Birtaniya ta sanar da cewa muddin Isra’ila ba ta biyayya wa wasu sharuɗa ba, to kuwa a watan Satumba mai zuwa za ta amince da Falasɗinu a matsayin halastacciyar ƙasa a yayin taron Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA).

Firaiministan Birtaniya Keir Starmer ne ya bayyana haka a wani jawabi da ya gudanar a yau Talata.

Starmer ya ce za su amince da ‘yancin Falasɗinu idan har Isra’ila ba ta ɗauki hanyar kawo ƙarshen halin da ake ciki a Gaza ba, ciki har da tsagaita wuta da kuma tsarin samar da zaman lafiya na din-din-din.

Nijar da Rasha sun ƙulla yarjejeniyar makamashin nukiliya Remi Tinubu ta bai wa waɗanda harin Benuwe ya shafa tallafin Naira biliyan ɗaya

A cewarsa, hakan zai tabbata “har sai idan Isra’ila ta ɗauki matakai na kawo karshen abin da ke faruwa a Gaza, ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, ta kuma tabbatar da cewa ba za a ƙwace Gaɓar Yamma ba, har ma da cimma yarjejeniyar zaman lafiya ta tsawon lokaci da za ta haifar da mafitar ƙasashe biyu.”

Firaministan ya ƙara nanata cewa babu wani bambanci tsakanin Isra’ila da Hamas kuma buƙatar da Birtaniya take da su kan Hamas suna nan — cewa dole su saki dukkan waɗanda suke garkuwa da su, su saka hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta, su kuma amince cewa ba za su saka baki a gwamnatin Gaza ba sannan su ajiye makamai.

Starmer ya ce za su ci gaba da duba lamarin da ke faruwa a Gaza gabanin taron babban zauren MDD da za a yi don ganin yadda ɓangarorin biyu suka ɗauki matakai na samar da zaman lafiya kafin ta ɗauki mataki na karshe.

Matakin da Birtaniyar ke shirin dauka na zuwa ne biyo bayan matsin lamba da Starmer ke sha a cikin ƙasar, inda ‘yan majalisu sama da 200 a makon da ya wuce, suka buƙaci ya aminta da ‘yancin Falasɗinu.

Baya ga haka kuma, ɗaruruwan mutane sun gudanar da zanga-zanga a titunan birnin Landan, suna mai kira ga Starmer ya amince da buƙatarsu na a samar da ƙasar Falasɗinu.

Ƙasashe da dama, kusan 139 sun amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa a hukumance, kuma a makon da ya wuce Faransa ta ce za ta yi shelar hakan yayin taron na Majalisar Ɗinkin Duniya da ke gudana yanzu haka.

Rikicin Gabas ta Tsakiya na ƙara ƙamari, inda al’ummar Gaza ke mutuwa a kullum , yayin da suke fuskantar matsananciyar yunwa, abinda wasu ke ganin samar da ƙasar Falasɗinu ne na mafita domin kawo ƙarshen yaƙin baki ɗaya.

A halin yanzu ƙasashen duniya sama da 100 ne ke tattauna makomar Falasdinu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa matsalar yunwa mafi muni a duniya na shirin faruwa a Gaza, saboda yadda mutane ke mutuwa wasu ke galabaita a dalilin rashin abinci.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Birtaniya Isra ila Majalisar Ɗinkin Duniya Majalisar Ɗinkin Duniya

এছাড়াও পড়ুন:

HKI Ta ce Ta Tsaida Yaki A Gaza Na Wani Lokaci

Majiyar sojojin HKI ta bada sanarwan cewa sun tsaida yaki na wucin gadi a gaza, don baya kungiyoyin agaji na MDD su shigar da abinci zuwa zirin gaza inda Falasdinawa suke mutuwa saboda yunwa.

Babu wata majiya ta MDD ko kuma na kungiyoyin agaji masu zaman kansu da suka tabbatar da labarin. Kuma mafi yawan kungiyayin sun bayyana cewa sai gani a kasa. Don hki ba abar amincewa bace. Tun shekara ta 2023 ne HKI ta kara tsananta hana shigo da abinci gaza.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Amincewa Da Kasar Falasɗinu: Birtaniya Ta Gindaya Wa Isra’ila Sharuɗɗa
  • Birtaniya Ta Yi Barazanar Amincewa Da Kasar Falasdinu A Watan Satumba Idan Yanayin Gaza Bai Canza Ba
  • Muddin Isra’ila ba ta cika wasu sharuɗa ba za mu amince da kafa ƙasar Falasɗinu — Birtaniya
  • An fara shigar da kayan agaji a Gaza
  • Pezeshkiya: Iran A Shirye Take Don Mu’amala Amma Bazata Bar Hakkinta Ba
  • Sin Ta Samar Da Manyan Manhajojin AI Sama Da 1500
  • Araqchi: Tattaunawar Nukiliya Wani Zabi Ne Mai Muhaimmanci Wanda Ya Karfafa Matsayin Iran A Duniya
  • Dakarun Yemen Zasu Kara Daukan Matakai Kan Jiragen Ruwan Da Ke Hulda Da Isra’ila
  • HKI Ta ce Ta Tsaida Yaki A Gaza Na Wani Lokaci