede ta je wurin yayar tata, Tewogboye Omowumi mai shekaru 35, domin karbar bashinta na N800 na kudin tumatir da barkono. Sai dai tankiyar da ta fara a matsayin ƙaramin sabani ta rikide zuwa tashin hankali, inda ake zargin Bosede ta riƙe kayan marigayiyar har ta faɗi ƙasa.”
“Abin takaici, duk da an garzaya da marigayiyar asibiti don samun kulawar gaggawa, likitoci sun tabbatar da mutuwarta tun kafin a fara ba ta taimako. Wannan lamari ya nuna yadda ƙaramin sabani zai iya rikidewa zuwa mummunar husuma idan ba a magance shi cikin lumana ba.”
Bayan faruwar lamarin, rundunar ta ce ta kama wadda ake zargi kuma tana tsare da ita a halin yanzu, yayin da bincike ke ci gaba.
Rundunar ta kuma tabbatar da cewa za a gurfanar da wadda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike, domin ta girbi abin da ta shuka.