Shugaban Ivory Coast Ouattara zai sake takara wa’adi na huɗu
Published: 30th, July 2025 GMT
Shugaban Ivory Coast, Alassane Ouattara wanda ke jagorantar ƙasar tun daga shekarar 2011, na fuskantar suka na neman mayar da shugabancin ƙasar mutu ka raba.
Wannan dai na zuwa ne bayan Ouattara mai shekaru 83 ya tabbatar da aniyar sake takara wa’adi na hudu a zaben da za a yi ranar 25 ga watan Oktoba.
A wani takaitaccen bayani da ya yi, Ouattara ya ce takararsa ta samo asali ne daga buƙatarsa ta kiyaye zaman lafiyar ƙasa a daidai lokacin da ta ke fuskantar kalubalen tsaro da na tattalin arziki.
Ya bayyana cewa, “Ni dan takara ne saboda kundin tsarin mulkin kasarmu ya ba ni damar sake tsayawa takara a wani wa’adi, kuma ina da lafiyar yin hakan,” inji Shugaba Ouattara.
Sanarwar da ya yi a kafafen sada zumunta, na zuwa ne bayan da jam’iyyarsa ta Rally of Houphouëtists for Democracy and Peace (RHDP) ta amince da takararsa a hukumance.
Jam’iyyun adawa sun soki matakin da cewa ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar.
Tun dai gabanin sanar da matsayar sake takara, aka soma tafka muhawara kan soke sunayen ’yan takarar shugaban kasa daga bagaren ’yan adawa.
Tsohon shugaban ƙasar Laurent Gbagbo, da tsohon Firaminista Guillaume Soro, da kuma tsohon minista Tidjane Thiam duk an cire sunayensu daga rajistar masu zaɓe, lamarin da ya hana su tsayawa takara.
Bayanai sun ce hankali ya ƙara tashi a yau bayan da hukumomi suka haramta zanga-zangar lumana da aka shirya gudanarwa a ranar 7 ga watan Agusta, ranar bikin samun ’yancin kai na Cote d’Ivoire.
Ƙungiyoyin ’yan adawa ne suka shirya zanga-zangar da nufin neman a gudanar da bincike mai zaman kansa kan jerin sunayen masu kaɗa ƙuri’a tare da mayar da sunayen waɗanda aka hana tsayawa takara.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Alassane Ouattara Ivory Coast
এছাড়াও পড়ুন:
Shugabar Tanzania Samia Suluhu Ta Lashe Zaɓe, Duk Da Rikicin Da Ya Mamaye Ƙasar
Shugaba Samia Suluhu Hassan, wadda ke neman wa’adin ta na farko a hukumance bayan ta gaji marigayi John Pombe Magufuli a 2021, ta tsaya takara ƙarƙashin jam’iyyar CCM mai mulki. Sai dai rashin shigar manyan ‘yan adawa da aka hana tsayawa ko aka daure ya jefa shakku kan ingancin zaɓen da aka gudanar, inda masu zanga-zanga suka yi kira da a kafa gwamnatin riƙon ƙwarya da zai shirya sahihin zaɓe a gaba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA