Gwamna Namadi Ya Naɗa Shugabannin Hukumar Hisbah Ta Jihar Jigawa
Published: 30th, July 2025 GMT
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da naɗa Muhammad Fa’iz a matsayin Kwamanda Janar na farko na Hukumar Hisbah ta Jihar.
Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ne ya tabbatar da naɗin ga manema labarai a Dutse.
Ya bayyana cewa hakan na daga cikin ƙoƙarin Gwamna Namadi na ƙarfafa ayyukan sabuwar hukumar Hisbah da inganta aikinta.
A cewar sa, naɗin ya haɗa da Dr. Husaini Yusuf Baban a matsayin Babban Mataimakin Kwamanda Janar, da Lawan Danbala a matsayin Mataimakin Kwamanda Janar da hedikwatar hukumar, da kuma Yunusa Idris Barau a matsayin Mataimakin Kwamanda Janar naYankin Dutse.
Sauran su ne Abdulkadir Zakar, Mataimakin Kwamanda Janar, Yankin Hadejia, da Suraja Adamu, Mataimakin Kwamanda Janar, Yankin Gumel, da Bello Musa Gada, Mataimakin Kwamanda Janar, Yankin Kazaure, sai Barrister Mustapha Habu a matsayin Sakatari kuma Lauya mai ba da shawara.
Malam Bala Ibrahim ya jaddada cewa an zaɓi waɗannan mutane ne bisa cancanta, ƙwarewa da kuma nagartar halayensu, yana mai kira gare su da su yi kokarin sauke nauyin da aka dora musu.
Sakataren Gwamnatin Jihar ya ce an riga an mika musu takardun naɗi kuma sun shirya tsaf don fara aiki nan take.
A nasa bangaren, Muhammad Fa’iz ya gode wa Gwamna bisa amincewar da ya nuna musu, tare da alƙawarin gudanar da aiki da ƙwazo da himma.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa Mataimakin Kwamanda Janar
এছাড়াও পড়ুন:
Kwale-kwale Ya Kife Da Fasinjoji 16 A Karamar Hukumar Taura
Akalla mutane 7 ne aka ceto, bayan kifewar kwale-kwale a wani kogi da ke Zangon Maje, ƙaramar hukumar Taura, ta jihar Jigawa ranar Litinin.
Shugaban ƙaramar hukumar Taura, Dr Shuaibu Hambali ne ya bayyana hakan ga Rediyon Najeriya a Dutse, babban birnin jihar.
A cewarsa, lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, lokacin da wasu manoma ke dawowa daga gonakinsu a ƙauyen Zangon Maje, inda suka hau kwale-kwalen.
Ya ce, jami’an bada agajin gaggawa na yankin sun samu nasarar ceto mutane 7 a kokarin da suka yi na ceto wadanda lamarin ya shafa.
Ya ƙara da cewa, masu ceton sun gano gawar mutum guda a yankin Yalleman da ke ƙaramar hukumar Kaugama.
Dr Shuaibu ya bayyana cewa, sauran mutane 9 da ke cikin jirgin har yanzu ba a same su ba a lokacin da ake bayar da wannan rahoto.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, ba a fitar da sunayen waɗanda abin ya shafa ba, amma lamarin ya jefa al’ummar yankin cikin jimami da baƙin ciki.
Shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana cewa, za a raba rigunan kariya (life jacket) ga fasinjoji a nan gaba kadan domin kiyaye sake afkuwar lamarin nan gaba.
Ya kuma gargadi matuka kwale-kwale da su kiyaye ƙa’idojin tsaro da kaucewa cunkoson fasinjoji, musamman da yamma a lokacin damina, inda ruwa ke ƙaruwa a kowane lokaci.
Dr Hambali, wanda ya isa wurin da abin ya faru, ya jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su.
Wasu daga cikin mazauna yankin da Rediyon Najeriya ta tattauna da su, sun nemi gwamnatin ta gaggauta ɗaukar matakan da suka dace, tare da inganta hanyoyin sufuri ta ruwa.
Usman Muhammad Zaria